Surah: Suratul Baqara

Ayah : 142

۞سَيَقُولُ ٱلسُّفَهَآءُ مِنَ ٱلنَّاسِ مَا وَلَّىٰهُمۡ عَن قِبۡلَتِهِمُ ٱلَّتِي كَانُواْ عَلَيۡهَاۚ قُل لِّلَّهِ ٱلۡمَشۡرِقُ وَٱلۡمَغۡرِبُۚ يَهۡدِي مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Ba da jimawa ba wawayen mutane za su ce: “Mene ne ya sa su juyawa su bar alqibilar da a da suke a kanta?”[1] Ka ce: “Gabas da yamma na Allah ne, Yana shiryar da wanda Ya ga dama zuwa ga tafarki madaidaici.”


1- Kafin saukar aya ta 144, Annabi () da sahabbansa a Makka suna fuskantar Baitul Maqdis yayin sallolinsu. Bayan sun yi hijira zuwa Madina sai Allah ya canza musu alqibla zuwa Ka’aba. Daga nan ne Yahudawa da Mushirikan Larabwa suka samu abin magana.


Surah: Suratul Baqara

Ayah : 143

وَكَذَٰلِكَ جَعَلۡنَٰكُمۡ أُمَّةٗ وَسَطٗا لِّتَكُونُواْ شُهَدَآءَ عَلَى ٱلنَّاسِ وَيَكُونَ ٱلرَّسُولُ عَلَيۡكُمۡ شَهِيدٗاۗ وَمَا جَعَلۡنَا ٱلۡقِبۡلَةَ ٱلَّتِي كُنتَ عَلَيۡهَآ إِلَّا لِنَعۡلَمَ مَن يَتَّبِعُ ٱلرَّسُولَ مِمَّن يَنقَلِبُ عَلَىٰ عَقِبَيۡهِۚ وَإِن كَانَتۡ لَكَبِيرَةً إِلَّا عَلَى ٱلَّذِينَ هَدَى ٱللَّهُۗ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيُضِيعَ إِيمَٰنَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِٱلنَّاسِ لَرَءُوفٞ رَّحِيمٞ

Kamar haka ne Muka sanya ku al’umma tsaka-tsaki (zavavvu) don ku zamo masu shaida ga mutane, kuma Manzo ya zamo mai shaida a gare ku. Kuma ba Mu sanya alqiblar da ka kasance a kanta ba sai don Mu bayyana wanda yake biyayya ga Manzo da wanda zai ja da baya (ya bijire). Kuma lalle wannan babban lamari ne sai dai ga waxanda Allah Ya shiryar. Kuma Allah ba zai tava tozarta imaninku ba. Lalle Allah Mai tausayi ne, Mai jin qai ga mutane



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 144

قَدۡ نَرَىٰ تَقَلُّبَ وَجۡهِكَ فِي ٱلسَّمَآءِۖ فَلَنُوَلِّيَنَّكَ قِبۡلَةٗ تَرۡضَىٰهَاۚ فَوَلِّ وَجۡهَكَ شَطۡرَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِۚ وَحَيۡثُ مَا كُنتُمۡ فَوَلُّواْ وُجُوهَكُمۡ شَطۡرَهُۥۗ وَإِنَّ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ لَيَعۡلَمُونَ أَنَّهُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّهِمۡۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَٰفِلٍ عَمَّا يَعۡمَلُونَ

Haqiqa Mun ga jujjuyawar fuskarka zuwa sama, to lalle za Mu fuskantar da kai zuwa ga alqibilar da za ka yarda da ita. Don haka ka juyar da fuskarka wajajen Masallaci mai alfarma; ku ma (Musulmi) a duk inda kuke to ku juyar da fuskokinku wajajensa. Lalle kuma waxanda aka ba su Littafi suna sane da cewa, lalle shi (wannan canji) gaskiya ne daga Ubangijinsu. Kuma Allah ba rafkananne ba ne game da abin da suke aikatawa



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 145

وَلَئِنۡ أَتَيۡتَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ بِكُلِّ ءَايَةٖ مَّا تَبِعُواْ قِبۡلَتَكَۚ وَمَآ أَنتَ بِتَابِعٖ قِبۡلَتَهُمۡۚ وَمَا بَعۡضُهُم بِتَابِعٖ قِبۡلَةَ بَعۡضٖۚ وَلَئِنِ ٱتَّبَعۡتَ أَهۡوَآءَهُم مِّنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَكَ مِنَ ٱلۡعِلۡمِ إِنَّكَ إِذٗا لَّمِنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Lalle kuma da za ka kawo wa waxanda aka ba su Littafi kowace irin hujja ba za su bi alqibilarka ba; kuma kai ma ba mai bin alqibilarsu ba ne; kuma sashinsu bai zama mai bin alqibilar sashi ba. Kuma haqiqa idan har ka bi soye-soyen zukatansu bayan abin da ya zo maka na gaskiya, to lalle idan ka yi haka tabbas kana cikin azzalumai



