وَأَنذِرۡ عَشِيرَتَكَ ٱلۡأَقۡرَبِينَ
Kuma ka gargaxi danginka mafiya kusanci
وَٱخۡفِضۡ جَنَاحَكَ لِمَنِ ٱتَّبَعَكَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Ka kuma tausasa ga wanda ya bi ka daga muminai
فَإِنۡ عَصَوۡكَ فَقُلۡ إِنِّي بَرِيٓءٞ مِّمَّا تَعۡمَلُونَ
To idan suka sava maka sai ka ce: “Ni lalle ba ruwana da abin da kuke aikatawa.”
وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱلۡعَزِيزِ ٱلرَّحِيمِ
Ka kuma dogara ga Mabuwayi, Mai rahama
ٱلَّذِي يَرَىٰكَ حِينَ تَقُومُ
Wanda Yake ganin ka yayin da kake tashi (don yin salla)
وَتَقَلُّبَكَ فِي ٱلسَّـٰجِدِينَ
Da kuma (yayin) jujjuyawarka cikin masu sujjada[1]
1- Watau masallata a sallar jam’i.
إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Haqiqa Shi Mai ji ne, Masani
هَلۡ أُنَبِّئُكُمۡ عَلَىٰ مَن تَنَزَّلُ ٱلشَّيَٰطِينُ
Shin ba Na ba ku labari ba game da wanda shexanu suke saukar masa?
تَنَزَّلُ عَلَىٰ كُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٖ
Suna sauka ne a kan duk wani maqaryaci mai yawan laifi
يُلۡقُونَ ٱلسَّمۡعَ وَأَكۡثَرُهُمۡ كَٰذِبُونَ
Suna jefa wa (bokaye) abin da suka sato jinsa, yawancinsu kuwa maqaryata ne
وَٱلشُّعَرَآءُ يَتَّبِعُهُمُ ٱلۡغَاوُۥنَ
Mawaqa kuwa vatattu ne suke bin su
أَلَمۡ تَرَ أَنَّهُمۡ فِي كُلِّ وَادٖ يَهِيمُونَ
Ba ka ga cewa su kutsawa suke yi cikin kowanne kwari ba[1]?
1- Watau suna kutsawa cikin kowane saqo-saqo na waqe-waqe, wani lokaci ta hanyar yabo, wani lokaci kuma ya hanyar zambo ko alfahari, su faxi qarya da gaskiya.
وَأَنَّهُمۡ يَقُولُونَ مَا لَا يَفۡعَلُونَ
Lalle kuma suna faxar abin da ba sa aikatawa
إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَذَكَرُواْ ٱللَّهَ كَثِيرٗا وَٱنتَصَرُواْ مِنۢ بَعۡدِ مَا ظُلِمُواْۗ وَسَيَعۡلَمُ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ أَيَّ مُنقَلَبٖ يَنقَلِبُونَ
Sai dai waxanda suka yi imani kuma suka yi aiki nagari, kuma suka ambaci Allah da yawa, suka kuma yi sakayya bayan an zalunce su[1]. Waxanda suka yi zalunci kuwa ba da daxewa ba za su san kowace makomar za su koma
1- Watau mawaqan Musulmi waxanda suke mayar da martani a kan mawaqan kafirai masu sukan Musulunci.
طسٓۚ تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡقُرۡءَانِ وَكِتَابٖ مُّبِينٍ
XA SIN[1]. Waxannan ayoyin Alqur’ani ne kuma Littafi mabayyani
1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.
هُدٗى وَبُشۡرَىٰ لِلۡمُؤۡمِنِينَ
(Kuma) shiriya da albishir ne ga muminai
ٱلَّذِينَ يُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَهُم بِٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ يُوقِنُونَ
Waxanda suke tsai da salla, suke kuma ba da zakka suna masu sakankancewa da ranar lahira
إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ زَيَّنَّا لَهُمۡ أَعۡمَٰلَهُمۡ فَهُمۡ يَعۡمَهُونَ
Lalle waxanda ba sa imani da ranar lahira Mun qawata musu ayyukansu, don haka suke ximuwa
أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ لَهُمۡ سُوٓءُ ٱلۡعَذَابِ وَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ هُمُ ٱلۡأَخۡسَرُونَ
Waxannan su ne waxanda suke da mummunar azaba, kuma su ne suka fi hasara a lahira
وَإِنَّكَ لَتُلَقَّى ٱلۡقُرۡءَانَ مِن لَّدُنۡ حَكِيمٍ عَلِيمٍ
Lalle kuma kai tabbas ana yi maka wahayin Alqur’ani ne daga wajen (Allah) Mai hikima, Masani
إِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِأَهۡلِهِۦٓ إِنِّيٓ ءَانَسۡتُ نَارٗا سَـَٔاتِيكُم مِّنۡهَا بِخَبَرٍ أَوۡ ءَاتِيكُم بِشِهَابٖ قَبَسٖ لَّعَلَّكُمۡ تَصۡطَلُونَ
Ka tuna lokacin da Musa ya ce da iyalinsa: “Lalle ni na hango wata wuta, to (zan je) in zo muku da labari, ko kuma in zo muku da xosanen garwashi don ku ji xumi.”
