Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 16

فَأَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ رِيحٗا صَرۡصَرٗا فِيٓ أَيَّامٖ نَّحِسَاتٖ لِّنُذِيقَهُمۡ عَذَابَ ٱلۡخِزۡيِ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَعَذَابُ ٱلۡأٓخِرَةِ أَخۡزَىٰۖ وَهُمۡ لَا يُنصَرُونَ

Sai Muka aiko musu da wata iska mai qara a wasu kwanaki masu cike da shu’umci don Mu xanxana musu azabar kunyata a rayuwar duniya; azabar lahira kuma ta fi kunyatarwa; alhalin su ba za a taimake su ba



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 17

وَأَمَّا ثَمُودُ فَهَدَيۡنَٰهُمۡ فَٱسۡتَحَبُّواْ ٱلۡعَمَىٰ عَلَى ٱلۡهُدَىٰ فَأَخَذَتۡهُمۡ صَٰعِقَةُ ٱلۡعَذَابِ ٱلۡهُونِ بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ

Amma Samudawa kuma sai Muka nuna musu hanyar shiriya, sai suka zavi vata a kan shiriya, sai tsawar azabar wulaqanci ta kama su saboda abin da suka kasance suna tsuwurwuta



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 18

وَنَجَّيۡنَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَكَانُواْ يَتَّقُونَ

Muka kuma tserar da waxanda suka yi imani suka kuma kasance masu kiyaye dokokin Allah



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 19

وَيَوۡمَ يُحۡشَرُ أَعۡدَآءُ ٱللَّهِ إِلَى ٱلنَّارِ فَهُمۡ يُوزَعُونَ

(Ka tuna) kuma ranar da za a tara maqiya Allah zuwa wuta ana kuma kora su



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 20

حَتَّىٰٓ إِذَا مَا جَآءُوهَا شَهِدَ عَلَيۡهِمۡ سَمۡعُهُمۡ وَأَبۡصَٰرُهُمۡ وَجُلُودُهُم بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Har sai lokacin da suka zo mata, jinsu da ganinsu da fatunsu za su ba da shaida a kan abin da suka kasance suna aikatawa



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 21

وَقَالُواْ لِجُلُودِهِمۡ لِمَ شَهِدتُّمۡ عَلَيۡنَاۖ قَالُوٓاْ أَنطَقَنَا ٱللَّهُ ٱلَّذِيٓ أَنطَقَ كُلَّ شَيۡءٖۚ وَهُوَ خَلَقَكُمۡ أَوَّلَ مَرَّةٖ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Sai Suka ce da fatunsu: “Don me kuka ba da shaida a kanmu?” Suka ce: “Allah da Ya bai wa kowane abu ikon yin furuci mu ma Shi Ya ba mu ikon furuci, Shi ne kuma Ya halicce ku tun farko, gare Shi kuma kaxai za a mayar da ku.”



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 22

وَمَا كُنتُمۡ تَسۡتَتِرُونَ أَن يَشۡهَدَ عَلَيۡكُمۡ سَمۡعُكُمۡ وَلَآ أَبۡصَٰرُكُمۡ وَلَا جُلُودُكُمۡ وَلَٰكِن ظَنَنتُمۡ أَنَّ ٱللَّهَ لَا يَعۡلَمُ كَثِيرٗا مِّمَّا تَعۡمَلُونَ

Kuma ba ku kasance kuna voye (ayyukanku) ba, don gudun kada jinku da ganinku da fatunku su ba da shaida a kanku ba, sai dai kuna tsammanin cewa Allah ba Ya sane da yawancin abin da kuke aikatawa



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 23

وَذَٰلِكُمۡ ظَنُّكُمُ ٱلَّذِي ظَنَنتُم بِرَبِّكُمۡ أَرۡدَىٰكُمۡ فَأَصۡبَحۡتُم مِّنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

Wannan kuma shi ne zatonku da kuka yi ga Ubangijinku da ya hallakar da ku, sai kuka wayi gari cikin hasararru



