Surah: Suratu Faxir

Ayah : 30

لِيُوَفِّيَهُمۡ أُجُورَهُمۡ وَيَزِيدَهُم مِّن فَضۡلِهِۦٓۚ إِنَّهُۥ غَفُورٞ شَكُورٞ

Domin Ya cika musu ladansu Ya kuma qara musu daga falalarsa. Lalle Shi Mai gafara ne, Mai godiya



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 31

وَٱلَّذِيٓ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ هُوَ ٱلۡحَقُّ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِۗ إِنَّ ٱللَّهَ بِعِبَادِهِۦ لَخَبِيرُۢ بَصِيرٞ

Kuma abin da Muka yiwo maka wahayinsa na Littafi shi ne gaskiya, yana gaskata abin da yake gabaninsa (na littattafai). Lalle Allah game da bayinsa Masani ne, Mai gani



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 32

ثُمَّ أَوۡرَثۡنَا ٱلۡكِتَٰبَ ٱلَّذِينَ ٱصۡطَفَيۡنَا مِنۡ عِبَادِنَاۖ فَمِنۡهُمۡ ظَالِمٞ لِّنَفۡسِهِۦ وَمِنۡهُم مُّقۡتَصِدٞ وَمِنۡهُمۡ سَابِقُۢ بِٱلۡخَيۡرَٰتِ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَضۡلُ ٱلۡكَبِيرُ

Sannan Muka gadar da Littafin ga waxanda Muka zava cikin bayinmu; to daga cikinsu akwai mai cutar kansa[1], akwai kuma mai tsakaitawa a cikinsu[2], kuma akwai wanda ya yi fintinkau a aikata alheri[3] da izinin Allah. Wannan kuwa shi ne falala mai girma


1- Watau ta hanyar aikata laifuffukan da ba su kai kafirci ba.


2- Watau masu aikata wajibai da guje wa haramun ba tare da sun kula da mustahabbai ba.


3- Su ne waxanda suka haxa da aikata mustahabbai da barin makruhi.


Surah: Suratu Faxir

Ayah : 33

جَنَّـٰتُ عَدۡنٖ يَدۡخُلُونَهَا يُحَلَّوۡنَ فِيهَا مِنۡ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٖ وَلُؤۡلُؤٗاۖ وَلِبَاسُهُمۡ فِيهَا حَرِيرٞ

(Watau) gidajen Aljanna na dawwama da za su shige su, za a yi musu ado a cikinsu na awarwaron zinare da kuma lu’ulu’u; tufafinsu a cikinsu (gidajen Aljanna) alharini ne



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 34

وَقَالُواْ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِيٓ أَذۡهَبَ عَنَّا ٱلۡحَزَنَۖ إِنَّ رَبَّنَا لَغَفُورٞ شَكُورٌ

Kuma Su ce: “Yabo ya tabbata ga Allah Wanda Ya yaye mana baqin ciki; lalle Ubangijinmu Mai gafara ne, Mai godiya



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 35

ٱلَّذِيٓ أَحَلَّنَا دَارَ ٱلۡمُقَامَةِ مِن فَضۡلِهِۦ لَا يَمَسُّنَا فِيهَا نَصَبٞ وَلَا يَمَسُّنَا فِيهَا لُغُوبٞ

“Wanda Ya saukar da mu a gidan dawwama don falalarsa, ba wata wahala da za ta shafe mu a cikinsa, kuma ba wata gajiya da za ta shafe mu a cikinsa.”



