سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 1

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُواْ رَبَّكُمُ ٱلَّذِي خَلَقَكُم مِّن نَّفۡسٖ وَٰحِدَةٖ وَخَلَقَ مِنۡهَا زَوۡجَهَا وَبَثَّ مِنۡهُمَا رِجَالٗا كَثِيرٗا وَنِسَآءٗۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ ٱلَّذِي تَسَآءَلُونَ بِهِۦ وَٱلۡأَرۡحَامَۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلَيۡكُمۡ رَقِيبٗا

Ya ku mutane, ku kiyaye dokokin Ubangijinku Wanda Ya halicce ku daga rai guda xaya, kuma Ya halicci matarsa daga shi, kuma Ya yaxa maza da mata masu yawa daga gare su. Kuma ku kiyaye dokokin Allah Wanda kuke yi wa juna magiya da Shi, kuma ku kiyaye (yanke) zumunci. Lalle Allah Mai kula da ku ne



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 2

وَءَاتُواْ ٱلۡيَتَٰمَىٰٓ أَمۡوَٰلَهُمۡۖ وَلَا تَتَبَدَّلُواْ ٱلۡخَبِيثَ بِٱلطَّيِّبِۖ وَلَا تَأۡكُلُوٓاْ أَمۡوَٰلَهُمۡ إِلَىٰٓ أَمۡوَٰلِكُمۡۚ إِنَّهُۥ كَانَ حُوبٗا كَبِيرٗا

Kuma ku bai wa marayu dukiyoyinsu; kuma kada ku musanya kyakkyawa da mummuna; kuma kada ku ci dukiyoyinsu haxe da dukiyoyinku. Lalle yin hakan ya tabbata zunubi ne mai girma



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 3

وَإِنۡ خِفۡتُمۡ أَلَّا تُقۡسِطُواْ فِي ٱلۡيَتَٰمَىٰ فَٱنكِحُواْ مَا طَابَ لَكُم مِّنَ ٱلنِّسَآءِ مَثۡنَىٰ وَثُلَٰثَ وَرُبَٰعَۖ فَإِنۡ خِفۡتُمۡ أَلَّا تَعۡدِلُواْ فَوَٰحِدَةً أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡۚ ذَٰلِكَ أَدۡنَىٰٓ أَلَّا تَعُولُواْ

Kuma idan kun ji tsoron cewa ba za ku iya yin adalci ba dangane da marayu, to ku auri matan da kuke so, ko dai bibbiyu ko uku-uku ko kuma hurhuxu. To idan kun ji tsoron ba za ku iya yin adalci ba, to sai ku taqaita a kan xaya ko kuma abin da kuka mallaka na qwarqwarori. Hakan shi ya fi nisanta ku daga zalunci



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 4

وَءَاتُواْ ٱلنِّسَآءَ صَدُقَٰتِهِنَّ نِحۡلَةٗۚ فَإِن طِبۡنَ لَكُمۡ عَن شَيۡءٖ مِّنۡهُ نَفۡسٗا فَكُلُوهُ هَنِيٓـٔٗا مَّرِيٓـٔٗا

Kuma ku bai wa mata sadakinsu kyauta. Amma idan suka ba ku wani abu cikin daxin rai, to ku ci shi yana mai daxi da sauqin haxiya



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 5

وَلَا تُؤۡتُواْ ٱلسُّفَهَآءَ أَمۡوَٰلَكُمُ ٱلَّتِي جَعَلَ ٱللَّهُ لَكُمۡ قِيَٰمٗا وَٱرۡزُقُوهُمۡ فِيهَا وَٱكۡسُوهُمۡ وَقُولُواْ لَهُمۡ قَوۡلٗا مَّعۡرُوفٗا

Kuma kada ku bai wa (marayu) wawaye dukiyoyinku wadda Allah Ya sanya rayuwarku take tsaye a kai, kuma ku ciyar da su, kuma ku tufatar da su daga cikinta, kuma ku faxa musu magana mai daxi



