Surah: Suratu Saba’i

Ayah : 48

قُلۡ إِنَّ رَبِّي يَقۡذِفُ بِٱلۡحَقِّ عَلَّـٰمُ ٱلۡغُيُوبِ

Ka ce: “Lalle Ubangijina Yana jefo gaskiya (sai ta rushe qarya), Masanin gaibu ne.”



Surah: Suratu Saba’i

Ayah : 49

قُلۡ جَآءَ ٱلۡحَقُّ وَمَا يُبۡدِئُ ٱلۡبَٰطِلُ وَمَا يُعِيدُ

Ka ce: “Gaskiya ta zo qarya kuma ba za ta sake faruwa ba, ba kuma za ta dawo ba.”



Surah: Suratu Saba’i

Ayah : 50

قُلۡ إِن ضَلَلۡتُ فَإِنَّمَآ أَضِلُّ عَلَىٰ نَفۡسِيۖ وَإِنِ ٱهۡتَدَيۡتُ فَبِمَا يُوحِيٓ إِلَيَّ رَبِّيٓۚ إِنَّهُۥ سَمِيعٞ قَرِيبٞ

Ka ce: “Idan na vata to na vata ne a kan kaina; idan kuwa na shiriya to (na shiriya ne) da abin da Ubangijina Yake yi min wahayinsa. Lalle Shi Mai ji ne, Makusanci.”



Surah: Suratu Saba’i

Ayah : 51

وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذۡ فَزِعُواْ فَلَا فَوۡتَ وَأُخِذُواْ مِن مَّكَانٖ قَرِيبٖ

Da kuwa za ka ga sanda (kafirai) za su firgita, (da ganin azaba), sannan ba wata makuvuta, kuma aka damqo su daga makusancin wuri



Surah: Suratu Saba’i

Ayah : 52

وَقَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِهِۦ وَأَنَّىٰ لَهُمُ ٱلتَّنَاوُشُ مِن مَّكَانِۭ بَعِيدٖ

Suka kuma ce: “Mun yi imani da shi,” yaya kuwa za su iya kamo (wannan imani) daga wuri mai nisa (wato duniya)?



Surah: Suratu Saba’i

Ayah : 53

وَقَدۡ كَفَرُواْ بِهِۦ مِن قَبۡلُۖ وَيَقۡذِفُونَ بِٱلۡغَيۡبِ مِن مَّكَانِۭ بَعِيدٖ

Alhalin kuma haqiqa sun riga sun kafirta da shi a da can, kuma suna jifa (da zato) ta wani wuri mai nisa[1]


1- Watau sun riqa jifan Manzon Allah () da zace-zace iri-iri da shaci-faxi, wani lokaci su kira shi mai sihiri, wani lokaci su ce masa boka, ko su kira shi mawaqi.


Surah: Suratu Saba’i

Ayah : 54

وَحِيلَ بَيۡنَهُمۡ وَبَيۡنَ مَا يَشۡتَهُونَ كَمَا فُعِلَ بِأَشۡيَاعِهِم مِّن قَبۡلُۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ فِي شَكّٖ مُّرِيبِۭ

Aka kuma kange tsakaninsu da abin da suke sha’awa (na jin daxin rayuwa ko komawa duniya) kamar yadda aka yi da ire-irensu tun da can. Lalle su sun kasance cikin shakka mai cike da kokwanto



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 1

ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ فَاطِرِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ جَاعِلِ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ رُسُلًا أُوْلِيٓ أَجۡنِحَةٖ مَّثۡنَىٰ وَثُلَٰثَ وَرُبَٰعَۚ يَزِيدُ فِي ٱلۡخَلۡقِ مَا يَشَآءُۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Mahaliccin sammai da qasa Mai sanya mala’iku manzanni masu fukafukai bibbiyu da masu uku-uku da kuma masu huxu-huxu. Yakan kuma qara abin da Ya ga dama ga halittar[1]. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai


1- Don haka akwai mala’iku masu fukafukai fiye da huxu, ya kuma qara wa wanda ya ga dama kyau ko wata gava.