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 36

وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَهُمۡ نَارُ جَهَنَّمَ لَا يُقۡضَىٰ عَلَيۡهِمۡ فَيَمُوتُواْ وَلَا يُخَفَّفُ عَنۡهُم مِّنۡ عَذَابِهَاۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي كُلَّ كَفُورٖ

Waxanda kuwa suka kafirta suna da (sakamakon) wutar Jahannama, ba za a karvi rayukansu ba balle su mutu, ba kuma za a sauqaqa musu wani abu daga azabarta ba. Kamar haka Muke saka wa kowanne kafiri



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 37

وَهُمۡ يَصۡطَرِخُونَ فِيهَا رَبَّنَآ أَخۡرِجۡنَا نَعۡمَلۡ صَٰلِحًا غَيۡرَ ٱلَّذِي كُنَّا نَعۡمَلُۚ أَوَلَمۡ نُعَمِّرۡكُم مَّا يَتَذَكَّرُ فِيهِ مَن تَذَكَّرَ وَجَآءَكُمُ ٱلنَّذِيرُۖ فَذُوقُواْ فَمَا لِلظَّـٰلِمِينَ مِن نَّصِيرٍ

Su kuwa suna ta kururuwa a cikinta suna cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka fitar da mu, za mu yi aiki nagari, ba irin wanda muka kasance muna aikatawa ba.” (Sai a ce da su): “Yanzu ba Mu raya ku ba gwargwadon lokacin da mai wa’azantuwa zai wa’azantu, kuma mai gargaxi ya zo muku? Sai ku xanxani (azaba), sannan azzalumai ba su da wani mataimaki.”



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 38

إِنَّ ٱللَّهَ عَٰلِمُ غَيۡبِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّهُۥ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ

Lalle Allah Masanin gaibin sammai da qasa ne. Lalle Shi Masanin abubuwan da suke cikin zukata ne



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 39

هُوَ ٱلَّذِي جَعَلَكُمۡ خَلَـٰٓئِفَ فِي ٱلۡأَرۡضِۚ فَمَن كَفَرَ فَعَلَيۡهِ كُفۡرُهُۥۖ وَلَا يَزِيدُ ٱلۡكَٰفِرِينَ كُفۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ إِلَّا مَقۡتٗاۖ وَلَا يَزِيدُ ٱلۡكَٰفِرِينَ كُفۡرُهُمۡ إِلَّا خَسَارٗا

Shi ne wanda Ya sanya ku halifofi a bayan qasa. Saboda haka wanda ya kafirta sakamakon kafircinsa yana kansa, kuma kafircin kafirai ba zai qara musu komai ba a wurin Ubangijinsu sai qiyayya; kuma kafircin kafirai ba zai qara musu komai ba sai hasara



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 40

قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ شُرَكَآءَكُمُ ٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَرُونِي مَاذَا خَلَقُواْ مِنَ ٱلۡأَرۡضِ أَمۡ لَهُمۡ شِرۡكٞ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ أَمۡ ءَاتَيۡنَٰهُمۡ كِتَٰبٗا فَهُمۡ عَلَىٰ بَيِّنَتٖ مِّنۡهُۚ بَلۡ إِن يَعِدُ ٱلظَّـٰلِمُونَ بَعۡضُهُم بَعۡضًا إِلَّا غُرُورًا

Ka ce: “Ku ba ni labarin abokan tarayyar naku da kuke bauta wa ba Allah ba, ku nuna min abin da suka halitta daga qasa, ko kuma suna da wata tarayya ne a cikin (halittar) sammai, ko kuma Mun ba su wani littafi ne, saboda haka suke da wata hujja daga wajensa?” Ba haka ba ne, ba dai abin da azzalumai suke wa juna alqawari da shi in ban da ruxi



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 41

۞إِنَّ ٱللَّهَ يُمۡسِكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ أَن تَزُولَاۚ وَلَئِن زَالَتَآ إِنۡ أَمۡسَكَهُمَا مِنۡ أَحَدٖ مِّنۢ بَعۡدِهِۦٓۚ إِنَّهُۥ كَانَ حَلِيمًا غَفُورٗا

Lalle Allah ne Yake riqe da sammai da qasa don kada su ruguje. Lallai kuwa idan da za su ruguje, to ba wani mai riqe su in ba Shi ba. Lalle Shi (Allah) Ya kasance Mai haquri ne, Mai gafara



