Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 91

وَٱلَّتِيٓ أَحۡصَنَتۡ فَرۡجَهَا فَنَفَخۡنَا فِيهَا مِن رُّوحِنَا وَجَعَلۡنَٰهَا وَٱبۡنَهَآ ءَايَةٗ لِّلۡعَٰلَمِينَ

(Ka tuna) kuma wadda ta tsare matancinta, sai Muka yi busa a cikinta daga Ruhinmu, Muka kuma sanya ta ita da xanta aya ga talikai



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 92

إِنَّ هَٰذِهِۦٓ أُمَّتُكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَأَنَا۠ رَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُونِ

Lallai wannan addini naku guda xaya ne (wato Musulunci), kuma Ni ne Ubangijinku, to ku bauta min



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 93

وَتَقَطَّعُوٓاْ أَمۡرَهُم بَيۡنَهُمۡۖ كُلٌّ إِلَيۡنَا رَٰجِعُونَ

Sannan sai suka rarraba al’amarinsu (na addini) a tsakaninsu; dukkaninsu dai masu komowa ne zuwa gare Mu



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 94

فَمَن يَعۡمَلۡ مِنَ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَا كُفۡرَانَ لِسَعۡيِهِۦ وَإِنَّا لَهُۥ كَٰتِبُونَ

To duk wanda ya aikata kyawawan ayyuka alhali kuwa shi mumini ne, to babu musantawa ga aikinsa[1], lallai kuma Mu Masu rubuta masa shi ne


1- Watau ba za a yi masa runton aikinsa mai kyau ba, za a yi masa kyakkyawar sakayya ne a kai.


Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 95

وَحَرَٰمٌ عَلَىٰ قَرۡيَةٍ أَهۡلَكۡنَٰهَآ أَنَّهُمۡ لَا يَرۡجِعُونَ

Kuma haramun ne ga (duk) wata al’umma da Muka hallaka cewa za su komo (duniya)



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 96

حَتَّىٰٓ إِذَا فُتِحَتۡ يَأۡجُوجُ وَمَأۡجُوجُ وَهُم مِّن كُلِّ حَدَبٖ يَنسِلُونَ

Har sai lokacin da aka buxe Yajuju da Majuju, su kuwa za su gangaro ne ta kowanne tudu



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 97

وَٱقۡتَرَبَ ٱلۡوَعۡدُ ٱلۡحَقُّ فَإِذَا هِيَ شَٰخِصَةٌ أَبۡصَٰرُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يَٰوَيۡلَنَا قَدۡ كُنَّا فِي غَفۡلَةٖ مِّنۡ هَٰذَا بَلۡ كُنَّا ظَٰلِمِينَ

Kuma alqawarin gaskiya ya gabato, sai ga shi idanuwan waxanda suka kafirta sun yi zuru-zuru (suna cewa): “Kaiconmu! Haqiqa mun kasance cikin gafala game da wannan (ranar); a’a, kai mu dai mun kasance azzalumai ne!”



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 98

إِنَّكُمۡ وَمَا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ حَصَبُ جَهَنَّمَ أَنتُمۡ لَهَا وَٰرِدُونَ

(Sai a ce da su): “Lallai ku da abin da kuke bauta wa ba Allah ba, (duka) makamashin Jahannama ne, kuma ku masu shigar ta ne.”



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 99

لَوۡ كَانَ هَـٰٓؤُلَآءِ ءَالِهَةٗ مَّا وَرَدُوهَاۖ وَكُلّٞ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Da waxancan (gumakan) sun kasance alloli (na gaske) da ba su shiga cikinta ba, dukkaninsu kuwa madawwama ne a cikinta



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 100

لَهُمۡ فِيهَا زَفِيرٞ وَهُمۡ فِيهَا لَا يَسۡمَعُونَ

Suna ta qaraji a cikinta, alhali kuwa su a cikinta ba sa jin (sautin komai)



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 101

إِنَّ ٱلَّذِينَ سَبَقَتۡ لَهُم مِّنَّا ٱلۡحُسۡنَىٰٓ أُوْلَـٰٓئِكَ عَنۡهَا مُبۡعَدُونَ

Lalle waxanda kalmarmu mafi kyau (ta cewa su ‘yan Aljanna ne) ta riga ta tabbata gare su, waxannan waxanda ake nesantawa ne daga gare ta (wutar)



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 102

لَا يَسۡمَعُونَ حَسِيسَهَاۖ وَهُمۡ فِي مَا ٱشۡتَهَتۡ أَنفُسُهُمۡ خَٰلِدُونَ

Ba za su ji hargowarta ba, kuma su masu dawwama ne cikin abin da ransu yake so



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 103

لَا يَحۡزُنُهُمُ ٱلۡفَزَعُ ٱلۡأَكۡبَرُ وَتَتَلَقَّىٰهُمُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ هَٰذَا يَوۡمُكُمُ ٱلَّذِي كُنتُمۡ تُوعَدُونَ

Babbar firgitar (wannan ranar) ba ta samun su, kuma mala’iku za su tare su, (suna cewa): “Wannan ita ce ranar taku wadda kuka zamanto ana yi muku alqawarinta (a duniya).”