Surah: Suratu Faxir

Ayah : 2

مَّا يَفۡتَحِ ٱللَّهُ لِلنَّاسِ مِن رَّحۡمَةٖ فَلَا مُمۡسِكَ لَهَاۖ وَمَا يُمۡسِكۡ فَلَا مُرۡسِلَ لَهُۥ مِنۢ بَعۡدِهِۦۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

Abin da Allah Yake yi wa mutane buxi da shi na rahama ba mai iya riqe shi; abin da kuma Yake riqewa ba mai iya sakin sa bayansa. Shi kuma Mabuwayi ne, Mai hikima



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 3

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡۚ هَلۡ مِنۡ خَٰلِقٍ غَيۡرُ ٱللَّهِ يَرۡزُقُكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۚ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ فَأَنَّىٰ تُؤۡفَكُونَ

Ya ku mutane, ku tuna ni’imar Allah a gare ku. Yanzu akwai wani mahalicci ban da Allah wanda zai arzuta ku daga sama da qasa? Babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. To ta yaya ake karkatar da ku?



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 4

وَإِن يُكَذِّبُوكَ فَقَدۡ كُذِّبَتۡ رُسُلٞ مِّن قَبۡلِكَۚ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرۡجَعُ ٱلۡأُمُورُ

Idan kuwa suka qaryata ka to haqiqa an qaryata wasu manzannin a gabaninka. Zuwa ga Allah ne kaxai ake mayar da al’amura



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 5

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞۖ فَلَا تَغُرَّنَّكُمُ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا وَلَا يَغُرَّنَّكُم بِٱللَّهِ ٱلۡغَرُورُ

Ya ku mutane, lalle alqawarin Allah gaskiya ne, saboda haka kada rayuwar duniya ta ruxe ku; kada kuma mai ruxarwa (Shaixan) ya ruxe ku game da Allah



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 6

إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ لَكُمۡ عَدُوّٞ فَٱتَّخِذُوهُ عَدُوًّاۚ إِنَّمَا يَدۡعُواْ حِزۡبَهُۥ لِيَكُونُواْ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلسَّعِيرِ

Lalle Shaixan maqiyinku ne, saboda haka sai ku riqe shi maqiyi. Lalle yana kiran mutanensa ne don su zama ‘yan wuta



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 7

ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَهُمۡ عَذَابٞ شَدِيدٞۖ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَأَجۡرٞ كَبِيرٌ

Waxanda suka kafirta suna da (sakamakon) azaba mai tsanani; waxanda kuwa suka yi imani suka kuma yi aiki nagari, to suna da gafara da lada mai girma



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 8

أَفَمَن زُيِّنَ لَهُۥ سُوٓءُ عَمَلِهِۦ فَرَءَاهُ حَسَنٗاۖ فَإِنَّ ٱللَّهَ يُضِلُّ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُۖ فَلَا تَذۡهَبۡ نَفۡسُكَ عَلَيۡهِمۡ حَسَرَٰتٍۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمُۢ بِمَا يَصۡنَعُونَ

Yanzu wanda aka qawata wa mummunan aikinsa ya gan shi kyakkyawa (zai yi daidai da wanda Allah Ya shiryar)? To lalle Allah Yana vatar da wanda Ya ga dama Ya shiryi wanda Ya ga dama; saboda haka kada ka halakar da kanka don baqin ciki game da su. Lalle Allah Masanin abin da suke aikatawa ne



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 9

وَٱللَّهُ ٱلَّذِيٓ أَرۡسَلَ ٱلرِّيَٰحَ فَتُثِيرُ سَحَابٗا فَسُقۡنَٰهُ إِلَىٰ بَلَدٖ مَّيِّتٖ فَأَحۡيَيۡنَا بِهِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَاۚ كَذَٰلِكَ ٱلنُّشُورُ

Kuma Allah Shi ne wanda ya aiko da iska sai ta motsa hadari, sai Muka koro shi zuwa ga mataccen gari, sai Muka raya qasa da shi bayan mutuwarta. Kamar haka tayar da (matattu) yake



