Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 19

أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِٱلۡحَقِّۚ إِن يَشَأۡ يُذۡهِبۡكُمۡ وَيَأۡتِ بِخَلۡقٖ جَدِيدٖ

Ashe ba ka ga cewa, lalle Allah Ya halicci sammai da qasa kan gaskiya ba? Idan Ya ga dama sai Ya hallakar da ku Ya kuma zo da wata halitta sabuwa



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 20

وَمَا ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ بِعَزِيزٖ

Wannan kuwa ba abin da zai gagari Allah ba ne



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 21

وَبَرَزُواْ لِلَّهِ جَمِيعٗا فَقَالَ ٱلضُّعَفَـٰٓؤُاْ لِلَّذِينَ ٱسۡتَكۡبَرُوٓاْ إِنَّا كُنَّا لَكُمۡ تَبَعٗا فَهَلۡ أَنتُم مُّغۡنُونَ عَنَّا مِنۡ عَذَابِ ٱللَّهِ مِن شَيۡءٖۚ قَالُواْ لَوۡ هَدَىٰنَا ٱللَّهُ لَهَدَيۡنَٰكُمۡۖ سَوَآءٌ عَلَيۡنَآ أَجَزِعۡنَآ أَمۡ صَبَرۡنَا مَا لَنَا مِن مَّحِيصٖ

Suka kuma fito gaba xaya a gaban Allah (ranar alqiyama), sai raunanan suka ce da waxanda suka yi girman kai: “Lalle mu mun zamanto mabiya a gare ku, to ko za ku maganta mana wani abu daga azabar Allah?” Suka ce: “Da Allah Ya shirye mu da lalle mun shiryar da ku; duka xaya ne gare mu ko mun yi raki ko mun yi haquri (duka dai) ba mu da wata maguda.”



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 22

وَقَالَ ٱلشَّيۡطَٰنُ لَمَّا قُضِيَ ٱلۡأَمۡرُ إِنَّ ٱللَّهَ وَعَدَكُمۡ وَعۡدَ ٱلۡحَقِّ وَوَعَدتُّكُمۡ فَأَخۡلَفۡتُكُمۡۖ وَمَا كَانَ لِيَ عَلَيۡكُم مِّن سُلۡطَٰنٍ إِلَّآ أَن دَعَوۡتُكُمۡ فَٱسۡتَجَبۡتُمۡ لِيۖ فَلَا تَلُومُونِي وَلُومُوٓاْ أَنفُسَكُمۖ مَّآ أَنَا۠ بِمُصۡرِخِكُمۡ وَمَآ أَنتُم بِمُصۡرِخِيَّ إِنِّي كَفَرۡتُ بِمَآ أَشۡرَكۡتُمُونِ مِن قَبۡلُۗ إِنَّ ٱلظَّـٰلِمِينَ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Shaixan kuma lokacin da aka gama hukunci ya ce: “Lalle Allah Ya yi muku alqawari na gaskiya, ni kuma na yi muku alqawari sai na sava muku. To ba ni da wani qarfi da na nuna muku, sai dai na yi kiran ku ne sai kuka amsa mini; to kada ku zarge ni, ku zargi kanku; ni ba zan taimake ku ba, ku kuma ba za ku taimake ni ba. Lalle ni na riga na kafirta da abin da kuka yi tarayya da ni a kansa tun a da can. Lalle azzalumai suna da (sakamakon) azaba mai raxaxi.”



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 23

وَأُدۡخِلَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا بِإِذۡنِ رَبِّهِمۡۖ تَحِيَّتُهُمۡ فِيهَا سَلَٰمٌ

Aka kuma shigar da waxanda suka yi imani, suka kuma yi aiki nagari gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna masu dawwama a cikinsu da izinin Ubangijinsu; gaisuwarsu a cikinsu ita ce: “Aminci (ya tabbata a gare ku).”



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 24

أَلَمۡ تَرَ كَيۡفَ ضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا كَلِمَةٗ طَيِّبَةٗ كَشَجَرَةٖ طَيِّبَةٍ أَصۡلُهَا ثَابِتٞ وَفَرۡعُهَا فِي ٱلسَّمَآءِ

Shin ba ka ga yadda Allah Ya ba da misali ba? Daddaxar kalma[1] kamar daddaxar bishiya ce[2] wadda tushenta kafaffe ne (a qasa) reshenta kuma yana sama


1- Daddaxar kalma ita ce kalmar shahada, watau shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah.


