أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ وَلِقَآئِهِۦ فَحَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡ فَلَا نُقِيمُ لَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَزۡنٗا
Waxannan (su ne) waxanda suka kafirce wa ayoyin Ubangijinsu da kuma gamuwa da shi, sai ayyukansu suka lalace, ba za Mu sanya musu wani ma’auni ba a ranar alqiyama
ذَٰلِكَ جَزَآؤُهُمۡ جَهَنَّمُ بِمَا كَفَرُواْ وَٱتَّخَذُوٓاْ ءَايَٰتِي وَرُسُلِي هُزُوًا
Wannan shi ne sakamakonsu, Jahannama, saboda kafircewa da suka yi suka kuma riqi ayoyina da manzannina abin yi wa izgili
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ كَانَتۡ لَهُمۡ جَنَّـٰتُ ٱلۡفِرۡدَوۡسِ نُزُلًا
Lalle waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari to Aljannar Firdausi[1] ita ce ta kasance masaukinsu
1- Aljannar Firdausi ita ce qololuwar Aljanna mafi daraja.
خَٰلِدِينَ فِيهَا لَا يَبۡغُونَ عَنۡهَا حِوَلٗا
Suna masu dawwama a cikinta, ba sa neman wani musaya da ita
قُل لَّوۡ كَانَ ٱلۡبَحۡرُ مِدَادٗا لِّكَلِمَٰتِ رَبِّي لَنَفِدَ ٱلۡبَحۡرُ قَبۡلَ أَن تَنفَدَ كَلِمَٰتُ رَبِّي وَلَوۡ جِئۡنَا بِمِثۡلِهِۦ مَدَدٗا
Ka ce (da su): “Da kogi zai zamanto tawada don (rubuta) kalmomin Ubangijina[1], to lalle da kogin ya qare kafin kalmomin Ubangijina su qare, ko da kuwa Mun zo da qarin wasu (koguna) kamarsa
1- Kalmomin Allah su ne yalwar siffofinsa da iliminsa da qudurarsa.
قُلۡ إِنَّمَآ أَنَا۠ بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡ يُوحَىٰٓ إِلَيَّ أَنَّمَآ إِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ فَمَن كَانَ يَرۡجُواْ لِقَآءَ رَبِّهِۦ فَلۡيَعۡمَلۡ عَمَلٗا صَٰلِحٗا وَلَا يُشۡرِكۡ بِعِبَادَةِ رَبِّهِۦٓ أَحَدَۢا
Ka ce: “Ni dai mutum ne kawai kamarku da ake yi mini wahayi cewa abin bautarku abin bauta ne Xaya; don haka wanda ya kasance yana tsoron gamuwa da Ubangijinsa, to sai ya yi aiki nagari, kada kuma ya tara wani cikin bautar Ubangijinsa.”
كٓهيعٓصٓ
KAF HA YA AIN SAD[1]
1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.
ذِكۡرُ رَحۡمَتِ رَبِّكَ عَبۡدَهُۥ زَكَرِيَّآ
(Wannan) ambaton rahamar Ubangijinka ne (da Ya yi wa) Bawansa Zakariyya
إِذۡ نَادَىٰ رَبَّهُۥ نِدَآءً خَفِيّٗا
Lokacin da ya kira Ubangijinsa (ya roqe Shi) cikin asiri
قَالَ رَبِّ إِنِّي وَهَنَ ٱلۡعَظۡمُ مِنِّي وَٱشۡتَعَلَ ٱلرَّأۡسُ شَيۡبٗا وَلَمۡ أَكُنۢ بِدُعَآئِكَ رَبِّ شَقِيّٗا
Ya ce: “Ya Ubangiji lalle qasusuwana sun yi rauni, kaina kuma ya yi fari fat da furfura, Ubangijina ban kuma zama mai tavewa ba game da roqon Ka
وَإِنِّي خِفۡتُ ٱلۡمَوَٰلِيَ مِن وَرَآءِي وَكَانَتِ ٱمۡرَأَتِي عَاقِرٗا فَهَبۡ لِي مِن لَّدُنكَ وَلِيّٗا
“Kuma lalle ni na ji tsoron dangina a bayana[1], matata kuma ga ta bakarara ce, saboda haka Ka yi mini baiwa daga gare Ka ta (xa) majivinci
1- Watau kada su watsar da kulawa da addini, su shagala da neman abincinsu.