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 10

مَن كَانَ يُرِيدُ ٱلۡعِزَّةَ فَلِلَّهِ ٱلۡعِزَّةُ جَمِيعًاۚ إِلَيۡهِ يَصۡعَدُ ٱلۡكَلِمُ ٱلطَّيِّبُ وَٱلۡعَمَلُ ٱلصَّـٰلِحُ يَرۡفَعُهُۥۚ وَٱلَّذِينَ يَمۡكُرُونَ ٱلسَّيِّـَٔاتِ لَهُمۡ عَذَابٞ شَدِيدٞۖ وَمَكۡرُ أُوْلَـٰٓئِكَ هُوَ يَبُورُ

Wanda ya zamanto yana nufin xaukaka, to xaukaka gaba xayanta ta Allah ce. Daxaxan kalmomi[1] zuwa wurinsa suke hawa, kyakkyawan aiki kuwa shi yake xaukaka shi. Waxanda kuwa suke shirya makirci suna da (sakamakon) azaba mai tsanani, kuma makircin waxannan shi ne yake lalacewa


1- Watau kamar kalmar shahada da karatun Alqur’ani da ambaton Allah.


Surah: Suratu Faxir

Ayah : 11

وَٱللَّهُ خَلَقَكُم مِّن تُرَابٖ ثُمَّ مِن نُّطۡفَةٖ ثُمَّ جَعَلَكُمۡ أَزۡوَٰجٗاۚ وَمَا تَحۡمِلُ مِنۡ أُنثَىٰ وَلَا تَضَعُ إِلَّا بِعِلۡمِهِۦۚ وَمَا يُعَمَّرُ مِن مُّعَمَّرٖ وَلَا يُنقَصُ مِنۡ عُمُرِهِۦٓ إِلَّا فِي كِتَٰبٍۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ

Kuma Allah Ya halicce ku ne daga turvaya sannan daga maniyyi, sannan kuma Ya mayar da ku maza da mata. Kuma mace ba za ta xauki ciki ba, ba kuma za ta haifu ba sai da saninsa. Ba kuma wani mai tsawon rai da za a raya shi, ko kuma wani da za a rage tsawon ransa face yana (rubuce) a cikin Lauhul-Mahafuzu. Wannan kuwa a wurin Allah mai sauqi ne



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 12

وَمَا يَسۡتَوِي ٱلۡبَحۡرَانِ هَٰذَا عَذۡبٞ فُرَاتٞ سَآئِغٞ شَرَابُهُۥ وَهَٰذَا مِلۡحٌ أُجَاجٞۖ وَمِن كُلّٖ تَأۡكُلُونَ لَحۡمٗا طَرِيّٗا وَتَسۡتَخۡرِجُونَ حِلۡيَةٗ تَلۡبَسُونَهَاۖ وَتَرَى ٱلۡفُلۡكَ فِيهِ مَوَاخِرَ لِتَبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِهِۦ وَلَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

Koguna biyu ba za su daidaita ba, wannan na da daxin gaske da sauqin haxiya, wannan kuma mai zartsin gaske ne, daga kowannensu kuma kuna cin nama sabo (ba bushasshe ba), kuna kuma fito da kayan ado (daga gare su) wanda kuke sawa; kuma kana ganin jiragen ruwa suna keta shi (kogin) don ku nemi falalarsa don kuma ku gode (masa)



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 13

يُولِجُ ٱلَّيۡلَ فِي ٱلنَّهَارِ وَيُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِي ٱلَّيۡلِ وَسَخَّرَ ٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَۖ كُلّٞ يَجۡرِي لِأَجَلٖ مُّسَمّٗىۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡ لَهُ ٱلۡمُلۡكُۚ وَٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ مَا يَمۡلِكُونَ مِن قِطۡمِيرٍ

Yana shigar da dare cikin yini, Yana kuma shigar da yini cikin dare, Ya kuma hore rana da wata kowannensu yana tafiya zuwa ga ajali iyakantacce. (Mai yin wannan kuwa) Shi ne Allah Ubangijinku, mulki (kuwa) nasa ne. Waxanda kuwa kuke bauta wa ba Shi ba, ba su mallaki ko da rigar qwallon dabino ba



