وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Tsananin azaba ya tabbata a wannan ranar ga masu qaryatawa
Share :
إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي ظِلَٰلٖ وَعُيُونٖ
Lalle masu taqawa suna cikin inuwoyi da idanuwan ruwa
وَفَوَٰكِهَ مِمَّا يَشۡتَهُونَ
Da kuma ababan marmari daga abin da suke sha’awa
كُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ هَنِيٓـَٔۢا بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Ku ci kuma ku sha kuna masu farin ciki saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Lalle Mu kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa
كُلُواْ وَتَمَتَّعُواْ قَلِيلًا إِنَّكُم مُّجۡرِمُونَ
Ku ci kuma ku ji daxi kaxan (a duniya), lalle ku kun tabbata manyan masu laifi
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱرۡكَعُواْ لَا يَرۡكَعُونَ
Idan kuma aka ce da su: “Ku yi ruku’u”, to ba za su yi ruku’u ba
فَبِأَيِّ حَدِيثِۭ بَعۡدَهُۥ يُؤۡمِنُونَ
To da wane irin zance ne bayansa (Alqur’ani) za su yi imani?