2- Daddaxar bishiya kuwa ita ce bishiyar dabino. A nan ana nufin mumini. Kalmar shahada tana kafa tushenta a ciki zuciyar mumini.


Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 25

تُؤۡتِيٓ أُكُلَهَا كُلَّ حِينِۭ بِإِذۡنِ رَبِّهَاۗ وَيَضۡرِبُ ٱللَّهُ ٱلۡأَمۡثَالَ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَتَذَكَّرُونَ

Tana bayar da ‘ya’yanta ko da yaushe da izinin Ubangijinta. Allah kuwa Yana ba da misalai ne ga mutane don su wa’azantu



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 26

وَمَثَلُ كَلِمَةٍ خَبِيثَةٖ كَشَجَرَةٍ خَبِيثَةٍ ٱجۡتُثَّتۡ مِن فَوۡقِ ٱلۡأَرۡضِ مَا لَهَا مِن قَرَارٖ

Misalin kuma mummunar kalma kamar mummunar bishiya ce da aka tumvuke daga kan qasa, ba ta da wata matabbata



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 27

يُثَبِّتُ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱلۡقَوۡلِ ٱلثَّابِتِ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِۖ وَيُضِلُّ ٱللَّهُ ٱلظَّـٰلِمِينَۚ وَيَفۡعَلُ ٱللَّهُ مَا يَشَآءُ

Allah Yana tabbatar da waxanda suka yi imani a kan magana tabbatacciya a rayuwar duniya da kuma a lahira; Yana kuma vatar da azzalumai. Allah kuma Yana aikata abin da Ya ga dama



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 28

۞أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ بَدَّلُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ كُفۡرٗا وَأَحَلُّواْ قَوۡمَهُمۡ دَارَ ٱلۡبَوَارِ

Shin ba ka ga waxanda suka musanya ni’imar Allah da kafirci ba[1], suka kuma jefa mutanensu gidan hallaka?


1- Su ne kafiran Quraishawa.


Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 29

جَهَنَّمَ يَصۡلَوۡنَهَاۖ وَبِئۡسَ ٱلۡقَرَارُ

(Watau) Jahannama, za su shige ta; makoma kuwa ta munana



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 30

وَجَعَلُواْ لِلَّهِ أَندَادٗا لِّيُضِلُّواْ عَن سَبِيلِهِۦۗ قُلۡ تَمَتَّعُواْ فَإِنَّ مَصِيرَكُمۡ إِلَى ٱلنَّارِ

Sun sanya wa Allah abokan tarayya don su vatar (da mutane) daga hanyarsa. Ka ce: “Ku ji daxi (kaxan a duniya), to lalle makomarku wuta ce!”



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 31

قُل لِّعِبَادِيَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ يُقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُنفِقُواْ مِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ سِرّٗا وَعَلَانِيَةٗ مِّن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَ يَوۡمٞ لَّا بَيۡعٞ فِيهِ وَلَا خِلَٰلٌ

Ka ce da bayina waxanda suka yi imani, su tsayar da salla kuma su ciyar daga abin da Muka arzuta su da shi, a voye da sarari tun kafin zuwan ranar da babu ciniki a cikinta, kuma babu abota



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 32

ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَأَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجَ بِهِۦ مِنَ ٱلثَّمَرَٰتِ رِزۡقٗا لَّكُمۡۖ وَسَخَّرَ لَكُمُ ٱلۡفُلۡكَ لِتَجۡرِيَ فِي ٱلۡبَحۡرِ بِأَمۡرِهِۦۖ وَسَخَّرَ لَكُمُ ٱلۡأَنۡهَٰرَ

Allah ne Wanda Ya halicci sammai da qasa, Ya kuma saukar da ruwa daga sama, sai Ya fitar da ‘ya’yan itace don arzuta ku; Ya kuma hore muku jiragen ruwa don ku yi tafiya a cikin kogi da umarninsa, Ya kuma hore muku qoramu