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 14

إِن تَدۡعُوهُمۡ لَا يَسۡمَعُواْ دُعَآءَكُمۡ وَلَوۡ سَمِعُواْ مَا ٱسۡتَجَابُواْ لَكُمۡۖ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ يَكۡفُرُونَ بِشِرۡكِكُمۡۚ وَلَا يُنَبِّئُكَ مِثۡلُ خَبِيرٖ

Idan kuna kiran su, ba sa jin kiranku, ko da ma sun ji, ba za su amsa muku ba; a ranar alqiyama kuma za su butulce wa shirkarku. Ba kuwa mai ba ka labari kamar cikakken Masani



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 15

۞يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ أَنتُمُ ٱلۡفُقَرَآءُ إِلَى ٱللَّهِۖ وَٱللَّهُ هُوَ ٱلۡغَنِيُّ ٱلۡحَمِيدُ

Ya ku mutane, ku ne mabuqata a wurin Allah; Allah kuma Shi ne Mawadaci, Sha-yabo



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 16

إِن يَشَأۡ يُذۡهِبۡكُمۡ وَيَأۡتِ بِخَلۡقٖ جَدِيدٖ

Idan Ya ga dama sai Ya tafiyar da ku Ya kawo wata sabuwar halittar



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 17

وَمَا ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ بِعَزِيزٖ

Wannan kuwa ba wani abu ne ba da zai gagari Allah



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 18

وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰۚ وَإِن تَدۡعُ مُثۡقَلَةٌ إِلَىٰ حِمۡلِهَا لَا يُحۡمَلۡ مِنۡهُ شَيۡءٞ وَلَوۡ كَانَ ذَا قُرۡبَىٰٓۗ إِنَّمَا تُنذِرُ ٱلَّذِينَ يَخۡشَوۡنَ رَبَّهُم بِٱلۡغَيۡبِ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَۚ وَمَن تَزَكَّىٰ فَإِنَّمَا يَتَزَكَّىٰ لِنَفۡسِهِۦۚ وَإِلَى ٱللَّهِ ٱلۡمَصِيرُ

Kuma wani mai xaukar nauyi ba ya xaukan laifin wani. Idan kuma wani mai nannauyan zunubi ya yi kira zuwa xauke nauyin nasa, ba za a xauke masa komai daga nauyin ba, ko da kuwa xan’uwa ne makusanci. Kai dai kana mai gargaxi ne kawai ga waxanda suke tsoron Ubangijinsu ba tare da ganin Sa ba, suka kuma tsai da salla. Wanda kuwa ya tsarkaka, to ya tsarkaka ne don kansa. Makoma kuma na ga Allah Shi kaxai



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 19

وَمَا يَسۡتَوِي ٱلۡأَعۡمَىٰ وَٱلۡبَصِيرُ

Makaho da mai gani ba za su yi daidai ba



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 20

وَلَا ٱلظُّلُمَٰتُ وَلَا ٱلنُّورُ

Da kuma duhu da haske (ba za su yi daidai ba)



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 21

وَلَا ٱلظِّلُّ وَلَا ٱلۡحَرُورُ

Da kuma inuwa da zafin (rana) (ba za su yi daidai ba)



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 22

وَمَا يَسۡتَوِي ٱلۡأَحۡيَآءُ وَلَا ٱلۡأَمۡوَٰتُۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُسۡمِعُ مَن يَشَآءُۖ وَمَآ أَنتَ بِمُسۡمِعٖ مَّن فِي ٱلۡقُبُورِ

Kuma rayayyu da matattu ba za su yi daidai ba. Lalle Allah Yana jiyar da wanda Ya ga dama; kai kuma ba mai iya jiyar da waxanda suke cikin qaburbura ne ba



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 23

إِنۡ أَنتَ إِلَّا نَذِيرٌ

Kai ba kowa ba ne face mai gargaxi