وَتَرَى ٱلۡمُجۡرِمِينَ يَوۡمَئِذٖ مُّقَرَّنِينَ فِي ٱلۡأَصۡفَادِ
Kuma za ka ga masu laifi a wannan ranar a ququmce cikin maruruwa
Share :
سَرَابِيلُهُم مِّن قَطِرَانٖ وَتَغۡشَىٰ وُجُوهَهُمُ ٱلنَّارُ
Rigunansu na (tafasasshen) man qaxiran ne[1], kuma wuta za ta lulluve fuskokinsu
1- Qaxiran, wani baqin mai ne kamar kwalta, mai saurin kamawa da wuta, mai kuma xan karen wari.
لِيَجۡزِيَ ٱللَّهُ كُلَّ نَفۡسٖ مَّا كَسَبَتۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ
(An yi musu haka ne) don Allah Ya saka wa kowanne rai da gwargwadon abin da ya aikata. Lalle Allah Mai saurin hisabi ne
هَٰذَا بَلَٰغٞ لِّلنَّاسِ وَلِيُنذَرُواْ بِهِۦ وَلِيَعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَا هُوَ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞ وَلِيَذَّكَّرَ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ
Wannan (Alqur’ani) saqo ne ga mutane don kuma a gargaxe su da shi, kuma su san cewa Shi Allah Xaya ne, don kuma ma’abota hankali su wa’azantu