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 24

فَإِن يَصۡبِرُواْ فَٱلنَّارُ مَثۡوٗى لَّهُمۡۖ وَإِن يَسۡتَعۡتِبُواْ فَمَا هُم مِّنَ ٱلۡمُعۡتَبِينَ

To idan ma sun yi haquri wuta ce dai makomarsu; idan kuma suka nemi kawo wani hanzari, to su ba sa cikin waxanda za a karvi hanzarinsu



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 25

۞وَقَيَّضۡنَا لَهُمۡ قُرَنَآءَ فَزَيَّنُواْ لَهُم مَّا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡ وَحَقَّ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقَوۡلُ فِيٓ أُمَمٖ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهِم مِّنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِۖ إِنَّهُمۡ كَانُواْ خَٰسِرِينَ

Muka kuma haxa su da abokai (shaixanu), sai suka qawata musu abin da yake gabansu (na duniya) da abin da yake bayansu (na musun alqiyama), sai kalmar (azaba) ta tabbata a kansu (na zamantowa) cikin al’ummun da suka gabace su na aljannu da mutane; lalle su, sun kasance hasararru



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 26

وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَا تَسۡمَعُواْ لِهَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ وَٱلۡغَوۡاْ فِيهِ لَعَلَّكُمۡ تَغۡلِبُونَ

Waxanda kuma suka kafirta suka ce: “Kada ku saurari wannan Alqur’ani, ku riqa yin hayaniya a cikinsa[1] don ku yi rinjaye.”


1- Watau ku riqa hayaniya da hargowa duk sanda ake karanta shi domin kada mutane su ji abin da ake faxa.


Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 27

فَلَنُذِيقَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ عَذَابٗا شَدِيدٗا وَلَنَجۡزِيَنَّهُمۡ أَسۡوَأَ ٱلَّذِي كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

To tabbas za Mu xanxana wa waxanda suka kafirta azaba mai tsanani, kuma tabbas za mu saka musu da mafi munin abin da suka kasance suna aikatawa



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 28

ذَٰلِكَ جَزَآءُ أَعۡدَآءِ ٱللَّهِ ٱلنَّارُۖ لَهُمۡ فِيهَا دَارُ ٱلۡخُلۡدِ جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ بِـَٔايَٰتِنَا يَجۡحَدُونَ

Wannan fa shi ne sakamakon maqiya Allah (watau) wuta; suna da gidan dawwama a cikinta; sakamako ne saboda abin da suka kasance suna musuntawa na ayoyinmu



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 29

وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ رَبَّنَآ أَرِنَا ٱلَّذَيۡنِ أَضَلَّانَا مِنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ نَجۡعَلۡهُمَا تَحۡتَ أَقۡدَامِنَا لِيَكُونَا مِنَ ٱلۡأَسۡفَلِينَ

Waxanda kuma suka kafirta suka ce: “Ya Ubangijinmu, Ka nuna mana waxanda suka vatar da mu daga aljannu da mutane, mu sanya su a qarqashin dugaduganmu don su zamanto cikin na can qasan qasa.”



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 30

إِنَّ ٱلَّذِينَ قَالُواْ رَبُّنَا ٱللَّهُ ثُمَّ ٱسۡتَقَٰمُواْ تَتَنَزَّلُ عَلَيۡهِمُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ أَلَّا تَخَافُواْ وَلَا تَحۡزَنُواْ وَأَبۡشِرُواْ بِٱلۡجَنَّةِ ٱلَّتِي كُنتُمۡ تُوعَدُونَ

Lalle waxanda suka ce: “Allah ne Ubangijinmu”, sannan suka tsaya kyam, to mala’iku za su sauko musu (lokacin mutuwa suna cewa): “Kada ku tsorata, kuma kada ku yi baqin ciki, kuma ku yi farin ciki da Aljanna wadda kuka kasance ana yi muku alqawarinta



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 31

نَحۡنُ أَوۡلِيَآؤُكُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِۖ وَلَكُمۡ فِيهَا مَا تَشۡتَهِيٓ أَنفُسُكُمۡ وَلَكُمۡ فِيهَا مَا تَدَّعُونَ

“Mu masoyanku ne a rayuwar duniya da kuma ta lahira; kuma a cikinta (Aljanna) za ku sami duk abin da rayukanku suke marmari, za kuma ku sami duk abin da kuke nema a cikinta



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 32

نُزُلٗا مِّنۡ غَفُورٖ رَّحِيمٖ

“Liyafa ce daga (Allah) Mai gafara, Mai jin qai.”