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 6

وَٱبۡتَلُواْ ٱلۡيَتَٰمَىٰ حَتَّىٰٓ إِذَا بَلَغُواْ ٱلنِّكَاحَ فَإِنۡ ءَانَسۡتُم مِّنۡهُمۡ رُشۡدٗا فَٱدۡفَعُوٓاْ إِلَيۡهِمۡ أَمۡوَٰلَهُمۡۖ وَلَا تَأۡكُلُوهَآ إِسۡرَافٗا وَبِدَارًا أَن يَكۡبَرُواْۚ وَمَن كَانَ غَنِيّٗا فَلۡيَسۡتَعۡفِفۡۖ وَمَن كَانَ فَقِيرٗا فَلۡيَأۡكُلۡ بِٱلۡمَعۡرُوفِۚ فَإِذَا دَفَعۡتُمۡ إِلَيۡهِمۡ أَمۡوَٰلَهُمۡ فَأَشۡهِدُواْ عَلَيۡهِمۡۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ حَسِيبٗا

Kuma ku jarraba hankulan marayu, har lokacin da suka isa aure, to idan kun ga alamar hankali tare da su, sai ku ba su dukiyoyinsu; kuma kada ku ci dukiyarsu ta hanyar almubazzaranci da kuma gaggawa don gudun kada su girma. Duk kuma wanda ya kasance mawadaci ne, to ya kame kansa; wanda kuma ya kasance mabuqaci ne, to ya ci ta hanyar da ta dace. To idan za ku miqa musu dukiyoyinsu, sai ku kafa musu shaidu. Kuma Allah Ya isa Mai hisabi



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 7

لِّلرِّجَالِ نَصِيبٞ مِّمَّا تَرَكَ ٱلۡوَٰلِدَانِ وَٱلۡأَقۡرَبُونَ وَلِلنِّسَآءِ نَصِيبٞ مِّمَّا تَرَكَ ٱلۡوَٰلِدَانِ وَٱلۡأَقۡرَبُونَ مِمَّا قَلَّ مِنۡهُ أَوۡ كَثُرَۚ نَصِيبٗا مَّفۡرُوضٗا

Mazaje suna da wani kaso daga abin da mahaifa da dangi mafiya kusanci suka bari, haka mata su ma suna da wani kaso cikin abin da mahaifa da dangi mafiya kusanci suka bari, daga abin da yake xan kaxan ko mai yawa. Kaso ne wanda an riga an rarraba shi



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 8

وَإِذَا حَضَرَ ٱلۡقِسۡمَةَ أُوْلُواْ ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينُ فَٱرۡزُقُوهُم مِّنۡهُ وَقُولُواْ لَهُمۡ قَوۡلٗا مَّعۡرُوفٗا

Kuma idan dangi makusanta da marayu da mabuqata suka halarci rabon gado, to ku arzurta su daga cikin wannan dukiya, kuma ku faxa musu magana mai daxi



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 9

وَلۡيَخۡشَ ٱلَّذِينَ لَوۡ تَرَكُواْ مِنۡ خَلۡفِهِمۡ ذُرِّيَّةٗ ضِعَٰفًا خَافُواْ عَلَيۡهِمۡ فَلۡيَتَّقُواْ ٱللَّهَ وَلۡيَقُولُواْ قَوۡلٗا سَدِيدًا

Waxanda suke jin tsoron za su mutu su bar ‘ya’ya raunana a bayansu, suna kuma jin tsoron a zalunce su, to su kiyaye dokokin Allah, kuma su faxi magana ta daidai



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 10

إِنَّ ٱلَّذِينَ يَأۡكُلُونَ أَمۡوَٰلَ ٱلۡيَتَٰمَىٰ ظُلۡمًا إِنَّمَا يَأۡكُلُونَ فِي بُطُونِهِمۡ نَارٗاۖ وَسَيَصۡلَوۡنَ سَعِيرٗا

Lalle waxanda suke cin dukiyar marayu bisa zalunci, wuta ce kawai suke ci a cikkunansu; kuma da sannu za su shiga wuta mai tsananin quna



