فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Da waxanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke qaryatawa?
Share :
وَمِن دُونِهِمَا جَنَّتَانِ
A qasa da su kuma akwai wasu aljannatai guda biyu
مُدۡهَآمَّتَانِ
Masu tsananin kore
فِيهِمَا عَيۡنَانِ نَضَّاخَتَانِ
A cikinsu (kuma) akwai idanuwan (ruwa) guda biyu masu feshi
فِيهِمَا فَٰكِهَةٞ وَنَخۡلٞ وَرُمَّانٞ
A cikinsu (kuma) akwai abin marmari da dabino da ruman
فِيهِنَّ خَيۡرَٰتٌ حِسَانٞ
A cikinsu (watau gidajen Aljannar) akwai mata nagartattu kyawawa
حُورٞ مَّقۡصُورَٰتٞ فِي ٱلۡخِيَامِ
(Matayen) masu fari da baqin ido ne, suna kawwame cikin tantuna
لَمۡ يَطۡمِثۡهُنَّ إِنسٞ قَبۡلَهُمۡ وَلَا جَآنّٞ
Wani mutum ko aljan bai tava shafar su ba a gabaninsu
مُتَّكِـِٔينَ عَلَىٰ رَفۡرَفٍ خُضۡرٖ وَعَبۡقَرِيٍّ حِسَانٖ
Suna kishingixe a kan matasan kai koraye, da kuma kilisai kyawawa
تَبَٰرَكَ ٱسۡمُ رَبِّكَ ذِي ٱلۡجَلَٰلِ وَٱلۡإِكۡرَامِ
Albarkatun sunan Ubangijinka Ma’abocin girma da xaukaka sun yawaita
إِذَا وَقَعَتِ ٱلۡوَاقِعَةُ
Idan mai afkowa ta afku (watau alqiyama)
لَيۡسَ لِوَقۡعَتِهَا كَاذِبَةٌ
Babu wani (rai) mai qaryata aukuwarta
خَافِضَةٞ رَّافِعَةٌ
Mai qasqantarwa ce mai xaukakawa
إِذَا رُجَّتِ ٱلۡأَرۡضُ رَجّٗا
Idan aka girgiza qasa girgizawa
وَبُسَّتِ ٱلۡجِبَالُ بَسّٗا
Aka kuma dandaqe duwatsu dandaqewa
فَكَانَتۡ هَبَآءٗ مُّنۢبَثّٗا
Suka zama qura abar sheqewa
وَكُنتُمۡ أَزۡوَٰجٗا ثَلَٰثَةٗ
Kuka kuma kasance dangogi guda uku
فَأَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ
To ma’abota dama fa, mamakin darajar ma’abota dama!
وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ
Da kuma ma’abota hagu, mamakin wulaqantar ma’abota hagu!
وَٱلسَّـٰبِقُونَ ٱلسَّـٰبِقُونَ
Da kuma masu rige-rige (zuwa alheri)
أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلۡمُقَرَّبُونَ
Waxannan su ne makusanta
فِي جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ
A cikin gidajen Aljanna na ni’ima