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 33

وَسَخَّرَ لَكُمُ ٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَ دَآئِبَيۡنِۖ وَسَخَّرَ لَكُمُ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ

Ya kuma hore muku rana da wata tutur; Ya kuma hore muku dare da rana



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 34

وَءَاتَىٰكُم مِّن كُلِّ مَا سَأَلۡتُمُوهُۚ وَإِن تَعُدُّواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ لَا تُحۡصُوهَآۗ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَظَلُومٞ كَفَّارٞ

Ya kuma ba ku daga duk abin da kuka roqe Shi. In da za ku qirga ni’imomin Allah to ba za ku iya qididdige su ba. Lalle mutum mai yawan zalunci ne mai yawan butulci



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 35

وَإِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِيمُ رَبِّ ٱجۡعَلۡ هَٰذَا ٱلۡبَلَدَ ءَامِنٗا وَٱجۡنُبۡنِي وَبَنِيَّ أَن نَّعۡبُدَ ٱلۡأَصۡنَامَ

(Ka tuna) kuma lokacin da Ibrahimu ya ce: “Ya Ubangijina, Ka sanya wannan gari (Makka) ya zama amintacce, kuma Ka nesantar da ni da ‘ya’yana daga bauta wa gumaka



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 36

رَبِّ إِنَّهُنَّ أَضۡلَلۡنَ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلنَّاسِۖ فَمَن تَبِعَنِي فَإِنَّهُۥ مِنِّيۖ وَمَنۡ عَصَانِي فَإِنَّكَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

“Ya Ubangijina, lalle su (gumakan) sun vatar da mutane masu yawa; wanda kuwa ya bi ni to lalle shi yana tare da ni; wanda kuma ya sava mini to lalle Kai Mai gafara ne, Mai jin qai.”



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 37

رَّبَّنَآ إِنِّيٓ أَسۡكَنتُ مِن ذُرِّيَّتِي بِوَادٍ غَيۡرِ ذِي زَرۡعٍ عِندَ بَيۡتِكَ ٱلۡمُحَرَّمِ رَبَّنَا لِيُقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ فَٱجۡعَلۡ أَفۡـِٔدَةٗ مِّنَ ٱلنَّاسِ تَهۡوِيٓ إِلَيۡهِمۡ وَٱرۡزُقۡهُم مِّنَ ٱلثَّمَرَٰتِ لَعَلَّهُمۡ يَشۡكُرُونَ

“Ya Ubangijinmu, lalle ni na zaunar da wasu daga zuriyata a wani kwari wanda ba a shuka a cikinsa[1] kusa da Xakinka mai alfarma; ya Ubangijinmu don su tsai da salla, to Ka sanya zukatan mutane su riqa karkatowa zuwa gare su, kuma Ka arzuta su da ‘ya’yan itace don su gode (maka)


1- Watau kuyangarsa Hajara () da xansa Isma’ilu (). Ya zaunar da su garin Makka da izinin Allah ().


Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 38

رَبَّنَآ إِنَّكَ تَعۡلَمُ مَا نُخۡفِي وَمَا نُعۡلِنُۗ وَمَا يَخۡفَىٰ عَلَى ٱللَّهِ مِن شَيۡءٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا فِي ٱلسَّمَآءِ

“Ya Ubangijinmu, lalle Kai Ka san abin da muke voyewa da abin da muke bayyanawa. Babu wani abu a cikin qasa ko a cikin sama da zai vuya ga Allah



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 39

ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي وَهَبَ لِي عَلَى ٱلۡكِبَرِ إِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَۚ إِنَّ رَبِّي لَسَمِيعُ ٱلدُّعَآءِ

“Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda Ya ba ni Isma’ila da Is’haqa a cikin halin tsufa. Lalle Ubangijina tabbas Mai jin roqo ne



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 40

رَبِّ ٱجۡعَلۡنِي مُقِيمَ ٱلصَّلَوٰةِ وَمِن ذُرِّيَّتِيۚ رَبَّنَا وَتَقَبَّلۡ دُعَآءِ

“Ya Ubangijina, Ka sanya ni in zama mai tsayar da salla da kuma zuriyata. Ya Ubangijinmu, Ka karvi addu’ata



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 41

رَبَّنَا ٱغۡفِرۡ لِي وَلِوَٰلِدَيَّ وَلِلۡمُؤۡمِنِينَ يَوۡمَ يَقُومُ ٱلۡحِسَابُ

“Ya Ubangijinmu Ka gafarta mini, ni da iyayena da kuma muminai ranar da hisabi zai kankama.”



