ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَالُواْ لِلَّذِينَ كَرِهُواْ مَا نَزَّلَ ٱللَّهُ سَنُطِيعُكُمۡ فِي بَعۡضِ ٱلۡأَمۡرِۖ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ إِسۡرَارَهُمۡ
Wannan kuwa saboda lalle su, sun ce wa waxanda suka qi bin abin da Allah Ya saukar: “Za mu bi ku a wasu al’amura.” Allah kuwa Yana sane da asiransu
فَكَيۡفَ إِذَا تَوَفَّتۡهُمُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ يَضۡرِبُونَ وُجُوهَهُمۡ وَأَدۡبَٰرَهُمۡ
To yaya za su zama lokacin da mala’iku za su karvi rayukansu suna dukan fuskokinsu da bayansu?
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمُ ٱتَّبَعُواْ مَآ أَسۡخَطَ ٱللَّهَ وَكَرِهُواْ رِضۡوَٰنَهُۥ فَأَحۡبَطَ أَعۡمَٰلَهُمۡ
Wannan kuwa saboda lalle su, sun bi abin da yake fusata Allah suka kuma qi bin yardarsa, sai ya rusa ayyukansa
أَمۡ حَسِبَ ٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ أَن لَّن يُخۡرِجَ ٱللَّهُ أَضۡغَٰنَهُمۡ
Ko kuwa waxanda suke da cuta a cikin zukatansu suna tsammanin cewa Allah ba zai fito da qulle-qullen zukatansu ba ne?
وَلَوۡ نَشَآءُ لَأَرَيۡنَٰكَهُمۡ فَلَعَرَفۡتَهُم بِسِيمَٰهُمۡۚ وَلَتَعۡرِفَنَّهُمۡ فِي لَحۡنِ ٱلۡقَوۡلِۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ أَعۡمَٰلَكُمۡ
Kuma da Mun ga dama da tabbas Mun nuna maka su (watau munafukai), to tabbas da ka gane su da alamominsu. Kuma tabbas za ka iya gane su ta hanyar salon maganarsu. Allah kuma Yana sane da ayyukanku
وَلَنَبۡلُوَنَّكُمۡ حَتَّىٰ نَعۡلَمَ ٱلۡمُجَٰهِدِينَ مِنكُمۡ وَٱلصَّـٰبِرِينَ وَنَبۡلُوَاْ أَخۡبَارَكُمۡ
Kuma tabbas za Mu jarraba ku har sai Mun bayyana masu jihadi daga cikinku, da masu haquri, kuma za Mu bayyana halayenku
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَشَآقُّواْ ٱلرَّسُولَ مِنۢ بَعۡدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمُ ٱلۡهُدَىٰ لَن يَضُرُّواْ ٱللَّهَ شَيۡـٔٗا وَسَيُحۡبِطُ أَعۡمَٰلَهُمۡ
Lalle waxanda suka kafirta suka kuma toshe hanyar Allah, kuma suka sava wa Manzo bayan shiriya ta bayyana a gare su, to ba za su tava cutar Allah da komai ba, kuma zai lalata ayyukansu
۞يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَلَا تُبۡطِلُوٓاْ أَعۡمَٰلَكُمۡ
Ya ku waxanda suka yi imani, ku bi Allah, kuma ku bi Manzonsa, kada kuma ku vata ayyukanku[1]
1- Watau ta hanyar aikata kafirci ko munafurci ko riya.
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ ثُمَّ مَاتُواْ وَهُمۡ كُفَّارٞ فَلَن يَغۡفِرَ ٱللَّهُ لَهُمۡ
Lalle waxanda suka kafirta suka kuma toshe hanyar Allah, sannan suka mutu a halin suna kafirai, to Allah ba zai tava gafarta musu ba
فَلَا تَهِنُواْ وَتَدۡعُوٓاْ إِلَى ٱلسَّلۡمِ وَأَنتُمُ ٱلۡأَعۡلَوۡنَ وَٱللَّهُ مَعَكُمۡ وَلَن يَتِرَكُمۡ أَعۡمَٰلَكُمۡ
To kada ku raunana, kuma kada ku kirawo su zuwa sulhu[1], alhali ku ne a sama, Allah kuwa Yana tare da ku, kuma ba zai tauye muku ayyukanku ba
1- Watau gabanin su kafiran su nuna suna son sulhu.
إِنَّمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا لَعِبٞ وَلَهۡوٞۚ وَإِن تُؤۡمِنُواْ وَتَتَّقُواْ يُؤۡتِكُمۡ أُجُورَكُمۡ وَلَا يَسۡـَٔلۡكُمۡ أَمۡوَٰلَكُمۡ
Rayuwar duniya wasa ce da sharholiya kawai. Idan kuwa kuka yi imani kuka kiyaye dokokin Allah, to zai ba ku ladanku, ba kuma zai tambaye ku ku ba da dukiyoyinku (duka) ba
إِن يَسۡـَٔلۡكُمُوهَا فَيُحۡفِكُمۡ تَبۡخَلُواْ وَيُخۡرِجۡ أَضۡغَٰنَكُمۡ
Don ko idan da zai tambaye ku ita (dukiyar gaba xaya) Ya kuma nace muku, to da sai ku yi rowa, Ya kuma fito da qulle-qullen zukatanku
هَـٰٓأَنتُمۡ هَـٰٓؤُلَآءِ تُدۡعَوۡنَ لِتُنفِقُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَمِنكُم مَّن يَبۡخَلُۖ وَمَن يَبۡخَلۡ فَإِنَّمَا يَبۡخَلُ عَن نَّفۡسِهِۦۚ وَٱللَّهُ ٱلۡغَنِيُّ وَأَنتُمُ ٱلۡفُقَرَآءُۚ وَإِن تَتَوَلَّوۡاْ يَسۡتَبۡدِلۡ قَوۡمًا غَيۡرَكُمۡ ثُمَّ لَا يَكُونُوٓاْ أَمۡثَٰلَكُم
To ga ku fa ku xin nan ana kiran ku don ku ciyar a hanyar Allah, to daga cikinku akwai masu yin rowa; wanda kuwa duk ya yi rowa, lalle ya yi wa kansa rowa ne. Allah kuma Mawadaci ne, ku ne mabuqata. Idan kuwa kuka ba da baya to zai canja wasu mutanen ba ku ba, sannan ba za su zama kamar ku ba
إِنَّا فَتَحۡنَا لَكَ فَتۡحٗا مُّبِينٗا
Lalle Mu ne Muka yi maka buxi, buxi mabayyani[1]
1- Watau ya ba shi nasara ta hanyar sulhun Hudaibiyya, wata yarjejeniya da Musulmi suka qulla da Quraishawa a shekara ta shida, don tsagaita yaqi a tsakaninsu har tsawon shekara goma.
لِّيَغۡفِرَ لَكَ ٱللَّهُ مَا تَقَدَّمَ مِن ذَنۢبِكَ وَمَا تَأَخَّرَ وَيُتِمَّ نِعۡمَتَهُۥ عَلَيۡكَ وَيَهۡدِيَكَ صِرَٰطٗا مُّسۡتَقِيمٗا
Don Allah Ya gafarta maka abin da ya gabata na zunubinka, da kuma wanda ya jinkirta, Ya kuma cika maka ni’imarsa, kuma Ya shiryar da kai hanya madaidaiciya
وَيَنصُرَكَ ٱللَّهُ نَصۡرًا عَزِيزًا
Allah kuma zai taimake ka da nasara mai girma
هُوَ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ ٱلسَّكِينَةَ فِي قُلُوبِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ لِيَزۡدَادُوٓاْ إِيمَٰنٗا مَّعَ إِيمَٰنِهِمۡۗ وَلِلَّهِ جُنُودُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمٗا
Shi ne wanda Ya sanya nutsuwa a zukatan muminai[1] don su qara imani a kan imaninsu. Rundunonin sammai da qasa kuma na Allah ne, kuma Allah Ya kasance Masani ne, Mai hikima
1- Watau bayan muminai suna ganin sharuxxan sulhun ba su yi musu daxi ba, amma Allah ya saukar musu da nutsuwa a cikin zukatansu.
لِّيُدۡخِلَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا وَيُكَفِّرَ عَنۡهُمۡ سَيِّـَٔاتِهِمۡۚ وَكَانَ ذَٰلِكَ عِندَ ٱللَّهِ فَوۡزًا عَظِيمٗا
(Ya yi haka ne) don Ya shigar da muminai maza da mata gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu suna masu dawwama a cikinsu, Ya kuma kankare musu laifukansu. Wannan kuwa ya kasance babban rabo ne a wurin Allah
وَيُعَذِّبَ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱلۡمُنَٰفِقَٰتِ وَٱلۡمُشۡرِكِينَ وَٱلۡمُشۡرِكَٰتِ ٱلظَّآنِّينَ بِٱللَّهِ ظَنَّ ٱلسَّوۡءِۚ عَلَيۡهِمۡ دَآئِرَةُ ٱلسَّوۡءِۖ وَغَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡ وَلَعَنَهُمۡ وَأَعَدَّ لَهُمۡ جَهَنَّمَۖ وَسَآءَتۡ مَصِيرٗا
Ya kuma azabtar da munafukai maza da mata, da mushirikai maza da mata, masu munana zato ga Allah. Mummunar azaba ta koma a kansu; kuma Allah Ya yi fushi da su, Ya kuma la’ance su, Ya kuma tanadar musu Jahannama; makoma kuwa ta munana
وَلِلَّهِ جُنُودُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمًا
Kuma rundunonin sammai da qasa na Allah ne. Allah kuwa Ya kasance Mabuwayi ne, Mai hikima
إِنَّآ أَرۡسَلۡنَٰكَ شَٰهِدٗا وَمُبَشِّرٗا وَنَذِيرٗا
Lalle Mu Muka aiko ka don ka zama sheda kuma mai albishir mai gargaxi
لِّتُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَتُعَزِّرُوهُ وَتُوَقِّرُوهُۚ وَتُسَبِّحُوهُ بُكۡرَةٗ وَأَصِيلًا
Don (ku mutane) ku yi imani da Allah da Manzonsa ku kuma taimake shi (wato Annabinsa), kuma ku girmama shi, ku kuma tsarkake Shi (wato Allah) safe da yamma
إِنَّ ٱلَّذِينَ يُبَايِعُونَكَ إِنَّمَا يُبَايِعُونَ ٱللَّهَ يَدُ ٱللَّهِ فَوۡقَ أَيۡدِيهِمۡۚ فَمَن نَّكَثَ فَإِنَّمَا يَنكُثُ عَلَىٰ نَفۡسِهِۦۖ وَمَنۡ أَوۡفَىٰ بِمَا عَٰهَدَ عَلَيۡهُ ٱللَّهَ فَسَيُؤۡتِيهِ أَجۡرًا عَظِيمٗا
Lalle waxanda suka yi maka mubaya’a[1] Allah kawai suke yi wa mubaya’a, Hannun Allah yana saman hannayensu. To duk wanda ya warware, to kansa kawai ya warware wa, wanda kuwa ya cika abin da ya yi wa Allah alqawarinsa, to ba da daxewa ba za Mu ba shi lada mai girma
1- Su ne sahabbai dubu da xari huxu da suka yi wa Annabi () mubaya’ar yaqi a Hudaibiyya, watau Bai’atur Ridhwan.
سَيَقُولُ لَكَ ٱلۡمُخَلَّفُونَ مِنَ ٱلۡأَعۡرَابِ شَغَلَتۡنَآ أَمۡوَٰلُنَا وَأَهۡلُونَا فَٱسۡتَغۡفِرۡ لَنَاۚ يَقُولُونَ بِأَلۡسِنَتِهِم مَّا لَيۡسَ فِي قُلُوبِهِمۡۚ قُلۡ فَمَن يَمۡلِكُ لَكُم مِّنَ ٱللَّهِ شَيۡـًٔا إِنۡ أَرَادَ بِكُمۡ ضَرًّا أَوۡ أَرَادَ بِكُمۡ نَفۡعَۢاۚ بَلۡ كَانَ ٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرَۢا
Waxanda suka qi fita da kai daga cikin mutanen qauye za su ce maka: “Dukiyoyinmu da iyalinmu ne suka shagaltar da mu, sai ka nema mana gafara.” Da harsunansu suna faxar abin da ba ya cikin zukatansu. Ka ce: “To wa zai amfana muku wani abu ne a wajen Allah idan Ya yi nufin ku da cutuwa, ko kuma Ya yi nufin ku da alhairi?” A’a, Allah yana sane da abin da kuka kasance kuna aikatawa
بَلۡ ظَنَنتُمۡ أَن لَّن يَنقَلِبَ ٱلرَّسُولُ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ إِلَىٰٓ أَهۡلِيهِمۡ أَبَدٗا وَزُيِّنَ ذَٰلِكَ فِي قُلُوبِكُمۡ وَظَنَنتُمۡ ظَنَّ ٱلسَّوۡءِ وَكُنتُمۡ قَوۡمَۢا بُورٗا
“A’a, ku dai kun zaci cewa Manzo da muminai ba za su komo wajen iyalinsu ba har abada, aka kuma qawata wannan a cikin zukatanku, kuka kuma yi mummunan zato, kuma kun kasance mutane halakakku.”
