وَإِنَّهُۥ عَلَىٰ ذَٰلِكَ لَشَهِيدٞ
Lalle kuma shi shaida ne a kan haka
Share :
وَإِنَّهُۥ لِحُبِّ ٱلۡخَيۡرِ لَشَدِيدٌ
Lalle shi kuma mai tsananin son alheri ne[1]
1- Watau yana da tsananin son dukiya, wannan ne kuma yake sanya shi rowa.
۞أَفَلَا يَعۡلَمُ إِذَا بُعۡثِرَ مَا فِي ٱلۡقُبُورِ
Shin bai sani ba ne idan aka bankaxo abubuwan da suke cikin qaburbura?
وَحُصِّلَ مَا فِي ٱلصُّدُورِ
Aka kuma tattaro abubuwan da suke cikin qiraza?
إِنَّ رَبَّهُم بِهِمۡ يَوۡمَئِذٖ لَّخَبِيرُۢ
Lalle a wannan ranar tabbas Ubangijinsu Masani ne game da su
ٱلۡقَارِعَةُ
Mai qwanqwasa (zukata da tsoro)
مَا ٱلۡقَارِعَةُ
Mece ce mai qwanqwsa (zukata da tsoro)?
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡقَارِعَةُ
Kuma me ya sanar da kai mece ce mai qwanqwasa (zukata da tsoro)?
يَوۡمَ يَكُونُ ٱلنَّاسُ كَٱلۡفَرَاشِ ٱلۡمَبۡثُوثِ
(Ita ce) ranar da mutane za su zama kamar xangon fari masu bazuwa
وَتَكُونُ ٱلۡجِبَالُ كَٱلۡعِهۡنِ ٱلۡمَنفُوشِ
Duwatsu kuma su zama kamar kaxaxxiyar auduga[1]
1- Watau saboda rashin nauyinsu da warwatsuwarsu a cikin sararin sama.
فَأَمَّا مَن ثَقُلَتۡ مَوَٰزِينُهُۥ
To amma wanda ma’aunan ayyukansa suka yi nauyi
فَهُوَ فِي عِيشَةٖ رَّاضِيَةٖ
To shi kam yana cikin rayuwa mai gamsarwa
وَأَمَّا مَنۡ خَفَّتۡ مَوَٰزِينُهُۥ
Amma kuma duk wanda ma’aunan ayyukansa suka yi shafal
فَأُمُّهُۥ هَاوِيَةٞ
To shi makomarsa (wutar) Hawiya ce
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا هِيَهۡ
Kuma me ya sanar da kai mece ce ita?
نَارٌ حَامِيَةُۢ
Wuta ce mai tsananin zafi
أَلۡهَىٰكُمُ ٱلتَّكَاثُرُ
Alfahari da yawan (‘ya’ya da dukiya) ya shagaltar da ku[1]
1- Watau su xauke musu hankali har su kai ga barin xa’ar Allah.
حَتَّىٰ زُرۡتُمُ ٱلۡمَقَابِرَ
Har kuka (mutu kuka) ziyarci qaburbura
كَلَّا سَوۡفَ تَعۡلَمُونَ
A’aha! (haka bai kamace ku ba) da sannu za ku sani
ثُمَّ كَلَّا سَوۡفَ تَعۡلَمُونَ
Sannan a’aha, da sannu za ku sani
كَلَّا لَوۡ تَعۡلَمُونَ عِلۡمَ ٱلۡيَقِينِ
Tabbas da za ku yi sani, sani na sakankancewa[1]
1- Watau wanda babu kokwanto ko kaxan a cikinsa.
لَتَرَوُنَّ ٱلۡجَحِيمَ
Tabbas haqiqa za ku ga wutar Jahimu
ثُمَّ لَتَرَوُنَّهَا عَيۡنَ ٱلۡيَقِينِ
Sannan tabbas haqiqa za ku gan ta gani da ido na sakankancewa
ثُمَّ لَتُسۡـَٔلُنَّ يَوۡمَئِذٍ عَنِ ٱلنَّعِيمِ
Sannan kuma tabbas lalle za a tambaye ku a wannan ranar game da ni’imomin (da kuka mora a duniya)
وَٱلۡعَصۡرِ
Na rantse da zamani[1]
1- Wannan ya qunshi dare da rana waxanda su ne mahallin dukkan ayyukan bayi.
إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَفِي خُسۡرٍ
Lalle mutum yana cikin asara
إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَتَوَاصَوۡاْ بِٱلۡحَقِّ وَتَوَاصَوۡاْ بِٱلصَّبۡرِ
Sai dai waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, suka kuma yi wa juna wasiyya da gaskiya, suka kuma yi wa juna wasiyya da haquri
وَيۡلٞ لِّكُلِّ هُمَزَةٖ لُّمَزَةٍ
Tsananin azaba ya tabbata ga duk wani mai yawan qyafice mai yawan suka[1]
1- Watau yawan qyafice ga mutane, yana kuma yawan sukan su da aibata su a bayan idanuwansu..
ٱلَّذِي جَمَعَ مَالٗا وَعَدَّدَهُۥ
Wanda ya tara dukiya ya qididdige ta
يَحۡسَبُ أَنَّ مَالَهُۥٓ أَخۡلَدَهُۥ
Yana zaton cewa dukiyarsa za ta dawwamar da shi