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 104

يَوۡمَ نَطۡوِي ٱلسَّمَآءَ كَطَيِّ ٱلسِّجِلِّ لِلۡكُتُبِۚ كَمَا بَدَأۡنَآ أَوَّلَ خَلۡقٖ نُّعِيدُهُۥۚ وَعۡدًا عَلَيۡنَآۚ إِنَّا كُنَّا فَٰعِلِينَ

(Ita ce) ranar da za Mu naxe sama kamar naxin marubuci ga takardu. Kamar yadda Muka qagi halitta da farko (haka) za Mu mai da ita. Wannan alqawari ne da Muka xauka. Lallai Mun kasance Masu aikata (haka)



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 105

وَلَقَدۡ كَتَبۡنَا فِي ٱلزَّبُورِ مِنۢ بَعۡدِ ٱلذِّكۡرِ أَنَّ ٱلۡأَرۡضَ يَرِثُهَا عِبَادِيَ ٱلصَّـٰلِحُونَ

Kuma haqiqa Mun rubuta cikin saukakkun littattafai bayan (an rubuta a Lauhul-Mahfuzu) cewa, ita qasa bayina na gari ne za su gaje ta



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 106

إِنَّ فِي هَٰذَا لَبَلَٰغٗا لِّقَوۡمٍ عَٰبِدِينَ

Lallai a cikin wannan (Alqur’ani) akwai isar da saqo ga mutane masu bauta



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 107

وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ إِلَّا رَحۡمَةٗ لِّلۡعَٰلَمِينَ

Ba Mu aiko ka ba sai don rahama ga talikai



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 108

قُلۡ إِنَّمَا يُوحَىٰٓ إِلَيَّ أَنَّمَآ إِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ فَهَلۡ أَنتُم مُّسۡلِمُونَ

Ka ce (da su): “Abin da kawai ake yiwo min wahayinsa (shi ne) lallai abin bautar ku Allah ne Guda Xaya; to shin ko za ku miqa wuya?”



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 109

فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَقُلۡ ءَاذَنتُكُمۡ عَلَىٰ سَوَآءٖۖ وَإِنۡ أَدۡرِيٓ أَقَرِيبٌ أَم بَعِيدٞ مَّا تُوعَدُونَ

To idan sun ba da baya sai ka ce (da su): “Na sanar da ku cewa ni da ku muna kan abu xaya ne (wato ta-ware). Kuma ni ban sani ba, shin abin da ake yi muku alqawari da shi[1] kusa yake ko kuwa nesa?


1- Watau alqawarin zuwan azabar Allah a gare su.


Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 110

إِنَّهُۥ يَعۡلَمُ ٱلۡجَهۡرَ مِنَ ٱلۡقَوۡلِ وَيَعۡلَمُ مَا تَكۡتُمُونَ

“Lalle Shi (Allah) Yana sane da (abin da kuke) bayyanawa na magana Yana kuma sane da abin da kuke voyewa



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 111

وَإِنۡ أَدۡرِي لَعَلَّهُۥ فِتۡنَةٞ لَّكُمۡ وَمَتَٰعٌ إِلَىٰ حِينٖ

“Kuma ban sani ba ko wataqila shi (jinkirta azabtar da ku) fitina ne a gare ku da kuma jin daxi zuwa wani xan lokaci



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 112

قَٰلَ رَبِّ ٱحۡكُم بِٱلۡحَقِّۗ وَرَبُّنَا ٱلرَّحۡمَٰنُ ٱلۡمُسۡتَعَانُ عَلَىٰ مَا تَصِفُونَ

(Annabi Muhammadu) ya ce: “Ya Ubangijina, Ka yi hukunci (tsakanina da kafirai) da gaskiya. Ubangijinmu kuwa (Shi ne) Ar-Rahamanu Wanda ake neman taimakonsa a kan abin da kuke siffantawa.”



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 1

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُواْ رَبَّكُمۡۚ إِنَّ زَلۡزَلَةَ ٱلسَّاعَةِ شَيۡءٌ عَظِيمٞ

Ya ku mutane, ku kiyaye dokokin Ubangijinku. Lalle girgizar (ranar) alqiyama abu ne mai girma



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 2

يَوۡمَ تَرَوۡنَهَا تَذۡهَلُ كُلُّ مُرۡضِعَةٍ عَمَّآ أَرۡضَعَتۡ وَتَضَعُ كُلُّ ذَاتِ حَمۡلٍ حَمۡلَهَا وَتَرَى ٱلنَّاسَ سُكَٰرَىٰ وَمَا هُم بِسُكَٰرَىٰ وَلَٰكِنَّ عَذَابَ ٱللَّهِ شَدِيدٞ