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 146

ٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَعۡرِفُونَهُۥ كَمَا يَعۡرِفُونَ أَبۡنَآءَهُمۡۖ وَإِنَّ فَرِيقٗا مِّنۡهُمۡ لَيَكۡتُمُونَ ٱلۡحَقَّ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ

Waxanda Muka ba su Littafi suna sane da shi (Manzon Allah) kamar yadda suke sane da ‘ya’yansu; kuma lalle wani vangare daga cikinsu tabbas suna voye gaskiya alhalin suna sane



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 147

ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُمۡتَرِينَ

Gaskiya kam daga Ubangijinka take, don haka lalle kada ka zama daga cikin masu shakka



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 148

وَلِكُلّٖ وِجۡهَةٌ هُوَ مُوَلِّيهَاۖ فَٱسۡتَبِقُواْ ٱلۡخَيۡرَٰتِۚ أَيۡنَ مَا تَكُونُواْ يَأۡتِ بِكُمُ ٱللَّهُ جَمِيعًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Kuma kowane vangare yana da inda ya sa gaba, don haka sai ku yi gaggawar cim ma alheri. A duk inda kuke Allah zai zo da ku gaba xaya. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 149

وَمِنۡ حَيۡثُ خَرَجۡتَ فَوَلِّ وَجۡهَكَ شَطۡرَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِۖ وَإِنَّهُۥ لَلۡحَقُّ مِن رَّبِّكَۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ

Ko ta ina ka fito, to ka juyar da fuskarka wajajen Masallaci mai alfarma; kuma lalle shi gaskiya ne daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama gafalalle game da abin da kuke aikatawa ba



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 150

وَمِنۡ حَيۡثُ خَرَجۡتَ فَوَلِّ وَجۡهَكَ شَطۡرَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِۚ وَحَيۡثُ مَا كُنتُمۡ فَوَلُّواْ وُجُوهَكُمۡ شَطۡرَهُۥ لِئَلَّا يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَيۡكُمۡ حُجَّةٌ إِلَّا ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنۡهُمۡ فَلَا تَخۡشَوۡهُمۡ وَٱخۡشَوۡنِي وَلِأُتِمَّ نِعۡمَتِي عَلَيۡكُمۡ وَلَعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ

Kuma duk inda ka fita, to ka juyar da fuskarka wajajen Masallaci mai alfarma. Ku ma duk inda kuke to ku juyar da fuskokinku wajajensa, don kada ya zama mutane suna da wata hujja a kanku, sai dai waxanda suka yi zalunci daga cikinsu, don haka kada ku ji tsoron su, ku ji tsorona, kuma domin in cika muku ni’imata, don ku shiriya



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 151

كَمَآ أَرۡسَلۡنَا فِيكُمۡ رَسُولٗا مِّنكُمۡ يَتۡلُواْ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتِنَا وَيُزَكِّيكُمۡ وَيُعَلِّمُكُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَيُعَلِّمُكُم مَّا لَمۡ تَكُونُواْ تَعۡلَمُونَ

Kamar yadda Muka aiko muku da wani manzo daga cikinku, yana karanta muku ayoyinmu, kuma yana tsarkake ku, kuma yana koyar da ku Littafi da Hikima[1], kuma yana koyar da ku abin da a da can ba ku sani ba


1- Hikima, ita ce sunnar Annabi ().


Surah: Suratul Baqara

Ayah : 152

فَٱذۡكُرُونِيٓ أَذۡكُرۡكُمۡ وَٱشۡكُرُواْ لِي وَلَا تَكۡفُرُونِ

Don haka ku ambace Ni, Ni ma zan ambace ku, kuma ku gode Mini, kada kuma ku kafirce Mini



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 153

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱسۡتَعِينُواْ بِٱلصَّبۡرِ وَٱلصَّلَوٰةِۚ إِنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلصَّـٰبِرِينَ

Ya ku waxanda suka yi imani ku nemi taimako ta hanyar haquri da salla. Lalle Allah Yana tare da masu haquri



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 154

وَلَا تَقُولُواْ لِمَن يُقۡتَلُ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أَمۡوَٰتُۢۚ بَلۡ أَحۡيَآءٞ وَلَٰكِن لَّا تَشۡعُرُونَ

Kada kuma ku ce wa waxanda ake kashewa a kan hanyar Allah su matattu ne. A’a, rayayyu ne, sai dai ku ne ba ku sani ba



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 155

وَلَنَبۡلُوَنَّكُم بِشَيۡءٖ مِّنَ ٱلۡخَوۡفِ وَٱلۡجُوعِ وَنَقۡصٖ مِّنَ ٱلۡأَمۡوَٰلِ وَٱلۡأَنفُسِ وَٱلثَّمَرَٰتِۗ وَبَشِّرِ ٱلصَّـٰبِرِينَ