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 11

يُوصِيكُمُ ٱللَّهُ فِيٓ أَوۡلَٰدِكُمۡۖ لِلذَّكَرِ مِثۡلُ حَظِّ ٱلۡأُنثَيَيۡنِۚ فَإِن كُنَّ نِسَآءٗ فَوۡقَ ٱثۡنَتَيۡنِ فَلَهُنَّ ثُلُثَا مَا تَرَكَۖ وَإِن كَانَتۡ وَٰحِدَةٗ فَلَهَا ٱلنِّصۡفُۚ وَلِأَبَوَيۡهِ لِكُلِّ وَٰحِدٖ مِّنۡهُمَا ٱلسُّدُسُ مِمَّا تَرَكَ إِن كَانَ لَهُۥ وَلَدٞۚ فَإِن لَّمۡ يَكُن لَّهُۥ وَلَدٞ وَوَرِثَهُۥٓ أَبَوَاهُ فَلِأُمِّهِ ٱلثُّلُثُۚ فَإِن كَانَ لَهُۥٓ إِخۡوَةٞ فَلِأُمِّهِ ٱلسُّدُسُۚ مِنۢ بَعۡدِ وَصِيَّةٖ يُوصِي بِهَآ أَوۡ دَيۡنٍۗ ءَابَآؤُكُمۡ وَأَبۡنَآؤُكُمۡ لَا تَدۡرُونَ أَيُّهُمۡ أَقۡرَبُ لَكُمۡ نَفۡعٗاۚ فَرِيضَةٗ مِّنَ ٱللَّهِۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمٗا

Allah Yana yi muku wasiyya game da ‘ya’yanku; namiji xaya yana da rabon ‘ya’ya mata biyu. Amma idan sun kasance mata ne biyu ko fiye da biyu, to suna da kaso biyu bisa uku na abin da ya bari; kuma idan ta kasance ‘ya ce guda xaya to tana da rabi. Kuma kowane xaya daga cikin mahaifansa biyu yana da kaso xaya bisa shida daga cikin abin da ya bari in ya kasance yana da xa ko ‘ya[1]. Idan kuma ya kasance ba shi da xa ko ‘ya, kuma mahaifansa biyu ne za su ci gadonsa, to mahaifiyarsa tana da kaso xaya bisa uku. Amma idan yana da ‘yan’uwa[2], to mahaifiyarsa tana da kaso xaya bisa shida; bayan an fitar da wasiyyar da aka yi ko kuma bashi[3]. Iyayenku da ‘ya’yanku, ba ku san daga cikinsu wane ne zai fi yi muku amfani ba. Rabo ne daga Allah. Lalle Allah Ya kasance Mai yawan sani ne, Mai cikakkiyar hikima


1- Ko kuma jika na vangaren ‘ya’ya maza.


2- Watau Shaqiqai ko li’abbai ko li’ummai.


3- Ana fara fitar da bashi, sannan wasiyya wadda ba za ta wuce xaya bisa uku na dukiyar mamaci ba. Kuma babu wasiyya ga wanda yake da gado.


سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 12

۞وَلَكُمۡ نِصۡفُ مَا تَرَكَ أَزۡوَٰجُكُمۡ إِن لَّمۡ يَكُن لَّهُنَّ وَلَدٞۚ فَإِن كَانَ لَهُنَّ وَلَدٞ فَلَكُمُ ٱلرُّبُعُ مِمَّا تَرَكۡنَۚ مِنۢ بَعۡدِ وَصِيَّةٖ يُوصِينَ بِهَآ أَوۡ دَيۡنٖۚ وَلَهُنَّ ٱلرُّبُعُ مِمَّا تَرَكۡتُمۡ إِن لَّمۡ يَكُن لَّكُمۡ وَلَدٞۚ فَإِن كَانَ لَكُمۡ وَلَدٞ فَلَهُنَّ ٱلثُّمُنُ مِمَّا تَرَكۡتُمۚ مِّنۢ بَعۡدِ وَصِيَّةٖ تُوصُونَ بِهَآ أَوۡ دَيۡنٖۗ وَإِن كَانَ رَجُلٞ يُورَثُ كَلَٰلَةً أَوِ ٱمۡرَأَةٞ وَلَهُۥٓ أَخٌ أَوۡ أُخۡتٞ فَلِكُلِّ وَٰحِدٖ مِّنۡهُمَا ٱلسُّدُسُۚ فَإِن كَانُوٓاْ أَكۡثَرَ مِن ذَٰلِكَ فَهُمۡ شُرَكَآءُ فِي ٱلثُّلُثِۚ مِنۢ بَعۡدِ وَصِيَّةٖ يُوصَىٰ بِهَآ أَوۡ دَيۡنٍ غَيۡرَ مُضَآرّٖۚ وَصِيَّةٗ مِّنَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَلِيمٞ

Kuma kuna da rabin abin da matanku suka bari in ya kasance ba su da xa ko ‘ya, amma idan sun kasance suna da xa ko ‘ya, to kuna da kaso xaya bisa huxu na abin da suka bari, bayan zartar da wasiyyar da suka yi ko kuma bashi. Kuma suna da kaso xaya bisa huxu[1] na abin da kuka bari, in ya kasance ba ku da xa ko ‘ya. Amma idan ya kasance kuna da xa ko ‘ya to (matanku) suna da kaso xaya cikin takwas na abin da kuka bari, bayan zartar da wasiyyar da kuka yi ko kuma bashi. Amma idan namiji ne za a gaje shi a matsayin kalala[2] ko mace, kuma yana da xan’uwa guda xaya ko ‘yar’uwa guda xaya, to kowanne xaya yana da kaso xaya bisa shida. Amma idan sun fi haka yawa, to za su yi tarayya cikin kaso xaya bisa uku, bayan zartar da wasiyyar da aka yi ko kuma bashi, ba wanda zai cutar da (magadansa) ba. Allah Yana yi muku wasiyya matuqar wasiyya. Allah kuma Mai cikakken sani ne, Mai haquri


1- Idan sama da mace xaya ce, to za su yi tarayya ne a cikin wannan kason.


2- Kalala shi ne mamaci; namiji ko mace da bai bar ‘ya’ya ko iyaye ba, sai ‘yan’uwa.


سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 13

تِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِۚ وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ يُدۡخِلۡهُ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ وَذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ

Waxannan iyakoki ne na Allah. Wanda duk yake bin Allah da Manzonsa, to zai shigar da shi gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna masu dawwama a cikinsu. Kuma wannan shi ne rabo mai girma



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 14

وَمَن يَعۡصِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَيَتَعَدَّ حُدُودَهُۥ يُدۡخِلۡهُ نَارًا خَٰلِدٗا فِيهَا وَلَهُۥ عَذَابٞ مُّهِينٞ

Wanda kuma yake sava wa Allah da Manzonsa, yake kuma qetare iyakokinsa, to zai shigar da shi wuta, yana mai dawwama a cikinta, kuma yana da wata azaba mai wulaqantarwa



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 15

وَٱلَّـٰتِي يَأۡتِينَ ٱلۡفَٰحِشَةَ مِن نِّسَآئِكُمۡ فَٱسۡتَشۡهِدُواْ عَلَيۡهِنَّ أَرۡبَعَةٗ مِّنكُمۡۖ فَإِن شَهِدُواْ فَأَمۡسِكُوهُنَّ فِي ٱلۡبُيُوتِ حَتَّىٰ يَتَوَفَّىٰهُنَّ ٱلۡمَوۡتُ أَوۡ يَجۡعَلَ ٱللَّهُ لَهُنَّ سَبِيلٗا

Kuma waxannan da suke aikata zina daga cikin matanku, to ku kafa musu shaidu guda huxu daga cikinku, sannan idan sun bayar da shaida, to sai ku tsare su a cikin gidaje har sai mutuwa ta xauke su ko kuma Allah Ya sanya musu wata mafita[1]


1- Wannan hukuncin ya kasance ne gabanin a saukar da hukuncin bulala xari ga mazinatan da ba su tava yin aure ba ko jefewa ga waxanda suka tava yin aure.


سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 16

وَٱلَّذَانِ يَأۡتِيَٰنِهَا مِنكُمۡ فَـَٔاذُوهُمَاۖ فَإِن تَابَا وَأَصۡلَحَا فَأَعۡرِضُواْ عَنۡهُمَآۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ تَوَّابٗا رَّحِيمًا

Kuma maza biyu daga cikinku da za su yi zina, to ku muzguna musu; amma idan sun tuba kuma suka gyara ayyukansu, to ku kawar da kai daga gare su. Lalle Allah Ya kasance Mai yawan karvar tuba ne, Mai jin qai



