وَعُرِضُواْ عَلَىٰ رَبِّكَ صَفّٗا لَّقَدۡ جِئۡتُمُونَا كَمَا خَلَقۡنَٰكُمۡ أَوَّلَ مَرَّةِۭۚ بَلۡ زَعَمۡتُمۡ أَلَّن نَّجۡعَلَ لَكُم مَّوۡعِدٗا
Aka kuma kawo su a gaban Ubangijinka sahu-sahu (a ce da su): “Haqiqa kun zo mana kamar yadda tun farko Muka halicce ku. Ba ma haka ba, kun riya cewa ba za Mu sanya muku wani wa’adi ba.”
وَوُضِعَ ٱلۡكِتَٰبُ فَتَرَى ٱلۡمُجۡرِمِينَ مُشۡفِقِينَ مِمَّا فِيهِ وَيَقُولُونَ يَٰوَيۡلَتَنَا مَالِ هَٰذَا ٱلۡكِتَٰبِ لَا يُغَادِرُ صَغِيرَةٗ وَلَا كَبِيرَةً إِلَّآ أَحۡصَىٰهَاۚ وَوَجَدُواْ مَا عَمِلُواْ حَاضِرٗاۗ وَلَا يَظۡلِمُ رَبُّكَ أَحَدٗا
Aka kuma ajiye littafin (ayyukansu), sannan sai ka ga masu laifi suna cike da tsoron abin da yake cikinsa, suna kuma cewa: “Kaiconmu, me ya sami wannan littafin, ba ya barin (aiki) qarami balle babba sai ya qididdige su. Suka kuma sami (duk) abubuwan da suka aikata an zo da su. Ubangijinka kuwa ba zai zalunci kowa ba
وَإِذۡ قُلۡنَا لِلۡمَلَـٰٓئِكَةِ ٱسۡجُدُواْ لِأٓدَمَ فَسَجَدُوٓاْ إِلَّآ إِبۡلِيسَ كَانَ مِنَ ٱلۡجِنِّ فَفَسَقَ عَنۡ أَمۡرِ رَبِّهِۦٓۗ أَفَتَتَّخِذُونَهُۥ وَذُرِّيَّتَهُۥٓ أَوۡلِيَآءَ مِن دُونِي وَهُمۡ لَكُمۡ عَدُوُّۢۚ بِئۡسَ لِلظَّـٰلِمِينَ بَدَلٗا
Kuma ka tuna lokacin da Muka ce da mala’iku: “Ku yi sujjada ga Adamu”, sai suka yi sujjadar in ban da Iblis, ya kasance kuwa daga cikin aljannu, sai ya sava wa umarnin Ubangijinsa. Yanzu kwa riqe shi shi da zurriyarsa masoya ba Ni ba, alhali kuwa su maqiyanku ne? Wannan canji na azzalumai ya munana
۞مَّآ أَشۡهَدتُّهُمۡ خَلۡقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلَا خَلۡقَ أَنفُسِهِمۡ وَمَا كُنتُ مُتَّخِذَ ٱلۡمُضِلِّينَ عَضُدٗا
Ban halarto da su ba lokacin halittar sammai da qasa, ko ma halittar kawunansu, ban kuma kasance Mai riqon masu vatarwa mataimaka ba
وَيَوۡمَ يَقُولُ نَادُواْ شُرَكَآءِيَ ٱلَّذِينَ زَعَمۡتُمۡ فَدَعَوۡهُمۡ فَلَمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَهُمۡ وَجَعَلۡنَا بَيۡنَهُم مَّوۡبِقٗا
Kuma (ka tuna) ranar da (Allah) zai ce (da kafirai): “Ku kirawo abokan tarayyar nawa waxanda kuka riya (cewa su ne iyayen gijinku)”, to sai suka kirawo su, sai ba su amsa musu ba, Muka kuma sanya mahallaka a tsakaninsu
وَرَءَا ٱلۡمُجۡرِمُونَ ٱلنَّارَ فَظَنُّوٓاْ أَنَّهُم مُّوَاقِعُوهَا وَلَمۡ يَجِدُواْ عَنۡهَا مَصۡرِفٗا
Masu laifi kuma suka ga wuta sai suka tabbatar da cewa lalle za su shige ta ba kuwa za su sami wata makauta ba daga gare ta
وَلَقَدۡ صَرَّفۡنَا فِي هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ لِلنَّاسِ مِن كُلِّ مَثَلٖۚ وَكَانَ ٱلۡإِنسَٰنُ أَكۡثَرَ شَيۡءٖ جَدَلٗا
Kuma haqiqa Mun sassarafa kowane irin misali ga mutane a cikin wannan Alqur’anin. Mutum kuwa ya kasance wanda ya fi komai yawan musu
