وَمَا تِلۡكَ بِيَمِينِكَ يَٰمُوسَىٰ
“Mene ne kuma wancan yake a hannun damanka ya Musa?”
قَالَ هِيَ عَصَايَ أَتَوَكَّؤُاْ عَلَيۡهَا وَأَهُشُّ بِهَا عَلَىٰ غَنَمِي وَلِيَ فِيهَا مَـَٔارِبُ أُخۡرَىٰ
(Musa) ya ce: “Ai sandata ce da nake jingina a kanta, ina kuma kaxo wa dabbobina ganye da ita, ina kuma da sauran wasu buqatu game da ita.”
قَالَ أَلۡقِهَا يَٰمُوسَىٰ
(Allah) Ya ce: “Jefar da ita ya Musa.”
فَأَلۡقَىٰهَا فَإِذَا هِيَ حَيَّةٞ تَسۡعَىٰ
Sai ya jefar da ita, sai ga ta ta zama macijiya tana ta sauri
قَالَ خُذۡهَا وَلَا تَخَفۡۖ سَنُعِيدُهَا سِيرَتَهَا ٱلۡأُولَىٰ
Ya ce: “Kama ta, kuma kada ka ji tsoro; za Mu mai da ita kamar yadda take a da
وَٱضۡمُمۡ يَدَكَ إِلَىٰ جَنَاحِكَ تَخۡرُجۡ بَيۡضَآءَ مِنۡ غَيۡرِ سُوٓءٍ ءَايَةً أُخۡرَىٰ
“Kuma ka haxa hannunka da kwivinka zai fito fari sal ba tare da wata cuta ba; (wannan) wata ayar ce daban
لِنُرِيَكَ مِنۡ ءَايَٰتِنَا ٱلۡكُبۡرَى
“Domin Mu nuna maka irin manya-manyan ayoyinmu
ٱذۡهَبۡ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ
“Ka tafi wurin Fir’auna don kuwa lalle ya qetare iyaka.”
قَالَ رَبِّ ٱشۡرَحۡ لِي صَدۡرِي
(Musa) ya ce: “Ubangijina Ka buxe mini qirjina[1]
1- Watau ya cire masa in’ina da take damun sa.
وَيَسِّرۡ لِيٓ أَمۡرِي
“Kuma Ka sauqaqa mini lamarina
وَٱحۡلُلۡ عُقۡدَةٗ مِّن لِّسَانِي
“Ka kuma warware qullin da yake a harshena
يَفۡقَهُواْ قَوۡلِي
“(Don) su fahimci maganata
وَٱجۡعَل لِّي وَزِيرٗا مِّنۡ أَهۡلِي
“Kuma Ka sanya mini waziri daga dangina
هَٰرُونَ أَخِي
“(Watau) xau’uwana Haruna
ٱشۡدُدۡ بِهِۦٓ أَزۡرِي
“Ka qarfafa gwiwata da shi
وَأَشۡرِكۡهُ فِيٓ أَمۡرِي
“Kuma Ka shigar da shi cikin lamarina[1]
1- Watau shi ma ya ba shi annabta ya aiko su tare.
كَيۡ نُسَبِّحَكَ كَثِيرٗا
“Domin mu tsarkake Ka da yawa
وَنَذۡكُرَكَ كَثِيرًا
“Mu kuma ambace Ka da yawa
إِنَّكَ كُنتَ بِنَا بَصِيرٗا
“Lalle Kai Ka kasance Kana ganin mu.”