Kuma lalle za Mu jarrabe ku da wani abin tsoro da yunwa da tawayar dukiya da ta rayuka da ta ‘ya’yan itatuwa. Don haka ka yi albishir ga masu haquri



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 156

ٱلَّذِينَ إِذَآ أَصَٰبَتۡهُم مُّصِيبَةٞ قَالُوٓاْ إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّآ إِلَيۡهِ رَٰجِعُونَ

(Su ne) waxanda idan wata musiba ta same su sai su ce: “Lalle mu na Allah ne, kuma lalle mu gare Shi muke komawa.”



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 157

أُوْلَـٰٓئِكَ عَلَيۡهِمۡ صَلَوَٰتٞ مِّن رَّبِّهِمۡ وَرَحۡمَةٞۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُهۡتَدُونَ

Waxannan suna da yabo daga Ubangijinsu da rahama, kuma waxannan su ne shiryayyu



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 158

۞إِنَّ ٱلصَّفَا وَٱلۡمَرۡوَةَ مِن شَعَآئِرِ ٱللَّهِۖ فَمَنۡ حَجَّ ٱلۡبَيۡتَ أَوِ ٱعۡتَمَرَ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡهِ أَن يَطَّوَّفَ بِهِمَاۚ وَمَن تَطَوَّعَ خَيۡرٗا فَإِنَّ ٱللَّهَ شَاكِرٌ عَلِيمٌ

Lalle dutsen Safa da na Marwa suna cikin alamomin bautar Allah, don haka wanda ya je Hajji ga Xakin Allah ko ya je Umara, to babu wani laifi a gare shi ya yi xawafi tsakaninsu. Kuma wanda ya yi biyayya ta hanyar aikata alheri, to lalle Allah Mai godiya ne kuma Masani



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 159

إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكۡتُمُونَ مَآ أَنزَلۡنَا مِنَ ٱلۡبَيِّنَٰتِ وَٱلۡهُدَىٰ مِنۢ بَعۡدِ مَا بَيَّنَّـٰهُ لِلنَّاسِ فِي ٱلۡكِتَٰبِ أُوْلَـٰٓئِكَ يَلۡعَنُهُمُ ٱللَّهُ وَيَلۡعَنُهُمُ ٱللَّـٰعِنُونَ

Lalle waxanda suke voye abin da Muka saukar na hujjoji da shiriya bayan Mun yi bayanin su ga mutane a cikin Littafi, to waxannan su ne Allah Yake la’antar su, kuma masu la’anta su ma suke la’antar su



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 160

إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ وَأَصۡلَحُواْ وَبَيَّنُواْ فَأُوْلَـٰٓئِكَ أَتُوبُ عَلَيۡهِمۡ وَأَنَا ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ

Sai dai waxanda suka tuba kuma suka gyara kuma suka bayyana, to waxannan zan karvi tubansu, kuma lalle Ni Mai karvar tuba ne, Mai jin qai



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 161

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَمَاتُواْ وَهُمۡ كُفَّارٌ أُوْلَـٰٓئِكَ عَلَيۡهِمۡ لَعۡنَةُ ٱللَّهِ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ وَٱلنَّاسِ أَجۡمَعِينَ

Lalle waxanda suka kafirta kuma suka mutu suna kafirai, to waxannan la’anar Allah ta tabbata a kansu da ta mala’iku da mutane gaba xaya



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 162

خَٰلِدِينَ فِيهَا لَا يُخَفَّفُ عَنۡهُمُ ٱلۡعَذَابُ وَلَا هُمۡ يُنظَرُونَ

Suna masu dawwama a cikinta, ba za a sassauta masu azaba ba kuma ba za a saurara musu ba



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 163

وَإِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ لَّآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلرَّحۡمَٰنُ ٱلرَّحِيمُ

Kuma abin bautarku abin bauta ne Guda Xaya, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Shi ne Mai rahama, Mai jin qai



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 164

إِنَّ فِي خَلۡقِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَٱخۡتِلَٰفِ ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ وَٱلۡفُلۡكِ ٱلَّتِي تَجۡرِي فِي ٱلۡبَحۡرِ بِمَا يَنفَعُ ٱلنَّاسَ وَمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مِن مَّآءٖ فَأَحۡيَا بِهِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَا وَبَثَّ فِيهَا مِن كُلِّ دَآبَّةٖ وَتَصۡرِيفِ ٱلرِّيَٰحِ وَٱلسَّحَابِ ٱلۡمُسَخَّرِ بَيۡنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ

Lalle a cikin halittar sammai da qasa da sassavawar dare da rana da jiragen ruwa da suke tafiya a kan ruwa da abin da yake amfanar mutane da kuma abin da Allah Ya saukar daga sama na ruwa, Ya rayar da qasa da shi bayan mutuwarta, Ya kuma yaxa duk wata halitta mai tafiya a cikin (qasa) da jujjuyawar iska, da kuma girgije da aka hore shi tsakanin sama da qasa, lalle akwai ayoyi ga mutane masu hankali



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 165

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَتَّخِذُ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَندَادٗا يُحِبُّونَهُمۡ كَحُبِّ ٱللَّهِۖ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَشَدُّ حُبّٗا لِّلَّهِۗ وَلَوۡ يَرَى ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ إِذۡ يَرَوۡنَ ٱلۡعَذَابَ أَنَّ ٱلۡقُوَّةَ لِلَّهِ جَمِيعٗا وَأَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعَذَابِ

Kuma akwai wasu mutane waxanda suke bauta wa wasu kishiyoyi ba Allah ba; suna son su kamar son Allah; waxanda kuwa suka yi imani sun fi son Allah (fiye da komai). Da a ce waxanda suka yi zalunci za su ga lokacin da suke ido huxu da azaba (to da sun gane) cewa, lalle duk wani qarfi na Allah ne gaba xaya, kuma lalle Allah Mai tsananin azaba ne



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 166

إِذۡ تَبَرَّأَ ٱلَّذِينَ ٱتُّبِعُواْ مِنَ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُواْ وَرَأَوُاْ ٱلۡعَذَابَ وَتَقَطَّعَتۡ بِهِمُ ٱلۡأَسۡبَابُ

Lokacin da waxanda aka yi wa biyayya (shugabanni) za su nisantar da kansu daga waxanda suka yi musu biyayya (mabiya), kuma suka yi arba da azaba, kuma duk wasu alaqoqi da ke tsakaninsu suka yanke



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 167

وَقَالَ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُواْ لَوۡ أَنَّ لَنَا كَرَّةٗ فَنَتَبَرَّأَ مِنۡهُمۡ كَمَا تَبَرَّءُواْ مِنَّاۗ كَذَٰلِكَ يُرِيهِمُ ٱللَّهُ أَعۡمَٰلَهُمۡ حَسَرَٰتٍ عَلَيۡهِمۡۖ وَمَا هُم بِخَٰرِجِينَ مِنَ ٱلنَّارِ

Kuma waxanda suka yi biyayya suka ce: “Ina ma dai muna da wata dama ta komawa (duniya) don mu ma mu nisantar da kanmu daga gare su, kamar yadda suka nisanta kansu daga gare mu?” Kamar haka ne Allah Yake nuna musu ayyukansu suka zama nadama a gare su, kuma su ba masu samun fita ne daga wuta ba



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 168

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ كُلُواْ مِمَّا فِي ٱلۡأَرۡضِ حَلَٰلٗا طَيِّبٗا وَلَا تَتَّبِعُواْ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِۚ إِنَّهُۥ لَكُمۡ عَدُوّٞ مُّبِينٌ

Ya ku mutane, ku ci halal mai daxi na abin da ke bayan qasa, kada kuma ku bi hanyoyin Shaixan, lalle shi maqiyi ne mai bayyana qiyayya a gare ku



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 169

إِنَّمَا يَأۡمُرُكُم بِٱلسُّوٓءِ وَٱلۡفَحۡشَآءِ وَأَن تَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ

Yana umartar ku ne kawai da savo da ayyukan assha da kuma faxin abin da ba ku da ilimi game da shi ku jingina wa Allah



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 170

وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱتَّبِعُواْ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ قَالُواْ بَلۡ نَتَّبِعُ مَآ أَلۡفَيۡنَا عَلَيۡهِ ءَابَآءَنَآۚ أَوَلَوۡ كَانَ ءَابَآؤُهُمۡ لَا يَعۡقِلُونَ شَيۡـٔٗا وَلَا يَهۡتَدُونَ

Idan kuma aka ce musu: “Ku bi abin da Allah Ya saukar”, sai su ce: “A’a, za dai mu bi abin da muka samu iyayenmu a kansa”. To, ko da iyayensu ba sa hankaltar komai, kuma ba sa shiryuwa?



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 171

وَمَثَلُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ كَمَثَلِ ٱلَّذِي يَنۡعِقُ بِمَا لَا يَسۡمَعُ إِلَّا دُعَآءٗ وَنِدَآءٗۚ صُمُّۢ بُكۡمٌ عُمۡيٞ فَهُمۡ لَا يَعۡقِلُونَ

Misalin wadanda suka kafirta kamar misalin wanda yake daga sauti ne ga wanda ba ya jin (komai) sai kira da sowa. Kurame ne, bebaye ne, makafi ne, don haka su ba sa hankalta