وَظِلّٖ مِّن يَحۡمُومٖ
Da kuma inuwa ta turnuqun hayaqi
Share :
لَّا بَارِدٖ وَلَا كَرِيمٍ
Ba mai sanyi ba, kuma ba mai daraja ba
إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَبۡلَ ذَٰلِكَ مُتۡرَفِينَ
Lalle su sun kasance masu holewa ne kafin wannan
وَكَانُواْ يُصِرُّونَ عَلَى ٱلۡحِنثِ ٱلۡعَظِيمِ
Sun kuma kasance suna dogewa a kan zunubi mai girma.[1]
1- Watau babban laifi na kafirci da bautar wanin Allah.
وَكَانُواْ يَقُولُونَ أَئِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابٗا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ
Sun kuma kasance suna cewa: “Yanzu idan mun mutu, mun zama qasa da qasusuwa, yanzu lalle za a tashe mu?
أَوَءَابَآؤُنَا ٱلۡأَوَّلُونَ
“Hakanan ma iyayenmu na farko?”
قُلۡ إِنَّ ٱلۡأَوَّلِينَ وَٱلۡأٓخِرِينَ
Ka ce: “Lalle na farkon da na qarshen
لَمَجۡمُوعُونَ إِلَىٰ مِيقَٰتِ يَوۡمٖ مَّعۡلُومٖ
“Tabbas za a tattara su zuwa wani lokaci na rana sananniya
ثُمَّ إِنَّكُمۡ أَيُّهَا ٱلضَّآلُّونَ ٱلۡمُكَذِّبُونَ
“Sannan lalle ku kuma waxannan vatattu masu qaryatawa
لَأٓكِلُونَ مِن شَجَرٖ مِّن زَقُّومٖ
“Tabbas za ku ci daga bishiyar Zaqqumu[1]
1- Watau wata bishiya ce mafi muni da sharri a wutar jahannama.
فَمَالِـُٔونَ مِنۡهَا ٱلۡبُطُونَ
“Sannan za ku cika cikunanku da ita
فَشَٰرِبُونَ عَلَيۡهِ مِنَ ٱلۡحَمِيمِ
“Sannan za ku sha tafasasshen ruwa a kanta
فَشَٰرِبُونَ شُرۡبَ ٱلۡهِيمِ
“Sannan za ku sha irin shan raquma masu jin qishirwa.”
هَٰذَا نُزُلُهُمۡ يَوۡمَ ٱلدِّينِ
Wannan ita ce gararsu a ranar sakamako
نَحۡنُ خَلَقۡنَٰكُمۡ فَلَوۡلَا تُصَدِّقُونَ
Mu ne Muka halicce ku, me ya sa ba kwa gaskatawa?
أَفَرَءَيۡتُم مَّا تُمۡنُونَ
Ba kwa ganin maniyyi da kuke zubawa
ءَأَنتُمۡ تَخۡلُقُونَهُۥٓ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡخَٰلِقُونَ
Shin ku ne kuke halittar sa, ko kuwa Mu ne Masu halittar?
نَحۡنُ قَدَّرۡنَا بَيۡنَكُمُ ٱلۡمَوۡتَ وَمَا نَحۡنُ بِمَسۡبُوقِينَ
Mu ne Muke qaddara mutuwa a tsakaninku, kuma Mu ba Masu gajiyawa ba ne
عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ أَمۡثَٰلَكُمۡ وَنُنشِئَكُمۡ فِي مَا لَا تَعۡلَمُونَ
A kan Mu musanya irinku Mu kuma halitta ku cikin abin da ba ku sani ba
وَلَقَدۡ عَلِمۡتُمُ ٱلنَّشۡأَةَ ٱلۡأُولَىٰ فَلَوۡلَا تَذَكَّرُونَ
Haqiqa kuma ku kun san halitta ta farko, don me ba kwa wa’azantuwa?
أَفَرَءَيۡتُم مَّا تَحۡرُثُونَ
Ku ba Ni labarin abin da kuke nomawa?
ءَأَنتُمۡ تَزۡرَعُونَهُۥٓ أَمۡ نَحۡنُ ٱلزَّـٰرِعُونَ
Shin ku ne kuke tsiro da shi, ko Mu ne Masu tsirarwar?
لَوۡ نَشَآءُ لَجَعَلۡنَٰهُ حُطَٰمٗا فَظَلۡتُمۡ تَفَكَّهُونَ
Idan da Mun ga dama tabbas da Mun mayar da shi karmami, sai ku wayi gari kuna mamaki
إِنَّا لَمُغۡرَمُونَ
(Kuna cewa): “Lalle mu an xora mana asara.”
بَلۡ نَحۡنُ مَحۡرُومُونَ
“A’a, mu dai an hana mu ne.”
أَفَرَءَيۡتُمُ ٱلۡمَآءَ ٱلَّذِي تَشۡرَبُونَ
Ku ba Ni labarin ruwa wanda kuke sha
ءَأَنتُمۡ أَنزَلۡتُمُوهُ مِنَ ٱلۡمُزۡنِ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡمُنزِلُونَ
Yanzu ku ne kuke sauko da shi daga girgije, ko kuwa Mu ne masu saukarwar?
لَوۡ نَشَآءُ جَعَلۡنَٰهُ أُجَاجٗا فَلَوۡلَا تَشۡكُرُونَ
Da Mun ga dama da Mun mayar da shi (ruwa) mai zartsi, to don me ba kwa godewa?
أَفَرَءَيۡتُمُ ٱلنَّارَ ٱلَّتِي تُورُونَ
Ku ba Ni labarin wutar da kuke kunnawa
ءَأَنتُمۡ أَنشَأۡتُمۡ شَجَرَتَهَآ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡمُنشِـُٔونَ
Yanzu ku ne kuka halicci bishiyarta, ko kuwa Mu ne Masu halittar?