يَرِثُنِي وَيَرِثُ مِنۡ ءَالِ يَعۡقُوبَۖ وَٱجۡعَلۡهُ رَبِّ رَضِيّٗا
“(Wanda) zai gaje ni[1] ya kuma gaji iyalan Ya’aqub; Ubangijina kuma Ka sanya shi yardajje (a wurinka).”
1- Watau ya gaji ilimi da annabta da shugabantar gudanar da harkokin addini.
يَٰزَكَرِيَّآ إِنَّا نُبَشِّرُكَ بِغُلَٰمٍ ٱسۡمُهُۥ يَحۡيَىٰ لَمۡ نَجۡعَل لَّهُۥ مِن قَبۡلُ سَمِيّٗا
(Aka ce): Ya Zakariyya, lalle Muna yi maka albishir da samun xa, sunansa Yahya, ba Mu kuwa sanya wa wani sunan ba gabaninsa
قَالَ رَبِّ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي غُلَٰمٞ وَكَانَتِ ٱمۡرَأَتِي عَاقِرٗا وَقَدۡ بَلَغۡتُ مِنَ ٱلۡكِبَرِ عِتِيّٗا
Ya ce: “Ubangijina ta qaqa zan samu xa, alhali kuwa matata ta zamanto bakarara ce, ni kuma ga shi na tsufa tukuf”
قَالَ كَذَٰلِكَ قَالَ رَبُّكَ هُوَ عَلَيَّ هَيِّنٞ وَقَدۡ خَلَقۡتُكَ مِن قَبۡلُ وَلَمۡ تَكُ شَيۡـٔٗا
Ya ce: “Kamar haka Ubangijinka Ya faxa (cewa): ‘Shi (wannan) mai sauqi ne a wurina, don kuwa haqiqa Na halicce ka alhalin ba ka zama komai ba.’”
قَالَ رَبِّ ٱجۡعَل لِّيٓ ءَايَةٗۖ قَالَ ءَايَتُكَ أَلَّا تُكَلِّمَ ٱلنَّاسَ ثَلَٰثَ لَيَالٖ سَوِيّٗا
Ya ce: “Ubangijina Ka sanya mini wata alama.” Sai (Allah) Ya ce: “Alamarka ita ce ka kasa yi wa mutane magana (tsawon) kwana uku daidai.”
فَخَرَجَ عَلَىٰ قَوۡمِهِۦ مِنَ ٱلۡمِحۡرَابِ فَأَوۡحَىٰٓ إِلَيۡهِمۡ أَن سَبِّحُواْ بُكۡرَةٗ وَعَشِيّٗا
Sannan (Zakariyya) ya fito wa mutanensa daga wurin ibada ya yi musu ishara cewa: “Ku yi tasbihi safe da maraice.”