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 42

وَلَا تَحۡسَبَنَّ ٱللَّهَ غَٰفِلًا عَمَّا يَعۡمَلُ ٱلظَّـٰلِمُونَۚ إِنَّمَا يُؤَخِّرُهُمۡ لِيَوۡمٖ تَشۡخَصُ فِيهِ ٱلۡأَبۡصَٰرُ

Kada ka yi tsammanin Allah ba Shi da masaniyar abin da azzalumai suke aikatawa. Yana dai saurara musu ne kawai zuwa ranar da idanuwa za su fito zuru-zuru



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 43

مُهۡطِعِينَ مُقۡنِعِي رُءُوسِهِمۡ لَا يَرۡتَدُّ إِلَيۡهِمۡ طَرۡفُهُمۡۖ وَأَفۡـِٔدَتُهُمۡ هَوَآءٞ

Suna masu gaggawa masu xage da kawunansu sama ba sa qiftawa; zukatansu kuma fanko ne (don tsananin firgita)



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 44

وَأَنذِرِ ٱلنَّاسَ يَوۡمَ يَأۡتِيهِمُ ٱلۡعَذَابُ فَيَقُولُ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ رَبَّنَآ أَخِّرۡنَآ إِلَىٰٓ أَجَلٖ قَرِيبٖ نُّجِبۡ دَعۡوَتَكَ وَنَتَّبِعِ ٱلرُّسُلَۗ أَوَلَمۡ تَكُونُوٓاْ أَقۡسَمۡتُم مِّن قَبۡلُ مَا لَكُم مِّن زَوَالٖ

Kuma ka gargaxi mutane game da ranar da azaba za ta zo musu, sai waxanda suka yi kafirci su ce: “Ya Ubangijinmu, Ka saurara mana zuwa xan lokaci qanqani, za mu amsa kiranka kuma mu bi manzanni.” (Sai a ce da su): “A da ba ku ne kuka yi rantsuwa ba cewa ba za ku gushe ba?



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 45

وَسَكَنتُمۡ فِي مَسَٰكِنِ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ وَتَبَيَّنَ لَكُمۡ كَيۡفَ فَعَلۡنَا بِهِمۡ وَضَرَبۡنَا لَكُمُ ٱلۡأَمۡثَالَ

“Kuka kuma zauna a gidajen waxanda suka zalunci kawunansu, kuma irin yadda Muka yi musu ya bayyana a gare ku, Muka kuma ba ku misalai!”



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 46

وَقَدۡ مَكَرُواْ مَكۡرَهُمۡ وَعِندَ ٱللَّهِ مَكۡرُهُمۡ وَإِن كَانَ مَكۡرُهُمۡ لِتَزُولَ مِنۡهُ ٱلۡجِبَالُ

Haqiqa kuma sun shirya makircinsu, sakamakon makircinsu kuma yana wurin Allah, ko da kuwa duwatsu za su gushe don makircinsu



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 47

فَلَا تَحۡسَبَنَّ ٱللَّهَ مُخۡلِفَ وَعۡدِهِۦ رُسُلَهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٞ ذُو ٱنتِقَامٖ

To kada ka yi tsammanin Allah Mai sava wa manzanninsa alqawarinsa ne. Lalle Allah Mabuwayi ne Ma’abocin uquba



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 48

يَوۡمَ تُبَدَّلُ ٱلۡأَرۡضُ غَيۡرَ ٱلۡأَرۡضِ وَٱلسَّمَٰوَٰتُۖ وَبَرَزُواْ لِلَّهِ ٱلۡوَٰحِدِ ٱلۡقَهَّارِ

(Ka tuna) ranar da za a sake qasa ba (wannan) qasar ba, da kuma sammai (ba waxannan samman ba. Halittu) kuma suka fito (daga cikin qasa) a gaban Allah Makaxaici, Mai rinjaye