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 42

وَأَقۡسَمُواْ بِٱللَّهِ جَهۡدَ أَيۡمَٰنِهِمۡ لَئِن جَآءَهُمۡ نَذِيرٞ لَّيَكُونُنَّ أَهۡدَىٰ مِنۡ إِحۡدَى ٱلۡأُمَمِۖ فَلَمَّا جَآءَهُمۡ نَذِيرٞ مَّا زَادَهُمۡ إِلَّا نُفُورًا

Suka kuma rantse da Allah iya rantsuwarsu cewa, lallai idan mai gargaxi ya zo musu, za su zamanto mafiya shiriya daga xayan al’ummu; sannan lokacin da mai gargaxi ya zo musu ba abin da ya qara musu sai nisanta (daga shiriya)



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 43

ٱسۡتِكۡبَارٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَكۡرَ ٱلسَّيِّيِٕۚ وَلَا يَحِيقُ ٱلۡمَكۡرُ ٱلسَّيِّئُ إِلَّا بِأَهۡلِهِۦۚ فَهَلۡ يَنظُرُونَ إِلَّا سُنَّتَ ٱلۡأَوَّلِينَۚ فَلَن تَجِدَ لِسُنَّتِ ٱللَّهِ تَبۡدِيلٗاۖ وَلَن تَجِدَ لِسُنَّتِ ٱللَّهِ تَحۡوِيلًا

Don girman kai a bayan qasa da kuma makirci mummuna. (Sakamakon) makirci mummuna kuwa ba ya sauka sai a kan masu shi. Ba abin da suke saurare in ban da sunnar da ta sami mutanen farko. Sannan ba za ka tava samun wani canji ba game da sunnar Allah; kuma ba za ka sami wani sauyi ba game da sunnar Allah



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 44

أَوَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ وَكَانُوٓاْ أَشَدَّ مِنۡهُمۡ قُوَّةٗۚ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيُعۡجِزَهُۥ مِن شَيۡءٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَلِيمٗا قَدِيرٗا

Shin ba su yi tafiya ba ne a cikin qasa, sai su ga yaya qarshen waxanda suke gabaninsu ya kasance, alhali kuwa sun zamanto qarfafa fiye da su? Ba kuwa wani abu da zai gagari Allah a cikin sammai ko a cikin qasa. Lalle Shi Ya kasance Masani ne, Mai iko



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 45

وَلَوۡ يُؤَاخِذُ ٱللَّهُ ٱلنَّاسَ بِمَا كَسَبُواْ مَا تَرَكَ عَلَىٰ ظَهۡرِهَا مِن دَآبَّةٖ وَلَٰكِن يُؤَخِّرُهُمۡ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗىۖ فَإِذَا جَآءَ أَجَلُهُمۡ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِعِبَادِهِۦ بَصِيرَۢا

Idan da Allah Yana (saurin) damqar mutane saboda laifin da suka aikata, to da bai bar kowane mai rai ba a bayan qasa, sai dai kuma Yana saurara musu ne zuwa wani lokaci qayyadajje; to idan lokacin nasu ya zo, to lalle Allah Ya kasance Mai ganin bayinsa ne, (zai kuwa saka musu)



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 1

يسٓ

YA SIN[1]


1- Duba Suratul Baqara aya ta 1, hashiya ta 8.


Surah: Suratu Yasin

Ayah : 2

وَٱلۡقُرۡءَانِ ٱلۡحَكِيمِ

Na rantse da Alqur’ani mai hikima



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 3

إِنَّكَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ

Lalle kai (Manzon Allah) tabbas kana daga cikin manzanni



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 4

عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

(Kana) a kan tafarki madaidaici



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 5

تَنزِيلَ ٱلۡعَزِيزِ ٱلرَّحِيمِ

(Alqur’ani) saukarwar (Allah) Mabuwayi Mai jin qai ne



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 6

لِتُنذِرَ قَوۡمٗا مَّآ أُنذِرَ ءَابَآؤُهُمۡ فَهُمۡ غَٰفِلُونَ

Don ka gargaxi mutanen da ba a yi wa iyayensu gargaxi ba[1], don haka kuwa suna cikin gafala


1- Su ne al’ummar Larabawa waxanda wani annabi bai zo musu ba.