قَالَ قَدۡ أُوتِيتَ سُؤۡلَكَ يَٰمُوسَىٰ
(Allah) Ya ce: “Haqiqa an ba ka abin da ka tambaya, ya Musa
وَلَقَدۡ مَنَنَّا عَلَيۡكَ مَرَّةً أُخۡرَىٰٓ
“Haqiqa kuma Mun yi ni’ima a gare ka a wani lokaci
إِذۡ أَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰٓ أُمِّكَ مَا يُوحَىٰٓ
“Sanda Muka yiwo wahayi ga mahaifiyarka da abin da ake yin wahayi da shi
أَنِ ٱقۡذِفِيهِ فِي ٱلتَّابُوتِ فَٱقۡذِفِيهِ فِي ٱلۡيَمِّ فَلۡيُلۡقِهِ ٱلۡيَمُّ بِٱلسَّاحِلِ يَأۡخُذۡهُ عَدُوّٞ لِّي وَعَدُوّٞ لَّهُۥۚ وَأَلۡقَيۡتُ عَلَيۡكَ مَحَبَّةٗ مِّنِّي وَلِتُصۡنَعَ عَلَىٰ عَيۡنِيٓ
“Cewa, ‘ki saka shi (jinjirin) a cikin akwatu, sannan ki jefa shi cikin kogi, to sai kogin ya jefa shi a gava, sai maqiyina kuma maqiyinsa ya xauke shi.’ Na kuma sanya maka farin jini daga gare Ni, don kuma a yi tarbiyar ka a gaban idona
إِذۡ تَمۡشِيٓ أُخۡتُكَ فَتَقُولُ هَلۡ أَدُلُّكُمۡ عَلَىٰ مَن يَكۡفُلُهُۥۖ فَرَجَعۡنَٰكَ إِلَىٰٓ أُمِّكَ كَيۡ تَقَرَّ عَيۡنُهَا وَلَا تَحۡزَنَۚ وَقَتَلۡتَ نَفۡسٗا فَنَجَّيۡنَٰكَ مِنَ ٱلۡغَمِّ وَفَتَنَّـٰكَ فُتُونٗاۚ فَلَبِثۡتَ سِنِينَ فِيٓ أَهۡلِ مَدۡيَنَ ثُمَّ جِئۡتَ عَلَىٰ قَدَرٖ يَٰمُوسَىٰ
“Lokacin da ‘yar’uwarka take tafiya tana cewa (da su): ‘Yanzu ba na haxa ku da wadda za ta raine shi ba?’ Sai Muka komo da kai zuwa ga mahaifiyarka don zuciyarta ta yi sanyi, kada kuma ta yi baqin ciki. Kuma ka kashe wani mutum[1] sannan Muka tserar da kai daga uquba, Muka kuma jarrabe ka da jarrabobi daban-daban. Sannan ka zauna shekaru a cikin mutanen Madyana, sannan ka zo (nan) daidai lokacin da Na qadarta (maka annabta) ya Musa
1- Shi ne Baqibxen da Annabi Musa ya naushe shi ya faxi nan take ya mutu.
وَٱصۡطَنَعۡتُكَ لِنَفۡسِي
“Kuma Na zave ka don kaina[1]
1- Watau Allah () ya zave shi domin ya yi magana da shi, ya aika shi zuwa Fir’auna da mutanensa.
ٱذۡهَبۡ أَنتَ وَأَخُوكَ بِـَٔايَٰتِي وَلَا تَنِيَا فِي ذِكۡرِي
“Ka tafi kai da xan’uwanka da ayoyina, kada kuwa ku sassauta game da ambatona
ٱذۡهَبَآ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ
“Ku tafi wurin Fir’auna, don ko lalle ya wuce iyaka
فَقُولَا لَهُۥ قَوۡلٗا لَّيِّنٗا لَّعَلَّهُۥ يَتَذَكَّرُ أَوۡ يَخۡشَىٰ
“Sai ku gaya masa magana mai taushi, ko wataqila zai wa’azantu ko kuma ya ji tsoron (azabar Allah).”
قَالَا رَبَّنَآ إِنَّنَا نَخَافُ أَن يَفۡرُطَ عَلَيۡنَآ أَوۡ أَن يَطۡغَىٰ
(Musa da Haruna) suka ce: “Ya Ubangijinmu, lalle mu muna tsoron ya far mana ko kuma ya wuce iyaka (wajen yi mana uquba).”
قَالَ لَا تَخَافَآۖ إِنَّنِي مَعَكُمَآ أَسۡمَعُ وَأَرَىٰ
Ya ce: “Kada ku ji tsoro; haqiqa Ni ina tare da ku, ina ji kuma ina ganin (komai)