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 33

وَمَنۡ أَحۡسَنُ قَوۡلٗا مِّمَّن دَعَآ إِلَى ٱللَّهِ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا وَقَالَ إِنَّنِي مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ

Wane ne ya fi kyakkyawar magana fiye da wanda ya yi kira zuwa ga Allah ya kuma yi aiki nagari, kuma ya ce: “Lalle ni ina daga cikin Musulmi?”



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 34

وَلَا تَسۡتَوِي ٱلۡحَسَنَةُ وَلَا ٱلسَّيِّئَةُۚ ٱدۡفَعۡ بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ فَإِذَا ٱلَّذِي بَيۡنَكَ وَبَيۡنَهُۥ عَدَٰوَةٞ كَأَنَّهُۥ وَلِيٌّ حَمِيمٞ

Kyakkyawan (abu) da mummuna ba za su zama xaya ba. To ka ture mummuna da abin da ya fi kyau, to sai ka ga wanda yake tsakaninsa da kai gaba ce, ya zamanto kamar wani masoyi ne na qut da qut



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 35

وَمَا يُلَقَّىٰهَآ إِلَّا ٱلَّذِينَ صَبَرُواْ وَمَا يُلَقَّىٰهَآ إِلَّا ذُو حَظٍّ عَظِيمٖ

Ba kowa ake bai wa wannan kyakkyawar xabi’ar ba sai waxanda suka yi haquri, ba kowa ake bai wa ita ba sai mai babban rabo



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 36

وَإِمَّا يَنزَغَنَّكَ مِنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ نَزۡغٞ فَٱسۡتَعِذۡ بِٱللَّهِۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

Idan kuma wani tunzuri daga Shaixan ya tunzura ka, to sai ka nemi tsari daga Allah; lalle Shi Mai ji ne, Masani



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 37

وَمِنۡ ءَايَٰتِهِ ٱلَّيۡلُ وَٱلنَّهَارُ وَٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُۚ لَا تَسۡجُدُواْ لِلشَّمۡسِ وَلَا لِلۡقَمَرِ وَٱسۡجُدُواْۤ لِلَّهِۤ ٱلَّذِي خَلَقَهُنَّ إِن كُنتُمۡ إِيَّاهُ تَعۡبُدُونَ

Kuma dare da wuni da rana da wata suna daga ayoyinsa. Kada ku yi sujjada ga rana ko ga wata, ku yi sujjada ga Allah Wanda Ya halicce su idan har kun kasance Shi kaxai kuke bauta wa



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 38

فَإِنِ ٱسۡتَكۡبَرُواْ فَٱلَّذِينَ عِندَ رَبِّكَ يُسَبِّحُونَ لَهُۥ بِٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ وَهُمۡ لَا يَسۡـَٔمُونَ۩

Idan kuwa sun yi girman kai, to waxanda suke wurin Ubangijinka (mala’iku) suna yi masa tasbihi dare da rana, kuma su ba sa qosawa



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 39

وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَنَّكَ تَرَى ٱلۡأَرۡضَ خَٰشِعَةٗ فَإِذَآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡهَا ٱلۡمَآءَ ٱهۡتَزَّتۡ وَرَبَتۡۚ إِنَّ ٱلَّذِيٓ أَحۡيَاهَا لَمُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰٓۚ إِنَّهُۥ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

Yana kuma daga ayoyinsa cewa lalle za ka ga qasa a qeqashe, to idan Mun saukar mata da ruwa sai ta girgiza ta kumbura (ta fitar da tsirrai). Lalle wanda Ya raya ta Shi ne Mai raya matattu. Lalle Shi Mai iko ne a kan komai