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 17

إِنَّمَا ٱلتَّوۡبَةُ عَلَى ٱللَّهِ لِلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلسُّوٓءَ بِجَهَٰلَةٖ ثُمَّ يَتُوبُونَ مِن قَرِيبٖ فَأُوْلَـٰٓئِكَ يَتُوبُ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمٗا

Tuban da Allah Yake karva kawai (ita ce) na waxanda suke aikata mummunan aiki da jahilci, sannan su gaggauta tuba, to waxannan Allah zai karvi tubansu. Allah kuma Ya kasance Mai yawan sani ne, Mai hikima



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 18

وَلَيۡسَتِ ٱلتَّوۡبَةُ لِلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلسَّيِّـَٔاتِ حَتَّىٰٓ إِذَا حَضَرَ أَحَدَهُمُ ٱلۡمَوۡتُ قَالَ إِنِّي تُبۡتُ ٱلۡـَٰٔنَ وَلَا ٱلَّذِينَ يَمُوتُونَ وَهُمۡ كُفَّارٌۚ أُوْلَـٰٓئِكَ أَعۡتَدۡنَا لَهُمۡ عَذَابًا أَلِيمٗا

Kuma ba a karvar tuba daga waxanda suke aikata munanan ayyuka har sai lokacin da mutuwa ta zo wa xayansu, sai ya ce: “Ni kam na tuba yanzu;” kuma ba a karvar tuban waxanda suke mutuwa alhalin suna kafirai. Waxannan Mun yi musu tanadin azaba mai raxaxi



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 19

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا يَحِلُّ لَكُمۡ أَن تَرِثُواْ ٱلنِّسَآءَ كَرۡهٗاۖ وَلَا تَعۡضُلُوهُنَّ لِتَذۡهَبُواْ بِبَعۡضِ مَآ ءَاتَيۡتُمُوهُنَّ إِلَّآ أَن يَأۡتِينَ بِفَٰحِشَةٖ مُّبَيِّنَةٖۚ وَعَاشِرُوهُنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِۚ فَإِن كَرِهۡتُمُوهُنَّ فَعَسَىٰٓ أَن تَكۡرَهُواْ شَيۡـٔٗا وَيَجۡعَلَ ٱللَّهُ فِيهِ خَيۡرٗا كَثِيرٗا

Ya ku waxanda suka yi imani, bai halatta gare ku ku gaji mata a bisa ga tilas ba; kuma kada ku hana su aure don ku qwace wani sashi na abin da kuka ba su, sai fa in sun zo da wata alfasha ta sarari. Kuma ku yi musu kyakkyawar mu’amala. Amma idan har kun qi su, to mai yiwuwa ne ku qi wani abu, Allah kuma Ya sanya alheri mai yawa a cikinsa



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 20

وَإِنۡ أَرَدتُّمُ ٱسۡتِبۡدَالَ زَوۡجٖ مَّكَانَ زَوۡجٖ وَءَاتَيۡتُمۡ إِحۡدَىٰهُنَّ قِنطَارٗا فَلَا تَأۡخُذُواْ مِنۡهُ شَيۡـًٔاۚ أَتَأۡخُذُونَهُۥ بُهۡتَٰنٗا وَإِثۡمٗا مُّبِينٗا

Kuma idan kun yi nufin musanya wata mace a gurbin wata macen, kuma kun riga kun ba wa xayarsu dukiya mai yawa (ta sadaki), to kar ku karvi komai daga cikinsa. Shin za ku karve shi ne a kan zalunci da laifi qarara?



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 21

وَكَيۡفَ تَأۡخُذُونَهُۥ وَقَدۡ أَفۡضَىٰ بَعۡضُكُمۡ إِلَىٰ بَعۡضٖ وَأَخَذۡنَ مِنكُم مِّيثَٰقًا غَلِيظٗا

Kuma ta yaya za ku karve shi alhali kuma kun riga kun sadu da juna, kuma sun riqi wani alqawari mai qarfi daga wajenku?