وَمَن لَّمۡ يُؤۡمِنۢ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ فَإِنَّآ أَعۡتَدۡنَا لِلۡكَٰفِرِينَ سَعِيرٗا
Duk kuwa wanda bai yi imani da Allah da Manzonsa ba, to lalle Mu Mun tanadi wutar Sa’ira ga kafirai
وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ يَغۡفِرُ لِمَن يَشَآءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَآءُۚ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا
Kuma mulkin sammai da qasa na Allah ne. Yana yin gafara ga wanda Ya ga dama, Yana kuma azabtar da wanda Ya ga dama. Allah kuwa Ya kasance Mai gafara ne, Mai rahama
سَيَقُولُ ٱلۡمُخَلَّفُونَ إِذَا ٱنطَلَقۡتُمۡ إِلَىٰ مَغَانِمَ لِتَأۡخُذُوهَا ذَرُونَا نَتَّبِعۡكُمۡۖ يُرِيدُونَ أَن يُبَدِّلُواْ كَلَٰمَ ٱللَّهِۚ قُل لَّن تَتَّبِعُونَا كَذَٰلِكُمۡ قَالَ ٱللَّهُ مِن قَبۡلُۖ فَسَيَقُولُونَ بَلۡ تَحۡسُدُونَنَاۚ بَلۡ كَانُواْ لَا يَفۡقَهُونَ إِلَّا قَلِيلٗا
Waxanda suka qi fita tare da kai[1] za su ce, lokacin da kuka tafi zuwa wasu wuraren ganima don ku samo ta: “Ku bar mu mu bi ku”[2], suna nufin su musanya zancen Allah ne. Ka ce: “Ba za ku bi mu ba, da ma tuni haka Allah Ya faxa.” To za su ce: “A’a, kuna yi mana hassada ne kawai.” Ba haka ba ne, sun kasance ba sa fahimta ne sai ‘yan kaxan
1- Watau suka fita tare da Annabi () zuwa Makka.
2- Watau zuwa Khaibar.
قُل لِّلۡمُخَلَّفِينَ مِنَ ٱلۡأَعۡرَابِ سَتُدۡعَوۡنَ إِلَىٰ قَوۡمٍ أُوْلِي بَأۡسٖ شَدِيدٖ تُقَٰتِلُونَهُمۡ أَوۡ يُسۡلِمُونَۖ فَإِن تُطِيعُواْ يُؤۡتِكُمُ ٱللَّهُ أَجۡرًا حَسَنٗاۖ وَإِن تَتَوَلَّوۡاْ كَمَا تَوَلَّيۡتُم مِّن قَبۡلُ يُعَذِّبۡكُمۡ عَذَابًا أَلِيمٗا
Ka ce da waxanda suka qi fita tare da kai[1] daga mutanen qauye: “Ba da daxewa ba za a kirawo ku zuwa wurin wasu mutane masu tsananin yaqi don ku yaqe su ko su musulunta. To idan kuka bi (wannan umarni), Allah zai ba ku lada kyakkyawa, idan kuwa kuka ba da baya kamar yadda kuka ba da baya a da can, zai azabtar da ku azaba mai raxaxi.”
1- Watau zuwa Makka.
لَّيۡسَ عَلَى ٱلۡأَعۡمَىٰ حَرَجٞ وَلَا عَلَى ٱلۡأَعۡرَجِ حَرَجٞ وَلَا عَلَى ٱلۡمَرِيضِ حَرَجٞۗ وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ يُدۡخِلۡهُ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ وَمَن يَتَوَلَّ يُعَذِّبۡهُ عَذَابًا أَلِيمٗا
Babu wani laifi a kan makaho, babu kuma wani laifi a kan gurgu, kuma babu wani laifi a kan marar lafiya (game da rashin fita yaqi). Wanda kuwa ya bi Allah da Manzonsa to zai shigar da shi gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, wanda kuma ya ba da baya to zai azabtar da shi azaba mai raxaxi