Surah: Suratu Yunus

Ayah : 54

وَلَوۡ أَنَّ لِكُلِّ نَفۡسٖ ظَلَمَتۡ مَا فِي ٱلۡأَرۡضِ لَٱفۡتَدَتۡ بِهِۦۗ وَأَسَرُّواْ ٱلنَّدَامَةَ لَمَّا رَأَوُاْ ٱلۡعَذَابَۖ وَقُضِيَ بَيۡنَهُم بِٱلۡقِسۡطِ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ

Da a ce kowane rai da ya yi zalunci ya mallaki duk abin da yake bayan qasa, to lalle da ya fanshi kansa da shi. Suka kuwa voye nadama a lokacin da suka ga azaba; an kuma yi hukunci tsakaninsu na adalci; ba kuma za a zalunce su ba



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 55

أَلَآ إِنَّ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ أَلَآ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

A saurara, lalle duk abin da yake sammai da qasa na Allah ne. A saurara, lalle alqwarin Allah gaskiya ne, sai dai kuma yawancin mutane ba su sani ba



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 56

هُوَ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Shi ne Yake rayawa Yake kuma kashewa, kuma wurinsa za a mai da ku



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 57

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ قَدۡ جَآءَتۡكُم مَّوۡعِظَةٞ مِّن رَّبِّكُمۡ وَشِفَآءٞ لِّمَا فِي ٱلصُّدُورِ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٞ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ

Ya ku mutane, haqiqa gargaxi ya zo muku daga Ubangijinku da kuma waraka ga abin da yake cikin zukatanku, kuma shiriya ne da rahama ga muminai



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 58

قُلۡ بِفَضۡلِ ٱللَّهِ وَبِرَحۡمَتِهِۦ فَبِذَٰلِكَ فَلۡيَفۡرَحُواْ هُوَ خَيۡرٞ مِّمَّا يَجۡمَعُونَ

Ka ce: “Da falalar Allah da rahamarsa, sai su yi farin ciki da wannan; shi ya fi alheri daga abin da suke tarawa (na dukiya).”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 59

قُلۡ أَرَءَيۡتُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ لَكُم مِّن رِّزۡقٖ فَجَعَلۡتُم مِّنۡهُ حَرَامٗا وَحَلَٰلٗا قُلۡ ءَآللَّهُ أَذِنَ لَكُمۡۖ أَمۡ عَلَى ٱللَّهِ تَفۡتَرُونَ

Ka ce (da su): “Ku ba ni labarin abin da Allah Ya saukar muku na arziki, sannan kuka mayar da wani haram wani kuma halal”. Ka ce: “Yanzu Allah ne Ya yi muku izinin (yin haka), ko kuwa Allah kuke yi wa qage ne?”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 60

وَمَا ظَنُّ ٱلَّذِينَ يَفۡتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَشۡكُرُونَ

Mene ne kuma tsammanin waxanda suke yi wa Allah qagen qarya a ranar alqiyama? Lalle Allah Ma’abocin falala ne ga mutane, sai dai kuma yawancinsu ba sa godewa



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 61

وَمَا تَكُونُ فِي شَأۡنٖ وَمَا تَتۡلُواْ مِنۡهُ مِن قُرۡءَانٖ وَلَا تَعۡمَلُونَ مِنۡ عَمَلٍ إِلَّا كُنَّا عَلَيۡكُمۡ شُهُودًا إِذۡ تُفِيضُونَ فِيهِۚ وَمَا يَعۡزُبُ عَن رَّبِّكَ مِن مِّثۡقَالِ ذَرَّةٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا فِي ٱلسَّمَآءِ وَلَآ أَصۡغَرَ مِن ذَٰلِكَ وَلَآ أَكۡبَرَ إِلَّا فِي كِتَٰبٖ مُّبِينٍ

Kuma babu wani al’amari da (kai Annabi) kake zamantowa cikinsa, babu kuma wani abu na Alqur’ani da kake karantawa, kuma babu wani abu da kuke aikatawa (kai da al’ummarka), sai Mun zamanto Muna kallon ku lokacin da kuke kutsawa cikinsa. Kuma babu wani abu da yake voye wa Ubangijinka daidai da qwayar komayya, a qasa ko a sama ko kuma mafi qanqanta ko mafi girma daga wancan (abin) sai fa yana cikin litttafi mabayyani (Lauhul-Mahafuzu)



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 62

أَلَآ إِنَّ أَوۡلِيَآءَ ٱللَّهِ لَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

A saurara, lalle waliyyan Allah babu wani tsoro a gare su, kuma ba za su yi wani baqin ciki ba



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 63

ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَكَانُواْ يَتَّقُونَ

(Su ne) waxanda suka yi imani kuma suka kasance masu kiyaye dokokin Allah



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 64

لَهُمُ ٱلۡبُشۡرَىٰ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِۚ لَا تَبۡدِيلَ لِكَلِمَٰتِ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ

Suna da albishir a rayuwar duniya da kuma ta lahira. Babu wani sauyi ga kalmomin Allah. Wannan shi ne babban rabo



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 65

وَلَا يَحۡزُنكَ قَوۡلُهُمۡۘ إِنَّ ٱلۡعِزَّةَ لِلَّهِ جَمِيعًاۚ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

Kada kuma wata maganarsu ta baqanta maka rai. Lalle girma gaba xayansa na Allah ne. Shi Mai ji ne, Masani



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 66

أَلَآ إِنَّ لِلَّهِ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِۗ وَمَا يَتَّبِعُ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ شُرَكَآءَۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَإِنۡ هُمۡ إِلَّا يَخۡرُصُونَ

Ku saurara, lalle duk abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa na Allah ne. Waxanda suke bauta wa wani ba Allah ba, ba ababen tarayya (na gaskiya) suke bi ba. Ba abin da suke bi sai mummunan zato, kuma ba abin da suke yi sai shaci-faxi



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 67

هُوَ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلَّيۡلَ لِتَسۡكُنُواْ فِيهِ وَٱلنَّهَارَ مُبۡصِرًاۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَسۡمَعُونَ

Shi ne Wanda Ya sanya muku dare don ku samu nutsuwa, rana kuma don haskakawa. Lalle a game da wannan ba tabbas akwai ayoyi ga mutane masu ji



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 68

قَالُواْ ٱتَّخَذَ ٱللَّهُ وَلَدٗاۗ سُبۡحَٰنَهُۥۖ هُوَ ٱلۡغَنِيُّۖ لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ إِنۡ عِندَكُم مِّن سُلۡطَٰنِۭ بِهَٰذَآۚ أَتَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ

Suke ce Allah Yana da xa! Tsarki ya tabbata gare Shi. Shi Mawadaci ne. Abin da yake cikin sammai da abin da yake qasa nasa ne. Ko kuna da wata hujja ne game da wannan? Yanzu kwa riqa faxar abin da ba ku sani ba game da Allah?



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 69

قُلۡ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَفۡتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ لَا يُفۡلِحُونَ

Ka ce: “Lalle waxanda suke qaga wa Allah qarya ba za su rabauta ba.”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 70

مَتَٰعٞ فِي ٱلدُّنۡيَا ثُمَّ إِلَيۡنَا مَرۡجِعُهُمۡ ثُمَّ نُذِيقُهُمُ ٱلۡعَذَابَ ٱلشَّدِيدَ بِمَا كَانُواْ يَكۡفُرُونَ

Jin daxi ne kawai a cikin duniya, sannan kuma gare Mu ne makomarsu take, sannan Mu xanxana musu azaba mai tsanani saboda abin da suka zamanto suna yi na kafirci



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 71

۞وَٱتۡلُ عَلَيۡهِمۡ نَبَأَ نُوحٍ إِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهِۦ يَٰقَوۡمِ إِن كَانَ كَبُرَ عَلَيۡكُم مَّقَامِي وَتَذۡكِيرِي بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ فَعَلَى ٱللَّهِ تَوَكَّلۡتُ فَأَجۡمِعُوٓاْ أَمۡرَكُمۡ وَشُرَكَآءَكُمۡ ثُمَّ لَا يَكُنۡ أَمۡرُكُمۡ عَلَيۡكُمۡ غُمَّةٗ ثُمَّ ٱقۡضُوٓاْ إِلَيَّ وَلَا تُنظِرُونِ

Ka kuma karanta musu labarin (Annabi) Nuhu, a lokacin da ya ce da mutanensa: “Ya ku mutanena, idan zamana a cikinku da kuma wa’azin da nake muku da ayoyin Allah sun dame ku, to ni fa ga Allah ne kawai na dogara, sai ku tattara al’amarinku ku kuma (ku kira) abokan tarayyarku, sannan kada al’amarin naku ya zama a voye, sannan ku zartar (da shi) a gare ni, kada kuma ku saurara mini



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 72

فَإِن تَوَلَّيۡتُمۡ فَمَا سَأَلۡتُكُم مِّنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَى ٱللَّهِۖ وَأُمِرۡتُ أَنۡ أَكُونَ مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ

“To idan kuka ba da baya, to ban tambaye ku wani lada ba; ladana yana ga Allah; an kuwa umarce ni da in kasance cikin Musulmai.”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 73

فَكَذَّبُوهُ فَنَجَّيۡنَٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ فِي ٱلۡفُلۡكِ وَجَعَلۡنَٰهُمۡ خَلَـٰٓئِفَ وَأَغۡرَقۡنَا ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَاۖ فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُنذَرِينَ

Sai suka qaryata shi, sai Muka tserar da shi da waxanda suke tare da shi a cikin jirgin ruwa, Muka kuma mayar da su masu maye gurbin (waxanda suka gabace su), Muka kuma nutsar da waxanda suka qaryata ayoyinmu. To duba ka ga yadda qarshen waxanda aka yi wa gargaxi ya kasance