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 22

وَلَا تَنكِحُواْ مَا نَكَحَ ءَابَآؤُكُم مِّنَ ٱلنِّسَآءِ إِلَّا مَا قَدۡ سَلَفَۚ إِنَّهُۥ كَانَ فَٰحِشَةٗ وَمَقۡتٗا وَسَآءَ سَبِيلًا

Kuma kada ku auri wadda iyayenku maza suka aure ta cikin mata, sai fa abin da ya riga ya shuxe. Lalle yin hakan ya kasance alfasha ce kuma abu ne da zai jawo fushin Allah, kuma tafarki ne wanda ya yi muni



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 23

حُرِّمَتۡ عَلَيۡكُمۡ أُمَّهَٰتُكُمۡ وَبَنَاتُكُمۡ وَأَخَوَٰتُكُمۡ وَعَمَّـٰتُكُمۡ وَخَٰلَٰتُكُمۡ وَبَنَاتُ ٱلۡأَخِ وَبَنَاتُ ٱلۡأُخۡتِ وَأُمَّهَٰتُكُمُ ٱلَّـٰتِيٓ أَرۡضَعۡنَكُمۡ وَأَخَوَٰتُكُم مِّنَ ٱلرَّضَٰعَةِ وَأُمَّهَٰتُ نِسَآئِكُمۡ وَرَبَـٰٓئِبُكُمُ ٱلَّـٰتِي فِي حُجُورِكُم مِّن نِّسَآئِكُمُ ٱلَّـٰتِي دَخَلۡتُم بِهِنَّ فَإِن لَّمۡ تَكُونُواْ دَخَلۡتُم بِهِنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ وَحَلَـٰٓئِلُ أَبۡنَآئِكُمُ ٱلَّذِينَ مِنۡ أَصۡلَٰبِكُمۡ وَأَن تَجۡمَعُواْ بَيۡنَ ٱلۡأُخۡتَيۡنِ إِلَّا مَا قَدۡ سَلَفَۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

An haramta muku auren iyayenku mata da ‘ya’yanku mata da ‘yan’uwanku mata da gwaggonninku da yagwalgwalanku da ‘ya’yan xan’uwa da ‘ya’yan ‘yar’uwa da iyayenku waxanda suka shayar da ku da ‘yan’uwanku mata ta wajen shayarwa, da iyayen matanku[1] da agololinku waxanda suke cikin gidajenku, waxanda matan da kuka tava saduwa da su suka haife su, in kuwa ba ku tava saduwa da su ba, to babu laifi a kanku, da matan ‘ya’yanku maza waxanda suke na tsatsonku; haramun ne kuma ku haxa ‘yan’uwa mata biyu, sai dai abin da ya wuce a baya[2]. Lalle Allah Ya kasance Mai yawan gafara ne, Mai jin qai


1- Daga zarar an xaura auren mutum da mace, to uwarta ta haramta gare shi, ko ba su tare ba.


2- Haramun ne mutum ya auri ya da qanwa lokaci xaya. Hakanan haramun ne ya haxa mace da gwaggonta ko innarta lokaci xaya.


سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 24

۞وَٱلۡمُحۡصَنَٰتُ مِنَ ٱلنِّسَآءِ إِلَّا مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡۖ كِتَٰبَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡۚ وَأُحِلَّ لَكُم مَّا وَرَآءَ ذَٰلِكُمۡ أَن تَبۡتَغُواْ بِأَمۡوَٰلِكُم مُّحۡصِنِينَ غَيۡرَ مُسَٰفِحِينَۚ فَمَا ٱسۡتَمۡتَعۡتُم بِهِۦ مِنۡهُنَّ فَـَٔاتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ فَرِيضَةٗۚ وَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ فِيمَا تَرَٰضَيۡتُم بِهِۦ مِنۢ بَعۡدِ ٱلۡفَرِيضَةِۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمٗا

Haka ma da matan aure, sai dai qwaraqwaranku; wannan hukuncin Allah ke nan a kanku. Kuma an halatta muku (sauran) matan da ba waxannan ba, ku neme su da kuxinku, kuna masu kame kanku, ba ma su zina ba. To waxanda kuka sadu da su daga cikinsu ku ba su sadakinsu wanda kuka yanka musu. Kuma babu laifi a kanku game da abin da kuka yi yarjejeniya da shi bayan sadakin da kuka yanka. Lalle Allah Ya kasance Mai yawan sani ne, Mai hikima