وَمَا مَنَعَ ٱلنَّاسَ أَن يُؤۡمِنُوٓاْ إِذۡ جَآءَهُمُ ٱلۡهُدَىٰ وَيَسۡتَغۡفِرُواْ رَبَّهُمۡ إِلَّآ أَن تَأۡتِيَهُمۡ سُنَّةُ ٱلۡأَوَّلِينَ أَوۡ يَأۡتِيَهُمُ ٱلۡعَذَابُ قُبُلٗا
Ba kuwa abin da ya hana mutane su yi imani lokacin da shiriya ta zo musu, su kuma nemi gafarar Ubangijinsu har sai irin abin da ya zo wa mutanen farko ya zo musu, ko kuwa azaba ta zo musu gaba-da-gaba
وَمَا نُرۡسِلُ ٱلۡمُرۡسَلِينَ إِلَّا مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَۚ وَيُجَٰدِلُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِٱلۡبَٰطِلِ لِيُدۡحِضُواْ بِهِ ٱلۡحَقَّۖ وَٱتَّخَذُوٓاْ ءَايَٰتِي وَمَآ أُنذِرُواْ هُزُوٗا
Ba Mu kuma aiko da manzanni ba sai don su zama masu albishir mai gargaxi. Su kuma waxanda suka kafirce sai su dinga jayayya da qarya don su kawar da gaskiya da ita; suka kuma riqi ayoyina da kuma abin da aka yi musu gargaxi da shi a matsayin abin izgili
وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن ذُكِّرَ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِۦ فَأَعۡرَضَ عَنۡهَا وَنَسِيَ مَا قَدَّمَتۡ يَدَاهُۚ إِنَّا جَعَلۡنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ أَكِنَّةً أَن يَفۡقَهُوهُ وَفِيٓ ءَاذَانِهِمۡ وَقۡرٗاۖ وَإِن تَدۡعُهُمۡ إِلَى ٱلۡهُدَىٰ فَلَن يَهۡتَدُوٓاْ إِذًا أَبَدٗا
Wane ne ya fi zalunci fiye da wanda aka yi masa gargaxi da ayoyin Ubangijinsa sannan ya bijire musu, ya kuma manta abin da hannayensa suka gabatar (na mugun aiki). Lalle Mun sanya rufi a zukatansu don kada su fahimce shi (Alqur’ani), a cikin kunnuwansu kuma (Muka sanya) wani nauyi. Idan kuwa ka kirawo su zuwa ga shiriya to ba za su yi imani ba har abada
وَرَبُّكَ ٱلۡغَفُورُ ذُو ٱلرَّحۡمَةِۖ لَوۡ يُؤَاخِذُهُم بِمَا كَسَبُواْ لَعَجَّلَ لَهُمُ ٱلۡعَذَابَۚ بَل لَّهُم مَّوۡعِدٞ لَّن يَجِدُواْ مِن دُونِهِۦ مَوۡئِلٗا
Ubangijinka kuwa Mai yawan gafara ne Ma’abocin rahama; da Yana kama su da abin da suka aikata, to da Ya gaggauta musu azaba. A’a, (ba Ya yin haka), sai dai suna da qayyadajjen lokaci wanda ba za su sami wata makauta ba daga gare shi
وَتِلۡكَ ٱلۡقُرَىٰٓ أَهۡلَكۡنَٰهُمۡ لَمَّا ظَلَمُواْ وَجَعَلۡنَا لِمَهۡلِكِهِم مَّوۡعِدٗا
Kuma waxancan alqaryu Mun hallakar da su yayin da suka yi zalunci, Muka kuma sanya qayyadajjen lokaci na hallakar da su
وَإِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِفَتَىٰهُ لَآ أَبۡرَحُ حَتَّىٰٓ أَبۡلُغَ مَجۡمَعَ ٱلۡبَحۡرَيۡنِ أَوۡ أَمۡضِيَ حُقُبٗا
Kuma (ka tuna) lokacin da Musa ya ce da yaronsa: “Ba zan dakata da (tafiyata) ba har sai na kai mahaxar kogunan nan biyu, ko kuwa in zarce har tsawon shekaru[1].”