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 40

إِنَّ ٱلَّذِينَ يُلۡحِدُونَ فِيٓ ءَايَٰتِنَا لَا يَخۡفَوۡنَ عَلَيۡنَآۗ أَفَمَن يُلۡقَىٰ فِي ٱلنَّارِ خَيۡرٌ أَم مَّن يَأۡتِيٓ ءَامِنٗا يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ ٱعۡمَلُواْ مَا شِئۡتُمۡ إِنَّهُۥ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٌ

Lalle waxanda suke fanxara game da ayoyinmu[1], ba za su voyu gare Mu ba. Yanzu wanda za a jefa shi a cikin wuta, shi ya fi ko kuma wanda zai zo yana amintacce a ranar alqiyama? Ku aikata abin da kuka ga dama, lalle Shi Mai ganin abin da kuke aikatawa ne


1- Watau suke fanxare wa ayoyinsa, suna qaryata su, suna musunta su da jirkita ma’anoninsa ko canza lafuzansu.


Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 41

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِٱلذِّكۡرِ لَمَّا جَآءَهُمۡۖ وَإِنَّهُۥ لَكِتَٰبٌ عَزِيزٞ

Lalle waxanda suka kafirce wa Alqur’ani lokacin da ya zo musu (tabbas Allah zai saka musu). Lalle kuma shi littafi ne mabuwayi



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 42

لَّا يَأۡتِيهِ ٱلۡبَٰطِلُ مِنۢ بَيۡنِ يَدَيۡهِ وَلَا مِنۡ خَلۡفِهِۦۖ تَنزِيلٞ مِّنۡ حَكِيمٍ حَمِيدٖ

Varna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa; saukakke ne daga Mai hikima, Sha-yabo



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 43

مَّا يُقَالُ لَكَ إِلَّا مَا قَدۡ قِيلَ لِلرُّسُلِ مِن قَبۡلِكَۚ إِنَّ رَبَّكَ لَذُو مَغۡفِرَةٖ وَذُو عِقَابٍ أَلِيمٖ

Ba abin da ake faxa maka sai irin abin da aka faxa wa manzanni a gabaninka[1]. Lalle Ubangijinka Mai gafara ne, kuma Mai uquba mai raxaxi ne


1- Watau na qaryata su da yi musu izgili.


Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 44

وَلَوۡ جَعَلۡنَٰهُ قُرۡءَانًا أَعۡجَمِيّٗا لَّقَالُواْ لَوۡلَا فُصِّلَتۡ ءَايَٰتُهُۥٓۖ ءَا۬عۡجَمِيّٞ وَعَرَبِيّٞۗ قُلۡ هُوَ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ هُدٗى وَشِفَآءٞۚ وَٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ فِيٓ ءَاذَانِهِمۡ وَقۡرٞ وَهُوَ عَلَيۡهِمۡ عَمًىۚ أُوْلَـٰٓئِكَ يُنَادَوۡنَ مِن مَّكَانِۭ بَعِيدٖ

Da Mun sanya shi Alqur’ani Ba’ajame da tabbas za su ce: “Me ya hana a bayyana ayoyinsa? Yanzu (a ce Alqur’ani) Ba’ajame (Annabi kuma) Balarabe?” Ka ce: “Shi ga waxanda suka yi imani shiriya ne da waraka. Waxanda kuwa ba sa yin imani akwai nauyi cikin kunnuwansu, shi kuma makanta ne a gare su.” Waxannan (sun yi kama da waxanda) ake kira daga wuri mai nisa



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 45

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ فَٱخۡتُلِفَ فِيهِۚ وَلَوۡلَا كَلِمَةٞ سَبَقَتۡ مِن رَّبِّكَ لَقُضِيَ بَيۡنَهُمۡۚ وَإِنَّهُمۡ لَفِي شَكّٖ مِّنۡهُ مُرِيبٖ

Haqiqa Mun bai wa Musa Littafin (Attaura), sai aka yi savani a cikinsa, kuma ba don Kalma ta gabata daga Ubangijinka ba, tabbas da an yi hukunci a tsakaninsu. Lalle kuma su, tabbas suna cikin shakka mai sa kokwanto a game da shi