وَتَذَرُونَ ٱلۡأٓخِرَةَ
Kuna kuma barin lahira
Share :
وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٖ نَّاضِرَةٌ
Wasu fuskokin a wannan rana a ni’imce suke
إِلَىٰ رَبِّهَا نَاظِرَةٞ
Suna masu kallon Ubangijinsu
وَوُجُوهٞ يَوۡمَئِذِۭ بَاسِرَةٞ
Wasu fuskokin kuma a wannan rana a xaxxaure suke
تَظُنُّ أَن يُفۡعَلَ بِهَا فَاقِرَةٞ
Suna tabbatar da cewa, za a saukar musu da wani bala’i
كَلَّآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلتَّرَاقِيَ
Ku saurara, yayin da rai ya iso a karankarama[1]
1- Watau ya zo qasusuwan qirji a lokacin gargarar mutuwa.
وَقِيلَ مَنۡۜ رَاقٖ
Aka kuma ce: “Wane ne mai tawaida[1]?”
1- Watau masu jinya su riqa tambayar junansu cewa, wane ne zai yi masa ruqya ko zai zamu sauqi?
وَظَنَّ أَنَّهُ ٱلۡفِرَاقُ
Ya kuma tabbata cewar (wannan) shi ne rabuwarsa (da duniya)
وَٱلۡتَفَّتِ ٱلسَّاقُ بِٱلسَّاقِ
Kuma tsananin bala’i ya haxu
إِلَىٰ رَبِّكَ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡمَسَاقُ
To zuwa Ubangijinka ne (za a) kora ka a wannan ranar
فَلَا صَدَّقَ وَلَا صَلَّىٰ
To bai ba da gaskiya ba bai kuma yi salla ba
وَلَٰكِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ
Sai dai ya qaryata ya kuma ba da baya
ثُمَّ ذَهَبَ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ يَتَمَطَّىٰٓ
Sannan ya tafi zuwa ga iyalinsa yana taqama
أَوۡلَىٰ لَكَ فَأَوۡلَىٰ
(Azaba) ta doso ka, ta fa doso ka!
ثُمَّ أَوۡلَىٰ لَكَ فَأَوۡلَىٰٓ
Sannan ta doso ka, ta fa doso ka!
أَيَحۡسَبُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَن يُتۡرَكَ سُدًى
Yanzu mutum yana tsammanin za a bar shi haka sasaka[1]?
1- Watau za a qyale shi ya yi abin da ya ga dama ba tare da umarni ko hani ba?
أَلَمۡ يَكُ نُطۡفَةٗ مِّن مَّنِيّٖ يُمۡنَىٰ
Shin bai kasance wani xigo na maniyyi da ake zuba shi (a mahaifa) ba?
ثُمَّ كَانَ عَلَقَةٗ فَخَلَقَ فَسَوَّىٰ
Sannan ya zama gudan jini sannan (Allah) Ya halicce (shi) sai Ya daidaita (shi)?
فَجَعَلَ مِنۡهُ ٱلزَّوۡجَيۡنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰٓ
Sannan Ya halicci dangi biyu daga gare shi, namiji da mace?
أَلَيۡسَ ذَٰلِكَ بِقَٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يُحۡـِۧيَ ٱلۡمَوۡتَىٰ
Yanzu wannan bai zama Mai iko a kan ya raya matattu ba?
هَلۡ أَتَىٰ عَلَى ٱلۡإِنسَٰنِ حِينٞ مِّنَ ٱلدَّهۡرِ لَمۡ يَكُن شَيۡـٔٗا مَّذۡكُورًا
Haqiqa wani yanki na zamani ya zo wa mutum yayin da bai zama wani abin ambato ba[1]
1- Watau babu shi gaba xaya, babu kuma wanda ya san shi.
إِنَّا خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ مِن نُّطۡفَةٍ أَمۡشَاجٖ نَّبۡتَلِيهِ فَجَعَلۡنَٰهُ سَمِيعَۢا بَصِيرًا
Lalle Mun halicci mutum daga maniyyi gamin-gambiza[1] don Mu jarrabe shi, sai Muka sanya shi mai ji mai gani
1- Watau tsakanin na namiji da na mace.
إِنَّا هَدَيۡنَٰهُ ٱلسَّبِيلَ إِمَّا شَاكِرٗا وَإِمَّا كَفُورًا
Lalle Mun bayyana masa hanya, ko dai (ya zama) mai godewa ko kuma mai butulcewa
إِنَّآ أَعۡتَدۡنَا لِلۡكَٰفِرِينَ سَلَٰسِلَاْ وَأَغۡلَٰلٗا وَسَعِيرًا
Lalle Mun tanadar wa kafirai sarqoqi da ququmai da wutar Sa’ira
إِنَّ ٱلۡأَبۡرَارَ يَشۡرَبُونَ مِن كَأۡسٖ كَانَ مِزَاجُهَا كَافُورًا
Lalle mutane nagari suna sha daga wani kofin (giya) da mahaxinta ya kasance kafur ne[1]
1- Watau mai daxin qamshi.
عَيۡنٗا يَشۡرَبُ بِهَا عِبَادُ ٱللَّهِ يُفَجِّرُونَهَا تَفۡجِيرٗا
Wani marmaro ne da bayin Allah suke sha daga gare shi suna vuvvugo shi vuvvugowa ta haqiqa
يُوفُونَ بِٱلنَّذۡرِ وَيَخَافُونَ يَوۡمٗا كَانَ شَرُّهُۥ مُسۡتَطِيرٗا
Suna cika alqawari na bakance suna kuma tsoron ranar da sharrinta ya kasance mai bazuwa ne
وَيُطۡعِمُونَ ٱلطَّعَامَ عَلَىٰ حُبِّهِۦ مِسۡكِينٗا وَيَتِيمٗا وَأَسِيرًا
Suna kuma ciyar da abinci tare da suna son sa ga miskini da maraya da kuma ribataccen yaqi
إِنَّمَا نُطۡعِمُكُمۡ لِوَجۡهِ ٱللَّهِ لَا نُرِيدُ مِنكُمۡ جَزَآءٗ وَلَا شُكُورًا
(Suna cewa): “Mu kawai muna ciyar da ku ne saboda Allah, ba ma nufin sakamako ko godiya daga wurinka
إِنَّا نَخَافُ مِن رَّبِّنَا يَوۡمًا عَبُوسٗا قَمۡطَرِيرٗا
“Lalle mu muna jin tsoron rana mai sa xaure fuska, matsananciya daga Ubangijinmu