Ranar da za ku gan ta, (don tsananin firgita) kowacce mai shayarwa za ta manta da abin da ta shayar, kuma kowacce mai ciki ta zubar da cikinta, ka ga kuma mutane suna tangaxi, alhali kuwa ba bugaggu ba ne, sai dai azabar Allah ce mai tsanani



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 3

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُجَٰدِلُ فِي ٱللَّهِ بِغَيۡرِ عِلۡمٖ وَيَتَّبِعُ كُلَّ شَيۡطَٰنٖ مَّرِيدٖ

Daga mutane kuma akwai wanda yake jayayya game da Allah ba tare da wani ilimi ba, kuma yake bin kowanne shaixani mai tsaurin kai



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 4

كُتِبَ عَلَيۡهِ أَنَّهُۥ مَن تَوَلَّاهُ فَأَنَّهُۥ يُضِلُّهُۥ وَيَهۡدِيهِ إِلَىٰ عَذَابِ ٱلسَّعِيرِ

An qaddara masa (wato Shaixan) cewa duk wanda ya rungume shi to haqiqa zai vatar da shi kuma ya ja shi zuwa ga azaba ta (wutar) Sa’ira



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 5

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِن كُنتُمۡ فِي رَيۡبٖ مِّنَ ٱلۡبَعۡثِ فَإِنَّا خَلَقۡنَٰكُم مِّن تُرَابٖ ثُمَّ مِن نُّطۡفَةٖ ثُمَّ مِنۡ عَلَقَةٖ ثُمَّ مِن مُّضۡغَةٖ مُّخَلَّقَةٖ وَغَيۡرِ مُخَلَّقَةٖ لِّنُبَيِّنَ لَكُمۡۚ وَنُقِرُّ فِي ٱلۡأَرۡحَامِ مَا نَشَآءُ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى ثُمَّ نُخۡرِجُكُمۡ طِفۡلٗا ثُمَّ لِتَبۡلُغُوٓاْ أَشُدَّكُمۡۖ وَمِنكُم مَّن يُتَوَفَّىٰ وَمِنكُم مَّن يُرَدُّ إِلَىٰٓ أَرۡذَلِ ٱلۡعُمُرِ لِكَيۡلَا يَعۡلَمَ مِنۢ بَعۡدِ عِلۡمٖ شَيۡـٔٗاۚ وَتَرَى ٱلۡأَرۡضَ هَامِدَةٗ فَإِذَآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡهَا ٱلۡمَآءَ ٱهۡتَزَّتۡ وَرَبَتۡ وَأَنۢبَتَتۡ مِن كُلِّ زَوۡجِۭ بَهِيجٖ

Ya ku mutane, idan kun zamanto cikin kokwanton tashi (bayan mutuwa), to lalle Mu Muka halicce ku daga qasa, sannan daga maniyyi, sannan daga gudan jini, sannan daga tsoka, mai cikakkiyar halitta da kuma wadda ba cikakkiya ba[1], don Mu bayyana muku (Ikonmu). Kuma Muna tabbatar da abin da Muka ga dama a cikin mahaifa har zuwa wani lokaci qayyadajje, sannan kuma Mu fito da ku kuna jarirai, sannan kuma don ku kai cikar qarfinku; daga cikinku akwai wanda za a karvi ransa, akwai kuma wanda za a bari har zuwa mafi qasqantar rayuwa don ya kai ga halin da ba zai san komai ba bayan kuwa da can ya sani. Za ka kuma ga qasa a qeqashe, sannan idan Muka saukar mata da ruwa sai ta girgiza ta kumbura kuma ta fitar da kowanne irin tsiro mai qayatarwa


1- Watau tsokar ta zama wata halitta wadda ba cikakken mutum ba, daga bisani a yi varin ta.


Surah: Suratul Hajji

Ayah : 6

ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡحَقُّ وَأَنَّهُۥ يُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰ وَأَنَّهُۥ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Wannan (kuwa) saboda lalle Allah Shi ne gaskiya, kuma lalle Shi ne Yake raya matattu, kuma lalle Mai iko ne a kan komai



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 7

وَأَنَّ ٱلسَّاعَةَ ءَاتِيَةٞ لَّا رَيۡبَ فِيهَا وَأَنَّ ٱللَّهَ يَبۡعَثُ مَن فِي ٱلۡقُبُورِ

Kuma lalle Alqiyama za ta zo babu kokwanto game da ita, kuma lalle Allah zai tashi waxanda suke cikin qaburbura



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 8

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُجَٰدِلُ فِي ٱللَّهِ بِغَيۡرِ عِلۡمٖ وَلَا هُدٗى وَلَا كِتَٰبٖ مُّنِيرٖ

Daga mutane kuma akwai wanda yake jayayya game da (al’amarin) Allah ba tare da ilimi ba ko shiriya ko kuma wani littafi mai haske