فَلَمَّا جَآءَهَا نُودِيَ أَنۢ بُورِكَ مَن فِي ٱلنَّارِ وَمَنۡ حَوۡلَهَا وَسُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
To lokacin da ya zo mata (wutar) sai aka kira shi cewa, an tsarkake wanda yake cikin wutar da waxanda suke daura da ita (wato mala’iku), kuma tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai
يَٰمُوسَىٰٓ إِنَّهُۥٓ أَنَا ٱللَّهُ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Ya Musa, lalle lamarin dai, Ni ne Allah Mabuwayi, Mai hikima
وَأَلۡقِ عَصَاكَۚ فَلَمَّا رَءَاهَا تَهۡتَزُّ كَأَنَّهَا جَآنّٞ وَلَّىٰ مُدۡبِرٗا وَلَمۡ يُعَقِّبۡۚ يَٰمُوسَىٰ لَا تَخَفۡ إِنِّي لَا يَخَافُ لَدَيَّ ٱلۡمُرۡسَلُونَ
Kuma ka jefar da sandarka. To lokacin da ya gan ta tana jujjuyawa kamar macijiya, sai ya juya da baya a guje bai dawo ba. (Allah ya ce): Ya Musa, kada ka ji tsoro, lalle Ni manzanni ba sa jin tsoro a wurina
إِلَّا مَن ظَلَمَ ثُمَّ بَدَّلَ حُسۡنَۢا بَعۡدَ سُوٓءٖ فَإِنِّي غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Sai dai wanda ya zalunci (kansa), sannan ya musanya kyakkyawa bayan mummuna, to lalle Ni Mai gafara ne, Mai jin qai
وَأَدۡخِلۡ يَدَكَ فِي جَيۡبِكَ تَخۡرُجۡ بَيۡضَآءَ مِنۡ غَيۡرِ سُوٓءٖۖ فِي تِسۡعِ ءَايَٰتٍ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَقَوۡمِهِۦٓۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَوۡمٗا فَٰسِقِينَ
Kuma ka saka hannunka cikin wuyan rigarka, zai fito fari fat ba na cuta ba; (wannan aya ce) daga cikin ayoyi tara zuwa ga Fir’auna da mutanensa. Lalle su sun kasance mutane ne fasiqai
فَلَمَّا جَآءَتۡهُمۡ ءَايَٰتُنَا مُبۡصِرَةٗ قَالُواْ هَٰذَا سِحۡرٞ مُّبِينٞ
To lokacin da ayoyinmu waxanda suke a sarari suka zo musu, sai suka ce: “Wannan sihiri ne mabayyani.”
وَجَحَدُواْ بِهَا وَٱسۡتَيۡقَنَتۡهَآ أَنفُسُهُمۡ ظُلۡمٗا وَعُلُوّٗاۚ فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُفۡسِدِينَ
Suka kuma musanta su don zalunci da girman kai, alhali kuwa zukatansu sun sakankance da su[1]. To sai ka duba ka ga yadda qarshen mavarnata ya kasance
1- Watau a zukatansu sun san gaskiya ce, su kuma a kan qarya suke, amma son zuciya ya hana su su sallama.
وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ وَسُلَيۡمَٰنَ عِلۡمٗاۖ وَقَالَا ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي فَضَّلَنَا عَلَىٰ كَثِيرٖ مِّنۡ عِبَادِهِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Haqiqa kuma Mun bai wa Dawuda da Sulaimana ilimi; suka kuma ce: “Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya fifita mu a kan masu yawa daga bayinsa muminai.”
وَوَرِثَ سُلَيۡمَٰنُ دَاوُۥدَۖ وَقَالَ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ عُلِّمۡنَا مَنطِقَ ٱلطَّيۡرِ وَأُوتِينَا مِن كُلِّ شَيۡءٍۖ إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ ٱلۡفَضۡلُ ٱلۡمُبِينُ
Sulaimanu kuma ya gaji Dawuda[1]; ya kuma ce: “Ya ku waxannan mutane, (watau Yahudawa), an sanar da mu zancen tsuntsaye, kuma an ba mu daga kowane abu (na tafiyar da mulki); lalle wannan tabbas ita ce bayyananniyar falala.”
1- Watau gadon ilimi da annabta da Allah ya ba shi, kamar yadda kuma ya gaji mulkinsa.