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 74

ثُمَّ بَعَثۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِۦ رُسُلًا إِلَىٰ قَوۡمِهِمۡ فَجَآءُوهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَمَا كَانُواْ لِيُؤۡمِنُواْ بِمَا كَذَّبُواْ بِهِۦ مِن قَبۡلُۚ كَذَٰلِكَ نَطۡبَعُ عَلَىٰ قُلُوبِ ٱلۡمُعۡتَدِينَ

Sannan a bayansa (Annabi Nuhu) Muka aika manzanni zuwa ga mutanensu suka zo musu da (ayoyi) mabayyana, ba su zamanto suna gaskata abin da a da can suke qaryata shi ba. Kamar haka ne Muke toshe zukatan masu shisshigi



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 75

ثُمَّ بَعَثۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِم مُّوسَىٰ وَهَٰرُونَ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ بِـَٔايَٰتِنَا فَٱسۡتَكۡبَرُواْ وَكَانُواْ قَوۡمٗا مُّجۡرِمِينَ

Sannan daga bayansu Muka aiko Musa da Haruna zuwa ga Fir’auna shi da jama’arsa da ayoyinmu, sai suka yi girman kai suka kuwa zamanto mutane masu laifi



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 76

فَلَمَّا جَآءَهُمُ ٱلۡحَقُّ مِنۡ عِندِنَا قَالُوٓاْ إِنَّ هَٰذَا لَسِحۡرٞ مُّبِينٞ

To lokacin da gaskiya ta zo musu daga wurinmu sai suka ce: “Lalle wannan tabbas tsafi ne bayyananne.”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 77

قَالَ مُوسَىٰٓ أَتَقُولُونَ لِلۡحَقِّ لَمَّا جَآءَكُمۡۖ أَسِحۡرٌ هَٰذَا وَلَا يُفۡلِحُ ٱلسَّـٰحِرُونَ

Musa ya ce: “Yanzu kwa riqa ce wa gaskiya (tsafi) lokacin da ta zo muku? Yanzu wannan ne tsafin, alhali kuwa matsafa ba sa cin nasara?”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 78

قَالُوٓاْ أَجِئۡتَنَا لِتَلۡفِتَنَا عَمَّا وَجَدۡنَا عَلَيۡهِ ءَابَآءَنَا وَتَكُونَ لَكُمَا ٱلۡكِبۡرِيَآءُ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا نَحۡنُ لَكُمَا بِمُؤۡمِنِينَ

Suka ce: “Yanzu ka zo mana ne don ka raba mu da abin da muka sami iyayenmu a kansa, ku kuma (kai da Haruna) ku zamanto ku ne masu girma a bayan qasa? Mu kam ba za mu yi imani da ku ba!”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 79

وَقَالَ فِرۡعَوۡنُ ٱئۡتُونِي بِكُلِّ سَٰحِرٍ عَلِيمٖ

Fir’auna kuma ya ce: “Ku zo mini da duk wani qwararren matsafi.”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 80

فَلَمَّا جَآءَ ٱلسَّحَرَةُ قَالَ لَهُم مُّوسَىٰٓ أَلۡقُواْ مَآ أَنتُم مُّلۡقُونَ

To lokacin da matsafan suka zo, sai Musa ya ce da su: “Ku jefa duk abin da za ku jefa.”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 81

فَلَمَّآ أَلۡقَوۡاْ قَالَ مُوسَىٰ مَا جِئۡتُم بِهِ ٱلسِّحۡرُۖ إِنَّ ٱللَّهَ سَيُبۡطِلُهُۥٓ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُصۡلِحُ عَمَلَ ٱلۡمُفۡسِدِينَ

To lokacin da suka jefa (kayan tsafinsu), sai Musa ya ce: “Ai abin da kuka zo da shi tsafi ne; lalle ko Allah zai vata shi. Lalle Allah ba Ya gyara aikin mavarnata



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 82

وَيُحِقُّ ٱللَّهُ ٱلۡحَقَّ بِكَلِمَٰتِهِۦ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡمُجۡرِمُونَ

“Allah zai tabbatar da gaskiya da ikonsa ko da kuwa masu manyan laifuka sun qi.”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 83

فَمَآ ءَامَنَ لِمُوسَىٰٓ إِلَّا ذُرِّيَّةٞ مِّن قَوۡمِهِۦ عَلَىٰ خَوۡفٖ مِّن فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِمۡ أَن يَفۡتِنَهُمۡۚ وَإِنَّ فِرۡعَوۡنَ لَعَالٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَإِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلۡمُسۡرِفِينَ

To ba wanda ya yi imani da Musa sai wasu ‘yan samari daga mutanensa don tsoron kada Fir’auna da mutanensa su azabtar da su. Kuma lalle Fir’auna ya tabbata mai girman kai ne a bayan qasa. Lalle kuma shi yana cikin mavarnata