Surah: Suratul Hadid

Ayah : 21

سَابِقُوٓاْ إِلَىٰ مَغۡفِرَةٖ مِّن رَّبِّكُمۡ وَجَنَّةٍ عَرۡضُهَا كَعَرۡضِ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ أُعِدَّتۡ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦۚ ذَٰلِكَ فَضۡلُ ٱللَّهِ يُؤۡتِيهِ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ ذُو ٱلۡفَضۡلِ ٱلۡعَظِيمِ

Ku yi rige-rige zuwa neman gafara daga Ubangijinku da Aljanna wadda faxinta kamar faxin sammai da qasa yake, an tanade ta don waxanda suka yi imani da Allah da manzanninsa. Wannan falalar Allah ce da Yake ba da ita ga wanda Ya ga dama. Allah kuwa Ma’abocin falala ne, Mai girma



Surah: Suratul Hadid

Ayah : 22

مَآ أَصَابَ مِن مُّصِيبَةٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا فِيٓ أَنفُسِكُمۡ إِلَّا فِي كِتَٰبٖ مِّن قَبۡلِ أَن نَّبۡرَأَهَآۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ

Babu wani abu da ya samu na musiba a bayan qasa, ko kuma ga kawunanku face yana cikin Littafin (Lauhul Mahafuzu) tun kafin Mu halicce ta (watau halittar). Lalle wannan (a wurin Allah) mai sauqi ne



Surah: Suratul Hadid

Ayah : 23

لِّكَيۡلَا تَأۡسَوۡاْ عَلَىٰ مَا فَاتَكُمۡ وَلَا تَفۡرَحُواْ بِمَآ ءَاتَىٰكُمۡۗ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ كُلَّ مُخۡتَالٖ فَخُورٍ

Don kada ku yi baqin ciki a kan abin da ya kuvuce muku, kada kuma ku yi fariya da abin da Ya ba ku, Allah kuwa ba Ya son duk wani mai taqama, mai fariya



Surah: Suratul Hadid

Ayah : 24

ٱلَّذِينَ يَبۡخَلُونَ وَيَأۡمُرُونَ ٱلنَّاسَ بِٱلۡبُخۡلِۗ وَمَن يَتَوَلَّ فَإِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡغَنِيُّ ٱلۡحَمِيدُ

(Su ne) waxanda suke yin rowa, suke kuma umartar mutane da yin rowar. Wanda kuwa ya ba da baya, to lalle Allah Shi Mawadaci ne, Sha-Yabo



Surah: Suratul Hadid

Ayah : 25

لَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا رُسُلَنَا بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَأَنزَلۡنَا مَعَهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡمِيزَانَ لِيَقُومَ ٱلنَّاسُ بِٱلۡقِسۡطِۖ وَأَنزَلۡنَا ٱلۡحَدِيدَ فِيهِ بَأۡسٞ شَدِيدٞ وَمَنَٰفِعُ لِلنَّاسِ وَلِيَعۡلَمَ ٱللَّهُ مَن يَنصُرُهُۥ وَرُسُلَهُۥ بِٱلۡغَيۡبِۚ إِنَّ ٱللَّهَ قَوِيٌّ عَزِيزٞ

Haqiqa Mun aiko manzanninmu da (ayoyi) mabayyana, Muka kuma saukar da littafi da ma’auni a tare da su (manzannin) don mutane su tsaya da adalci; Muka kuma saukar da baqin qarfe wanda a tare da shi akwai tsananin qarfi da kuma amfani ga mutane, don kuma Allah Ya bayyanar da wanda yake taimakon Sa da manzanninsa a voye. Lalle Allah Mai qarfi ne, Mabuwayi



Surah: Suratul Hadid

Ayah : 26

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا نُوحٗا وَإِبۡرَٰهِيمَ وَجَعَلۡنَا فِي ذُرِّيَّتِهِمَا ٱلنُّبُوَّةَ وَٱلۡكِتَٰبَۖ فَمِنۡهُم مُّهۡتَدٖۖ وَكَثِيرٞ مِّنۡهُمۡ فَٰسِقُونَ

Haqiqa kuma Mun aiko Nuhu da Ibrahimu, Muka kuma sanya annabta da littafi cikin zuriyarsu; To daga cikinsu akwai shiryayyu, masu yawa kuwa daga cikinsu fasiqai ne



Surah: Suratul Hadid

Ayah : 27

ثُمَّ قَفَّيۡنَا عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِم بِرُسُلِنَا وَقَفَّيۡنَا بِعِيسَى ٱبۡنِ مَرۡيَمَ وَءَاتَيۡنَٰهُ ٱلۡإِنجِيلَۖ وَجَعَلۡنَا فِي قُلُوبِ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُ رَأۡفَةٗ وَرَحۡمَةٗۚ وَرَهۡبَانِيَّةً ٱبۡتَدَعُوهَا مَا كَتَبۡنَٰهَا عَلَيۡهِمۡ إِلَّا ٱبۡتِغَآءَ رِضۡوَٰنِ ٱللَّهِ فَمَا رَعَوۡهَا حَقَّ رِعَايَتِهَاۖ فَـَٔاتَيۡنَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنۡهُمۡ أَجۡرَهُمۡۖ وَكَثِيرٞ مِّنۡهُمۡ فَٰسِقُونَ

Sannan a bayansu Muka biyar da manzanninmu, Muka kuma biyar da Isa xan Maryamu Muka kuma ba shi Linjila, kuma Muka sanya jin qai da rahama a cikin zukatan waxanda suka bi shi. Rahbaniyanci[1] kuma su ne suka qago shi, ba Mu wajabta musu shi ba, sai dai (Mun wajabta musu) neman yardar Allah, amma ba su kiyaye shi ba kamar yadda ya kamata; sai Muka bai wa waxanda suka yi imani daga cikinsu ladansu; da yawa kuwa fasiqai ne


1- Bidi’ar Rahbaniyanci ita ce, qaurace wa aure da barin cin daxaxan abubuwa na halal da haramta wa kai wasu abubuwa da Allah ya halatta.


Surah: Suratul Hadid

Ayah : 28

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَءَامِنُواْ بِرَسُولِهِۦ يُؤۡتِكُمۡ كِفۡلَيۡنِ مِن رَّحۡمَتِهِۦ وَيَجۡعَل لَّكُمۡ نُورٗا تَمۡشُونَ بِهِۦ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Ya ku waxanda suka imani, ku kiyaye dokokin Allah, ku kuma yi imani da Manzonsa, zai ba ku rivi biyu na rahamarsa, Ya kuma sanya muku haske da za ku riqa tafiya da shi, kuma Ya gafarta muku. Domin kuwa Allah Mai gafara ne, Mai rahama



Surah: Suratul Hadid

Ayah : 29

لِّئَلَّا يَعۡلَمَ أَهۡلُ ٱلۡكِتَٰبِ أَلَّا يَقۡدِرُونَ عَلَىٰ شَيۡءٖ مِّن فَضۡلِ ٱللَّهِ وَأَنَّ ٱلۡفَضۡلَ بِيَدِ ٱللَّهِ يُؤۡتِيهِ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ ذُو ٱلۡفَضۡلِ ٱلۡعَظِيمِ

Don ma’abota littafi su san cewa ba su da hannu a falalar Allah, don ko lalle falala a hannun Allah take, Yana ba da ita ga wanda Ya ga dama. Allah kuma Ma’abocin babbar falala ne