يَٰيَحۡيَىٰ خُذِ ٱلۡكِتَٰبَ بِقُوَّةٖۖ وَءَاتَيۡنَٰهُ ٱلۡحُكۡمَ صَبِيّٗا
(Allah ya ce): “Ya Yahaya, ka riqi littafin (Attaura) da qarfi”; Muka kuma ba shi annabci tun yana qarami
وَحَنَانٗا مِّن لَّدُنَّا وَزَكَوٰةٗۖ وَكَانَ تَقِيّٗا
Kuma (Muka hore masa) tausayi daga gare Mu da tsarkin (zuciya), ya kuma kasance mai kiyaye dokokin Allah ne
وَبَرَّۢا بِوَٰلِدَيۡهِ وَلَمۡ يَكُن جَبَّارًا عَصِيّٗا
Kuma mai biyayya ga mahaifansa, bai kuma zamanto mai taurin kai mai sava wa (umarnin Allah) ba
وَسَلَٰمٌ عَلَيۡهِ يَوۡمَ وُلِدَ وَيَوۡمَ يَمُوتُ وَيَوۡمَ يُبۡعَثُ حَيّٗا
Kuma aminci ya tabbata a gare shi ranar da aka haife shi da kuma ranar da zai mutu da kuma ranar da za a tashe shi rayayye
وَٱذۡكُرۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ مَرۡيَمَ إِذِ ٱنتَبَذَتۡ مِنۡ أَهۡلِهَا مَكَانٗا شَرۡقِيّٗا
Kuma ka ambaci (labarin) Maryamu a cikin (wannan) Littafi lokacin da ta qaurace wa mutanenta zuwa wani wuri a nahiyar gabas
فَٱتَّخَذَتۡ مِن دُونِهِمۡ حِجَابٗا فَأَرۡسَلۡنَآ إِلَيۡهَا رُوحَنَا فَتَمَثَّلَ لَهَا بَشَرٗا سَوِيّٗا
Sai ta saka shamaki tsakaninta da su (mutanen nata), to sai Muka aiko mata da Ruhinmu (shi ne Jibrilu) ya bayyana gare ta da surar daidaitaccen mutum
قَالَتۡ إِنِّيٓ أَعُوذُ بِٱلرَّحۡمَٰنِ مِنكَ إِن كُنتَ تَقِيّٗا
Ta ce: “Lalle ina neman Allah ya tsare ni daga gare ka idan ka zamanto mai taqawa ne.”
قَالَ إِنَّمَآ أَنَا۠ رَسُولُ رَبِّكِ لِأَهَبَ لَكِ غُلَٰمٗا زَكِيّٗا
Ya ce: “Ni manzo ne kawai na Ubangijinki na zo don in yi miki baiwar xa tsarkakakke.”
قَالَتۡ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي غُلَٰمٞ وَلَمۡ يَمۡسَسۡنِي بَشَرٞ وَلَمۡ أَكُ بَغِيّٗا
Ta ce: “Ta qaqa zan samu xa, alhalin kuwa wani namiji bai tava shafa ta ba, kuma ni ban zamanto mazinaciya ba?”
قَالَ كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِ هُوَ عَلَيَّ هَيِّنٞۖ وَلِنَجۡعَلَهُۥٓ ءَايَةٗ لِّلنَّاسِ وَرَحۡمَةٗ مِّنَّاۚ وَكَانَ أَمۡرٗا مَّقۡضِيّٗا
(Mala’ika) ya ce: “Kamar haka ne Ubangijinki Ya faxa (cewa): “Shi (wannan) mai sauqi ne a wurina, kuma don Mu mayar da shi aya ga mutane da kuma rahama daga gare Mu, kuma (yin haka) ya zamanto al’amari ne tabbatacce (rubuce a Lauhul-Mahafuzu).”
۞فَحَمَلَتۡهُ فَٱنتَبَذَتۡ بِهِۦ مَكَانٗا قَصِيّٗا
Sai ta xauki cikinsa sannan ta (tafi) da shi wani wuri mai nisa
فَأَجَآءَهَا ٱلۡمَخَاضُ إِلَىٰ جِذۡعِ ٱلنَّخۡلَةِ قَالَتۡ يَٰلَيۡتَنِي مِتُّ قَبۡلَ هَٰذَا وَكُنتُ نَسۡيٗا مَّنسِيّٗا
Sai ciwon naquda ya tilasta mata zuwa ga kututturen dabino, ta ce: “Ina ma na mutu tun kafin wannan (abu ya faru), na kuma kasance yasasshiya, mantacciya!”
فَنَادَىٰهَا مِن تَحۡتِهَآ أَلَّا تَحۡزَنِي قَدۡ جَعَلَ رَبُّكِ تَحۡتَكِ سَرِيّٗا
Sai ya kira ta daga qarqashinta[1] cewa: “Kada ki yi baqin ciki, haqiqa Ubangijinki Ya sanya qorama a qarqashinki
1- Watau Annabi Isa ().