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 25

وَمَن لَّمۡ يَسۡتَطِعۡ مِنكُمۡ طَوۡلًا أَن يَنكِحَ ٱلۡمُحۡصَنَٰتِ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ فَمِن مَّا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُم مِّن فَتَيَٰتِكُمُ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتِۚ وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِإِيمَٰنِكُمۚ بَعۡضُكُم مِّنۢ بَعۡضٖۚ فَٱنكِحُوهُنَّ بِإِذۡنِ أَهۡلِهِنَّ وَءَاتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِ مُحۡصَنَٰتٍ غَيۡرَ مُسَٰفِحَٰتٖ وَلَا مُتَّخِذَٰتِ أَخۡدَانٖۚ فَإِذَآ أُحۡصِنَّ فَإِنۡ أَتَيۡنَ بِفَٰحِشَةٖ فَعَلَيۡهِنَّ نِصۡفُ مَا عَلَى ٱلۡمُحۡصَنَٰتِ مِنَ ٱلۡعَذَابِۚ ذَٰلِكَ لِمَنۡ خَشِيَ ٱلۡعَنَتَ مِنكُمۡۚ وَأَن تَصۡبِرُواْ خَيۡرٞ لَّكُمۡۗ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Kuma daga cikinku wanda ba shi da yalwar dukiya da zai iya auren ‘ya’ya muminai, to ya aura daga cikin abin da kuka mallaka na kuyanginku muminai. Kuma Allah Shi ne Mafi sanin imaninku. Sashinku ‘yan’uwan sashi ne. To ku aure su da izinin iyayen gidansu. Sai ku ba su sadakinsu ta hanyar da ta dace, suna masu kame kawunansu ba mazinata ba, sannan ba waxanda suke riqar farka a voye ba. To idan sun yi aure, sannan suka yi zina, to abin da za a yi musu na azaba, shi ne rabin abin da ake yi wa ‘ya’ya. Wannan ya shafi wanda ya ji tsoron matsatsi a cikinku. Amma ku yi haquri shi ya fi muku alheri. Allah kuma Mai yawan gafara ne, Mai jin qai



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 26

يُرِيدُ ٱللَّهُ لِيُبَيِّنَ لَكُمۡ وَيَهۡدِيَكُمۡ سُنَنَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ وَيَتُوبَ عَلَيۡكُمۡۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

Allah Yana nufin yi muku bayani ne, kuma Ya shiryar da ku hanyoyin waxanda suka gabace ku, kuma Ya karvi tubanku. Kuma Allah Mai yawan sani ne, Mai hikima



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 27

وَٱللَّهُ يُرِيدُ أَن يَتُوبَ عَلَيۡكُمۡ وَيُرِيدُ ٱلَّذِينَ يَتَّبِعُونَ ٱلشَّهَوَٰتِ أَن تَمِيلُواْ مَيۡلًا عَظِيمٗا

Kuma Allah Yana nufin Ya karvi tubanku ne, amma waxanda suke bin sha’awace-sha’awace, su kuma suna nufin ku karkace karkacewa mai girma



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 28

يُرِيدُ ٱللَّهُ أَن يُخَفِّفَ عَنكُمۡۚ وَخُلِقَ ٱلۡإِنسَٰنُ ضَعِيفٗا

Allah Yana nufin Ya sassauta muku. Kuma an halicci xan’adam mai rauni ne



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 29

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَأۡكُلُوٓاْ أَمۡوَٰلَكُم بَيۡنَكُم بِٱلۡبَٰطِلِ إِلَّآ أَن تَكُونَ تِجَٰرَةً عَن تَرَاضٖ مِّنكُمۡۚ وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَنفُسَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِكُمۡ رَحِيمٗا

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku ta hanyar rashin gaskiya, sai dai in ya kasance kasuwanci ne bisa yarjejeniya a tsakaninku. Kuma kada ku kashe kawunanku. Lalle Allah Ya kasance Mai tausaya muku ne



سوره: Suratun Nisa’i

آيه : 30

وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ عُدۡوَٰنٗا وَظُلۡمٗا فَسَوۡفَ نُصۡلِيهِ نَارٗاۚ وَكَانَ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرًا

Kuma duk wanda ya aikata haka don qetare iyaka da zalunci, to za Mu shigar da shi cikin wata wuta; kuma yin haka ya kasance abu ne mai sauqi a wurin Allah