Surah: Suratu Yasin

Ayah : 7

لَقَدۡ حَقَّ ٱلۡقَوۡلُ عَلَىٰٓ أَكۡثَرِهِمۡ فَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ

Haqiqa hukuncin Allah (na azaba) ya wajaba a kan mafiya yawansu, don ba za su yi imani ba



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 8

إِنَّا جَعَلۡنَا فِيٓ أَعۡنَٰقِهِمۡ أَغۡلَٰلٗا فَهِيَ إِلَى ٱلۡأَذۡقَانِ فَهُم مُّقۡمَحُونَ

Lalle Mun sanya ququmai a wuyoyinsu har zuwa havovinsu, don haka kawunansu a xage suke



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 9

وَجَعَلۡنَا مِنۢ بَيۡنِ أَيۡدِيهِمۡ سَدّٗا وَمِنۡ خَلۡفِهِمۡ سَدّٗا فَأَغۡشَيۡنَٰهُمۡ فَهُمۡ لَا يُبۡصِرُونَ

Muka kuma sanya wani shamaki a gabansu da kuma shamaki a bayansu, sai Muka lulluve musu (idanuwa), don haka ba sa gani



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 10

وَسَوَآءٌ عَلَيۡهِمۡ ءَأَنذَرۡتَهُمۡ أَمۡ لَمۡ تُنذِرۡهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ

Kuma duk xaya ne a wurinsu ko ka yi musu gargaxi ko ba ka yi musu gargaxi ba, ba za su yi imani ba



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 11

إِنَّمَا تُنذِرُ مَنِ ٱتَّبَعَ ٱلذِّكۡرَ وَخَشِيَ ٱلرَّحۡمَٰنَ بِٱلۡغَيۡبِۖ فَبَشِّرۡهُ بِمَغۡفِرَةٖ وَأَجۡرٖ كَرِيمٍ

Kana yin gargaxi ne kawai ga wanda ya bi umarnin Alqur’ani, ya kuma ji tsoron Allah ba tare da ya gan Shi ba; sai ka yi masa albishir da samun gafara da lada na karamci



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 12

إِنَّا نَحۡنُ نُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰ وَنَكۡتُبُ مَا قَدَّمُواْ وَءَاثَٰرَهُمۡۚ وَكُلَّ شَيۡءٍ أَحۡصَيۡنَٰهُ فِيٓ إِمَامٖ مُّبِينٖ

Lalle Mu ne za Mu raya matattu, Muke kuma rubuta irin abubuwan da suka gabatar (a rayuwarsu) da kuma abin da suka bari a bayansu (bayan mutuwa). Kowane abu kuma Mun qididdige shi a cikin Lauhul-Mahafuzu



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 13

وَٱضۡرِبۡ لَهُم مَّثَلًا أَصۡحَٰبَ ٱلۡقَرۡيَةِ إِذۡ جَآءَهَا ٱلۡمُرۡسَلُونَ

Kuma ka ba su misali da mutanen wata alqarya lokacin da manzannin suka zo mata



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 14

إِذۡ أَرۡسَلۡنَآ إِلَيۡهِمُ ٱثۡنَيۡنِ فَكَذَّبُوهُمَا فَعَزَّزۡنَا بِثَالِثٖ فَقَالُوٓاْ إِنَّآ إِلَيۡكُم مُّرۡسَلُونَ

A yayin da Muka aika musu (manzanni) biyu sai suka qaryata su, sannan Muka qarfafe su da na uku, sai suka ce: “Lalle mu manzanni ne zuwa gare ku.”