Surah: Suratu Maryam

Ayah : 85

يَوۡمَ نَحۡشُرُ ٱلۡمُتَّقِينَ إِلَى ٱلرَّحۡمَٰنِ وَفۡدٗا

Ranar da za Mu tayar da masu taqawa zuwa ga (Allah) Mai rahama a matsayin manyan baqi



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 86

وَنَسُوقُ ٱلۡمُجۡرِمِينَ إِلَىٰ جَهَنَّمَ وِرۡدٗا

Mu kuma kora kafirai zuwa Jahannama cikin tsananin qishirwa



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 87

لَّا يَمۡلِكُونَ ٱلشَّفَٰعَةَ إِلَّا مَنِ ٱتَّخَذَ عِندَ ٱلرَّحۡمَٰنِ عَهۡدٗا

Ba wani mai ikon yin ceto sai wanda yake da alqawari a wurin (Allah) Mai rahama[1]


1- Watau ya riqe alqawarin da ya yi na imani da Allah da manzanninsa.


Surah: Suratu Maryam

Ayah : 88

وَقَالُواْ ٱتَّخَذَ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَلَدٗا

Suka kuma ce: “(Allah) Mai rahama (wai) yana da xa



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 89

لَّقَدۡ جِئۡتُمۡ شَيۡـًٔا إِدّٗا

Haqiqa kun zo da babban abu (marar daxin ji)



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 90

تَكَادُ ٱلسَّمَٰوَٰتُ يَتَفَطَّرۡنَ مِنۡهُ وَتَنشَقُّ ٱلۡأَرۡضُ وَتَخِرُّ ٱلۡجِبَالُ هَدًّا

Sama ta kusa ta kece saboda shi (mummunan furucin), qasa kuma ta tsage, duwatsu kuma su zube su yi rugu-rugu



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 91

أَن دَعَوۡاْ لِلرَّحۡمَٰنِ وَلَدٗا

Saboda sun yi da’awar Allah Yana da xa!



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 92

وَمَا يَنۢبَغِي لِلرَّحۡمَٰنِ أَن يَتَّخِذَ وَلَدًا

Bai kuwa dace da (Allah) Mai rahama Ya zama Yana da xa ba



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 93

إِن كُلُّ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ إِلَّآ ءَاتِي ٱلرَّحۡمَٰنِ عَبۡدٗا

Ba wani abu da yake cikin sammai da qasa face ya zo wa (Allah) Mai rahama a matsayin bawa



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 94

لَّقَدۡ أَحۡصَىٰهُمۡ وَعَدَّهُمۡ عَدّٗا

Lalle Ya kiyaye da su Ya kuma qididdige su sosai



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 95

وَكُلُّهُمۡ ءَاتِيهِ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فَرۡدًا

Kuma dukkansu kowa zai zo masa a ranar alqiyama shi kaxai



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 96

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ سَيَجۡعَلُ لَهُمُ ٱلرَّحۡمَٰنُ وُدّٗا

Lalle waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki na gari, to (Allah) Mai rahama zai sanya musu qauna[1]


1- Watau zanya farin jininsu a zukatan masoyansa a sama da qasa. Shi ma kuma zai qaunace su.


Surah: Suratu Maryam

Ayah : 97

فَإِنَّمَا يَسَّرۡنَٰهُ بِلِسَانِكَ لِتُبَشِّرَ بِهِ ٱلۡمُتَّقِينَ وَتُنذِرَ بِهِۦ قَوۡمٗا لُّدّٗا

To Mun dai sauqaqe shi (Alqur’ani) da harshenka ne don kawai ka yi wa masu taqawa albishir da shi, ka kuma gargaxi mutane masu tsananin jayayya da shi



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 98

وَكَمۡ أَهۡلَكۡنَا قَبۡلَهُم مِّن قَرۡنٍ هَلۡ تُحِسُّ مِنۡهُم مِّنۡ أَحَدٍ أَوۡ تَسۡمَعُ لَهُمۡ رِكۡزَۢا

Al’umma nawa Muka hallaka a gabaninsu, shin kana jin xuriyar wani daga cikinsu, ko kuwa kana jin ‘yar muryarsu?