1- Daga nan har zuwa qarshen aya ta 82 Allah () ya ba da labarin tafiyar Annabi Musa () neman ilimi wajen Annabi Khadir (). Yaronsa shi ne Annabi Yusha’u ().
فَلَمَّا بَلَغَا مَجۡمَعَ بَيۡنِهِمَا نَسِيَا حُوتَهُمَا فَٱتَّخَذَ سَبِيلَهُۥ فِي ٱلۡبَحۡرِ سَرَبٗا
To lokacin da suka isa mahaxar tasu (watau kogunan) sai suka manta da kifinsu wanda ya kama hanyarsa a cikin kogi kamar xakin qarqashin qasa
فَلَمَّا جَاوَزَا قَالَ لِفَتَىٰهُ ءَاتِنَا غَدَآءَنَا لَقَدۡ لَقِينَا مِن سَفَرِنَا هَٰذَا نَصَبٗا
To lokacin da suka wuce (wannan wuri) sai (Musa) ya ce da yaronsa: “Kawo mana abincinmu, haqiqa mun haxu da wahala cikin wannan tafiya tamu.”
قَالَ أَرَءَيۡتَ إِذۡ أَوَيۡنَآ إِلَى ٱلصَّخۡرَةِ فَإِنِّي نَسِيتُ ٱلۡحُوتَ وَمَآ أَنسَىٰنِيهُ إِلَّا ٱلشَّيۡطَٰنُ أَنۡ أَذۡكُرَهُۥۚ وَٱتَّخَذَ سَبِيلَهُۥ فِي ٱلۡبَحۡرِ عَجَبٗا
Sai (yaron) ya ce: “Ba ka gani ba lokacin da muka fake a daidai dutsen nan ai sai na manta da kifin, ba kuwa wani ne ya mantar da ni shi ba sai Shaixan, ya hana ni in tuna. Sai kuma ya kama hanyarsa cikin kogi, abin mamaki!”
قَالَ ذَٰلِكَ مَا كُنَّا نَبۡغِۚ فَٱرۡتَدَّا عَلَىٰٓ ءَاثَارِهِمَا قَصَصٗا
(Musa) ya ce: “Wannan da ma shi ne abin da muke nema”, Sai suka koma da baya suna bin sawunsu (ta inda suka fito)
فَوَجَدَا عَبۡدٗا مِّنۡ عِبَادِنَآ ءَاتَيۡنَٰهُ رَحۡمَةٗ مِّنۡ عِندِنَا وَعَلَّمۡنَٰهُ مِن لَّدُنَّا عِلۡمٗا
To sai suka sami wani bawa daga bayinmu wanda Muka bai wa rahama daga gare Mu, kuma Muka koyar da shi wani ilimi daga wajenmu
قَالَ لَهُۥ مُوسَىٰ هَلۡ أَتَّبِعُكَ عَلَىٰٓ أَن تُعَلِّمَنِ مِمَّا عُلِّمۡتَ رُشۡدٗا
Musa ya ce da shi: “Shin na iya bin ka don ka koyar da ni (wani abu) daga abin da aka koyar da kai na shiriya?”
قَالَ إِنَّكَ لَن تَسۡتَطِيعَ مَعِيَ صَبۡرٗا
Ya ce: “Lalle ba za ka iya haquri da ni ba
وَكَيۡفَ تَصۡبِرُ عَلَىٰ مَا لَمۡ تُحِطۡ بِهِۦ خُبۡرٗا
“Qaqa kuwa za ka yi haquri kan abin da ba ka kewaye da saninsa ba?”
قَالَ سَتَجِدُنِيٓ إِن شَآءَ ٱللَّهُ صَابِرٗا وَلَآ أَعۡصِي لَكَ أَمۡرٗا
(Musa) ya ce: “Za ka same ni mai haquri in sha Allahu, ba kuma zan sava wa umarninka ba.”
قَالَ فَإِنِ ٱتَّبَعۡتَنِي فَلَا تَسۡـَٔلۡنِي عَن شَيۡءٍ حَتَّىٰٓ أُحۡدِثَ لَكَ مِنۡهُ ذِكۡرٗا
Ya ce, “To idan ka bi ni kada ka tambaye ni game da kowane abu har sai na ba ka labari game da shi.”
فَٱنطَلَقَا حَتَّىٰٓ إِذَا رَكِبَا فِي ٱلسَّفِينَةِ خَرَقَهَاۖ قَالَ أَخَرَقۡتَهَا لِتُغۡرِقَ أَهۡلَهَا لَقَدۡ جِئۡتَ شَيۡـًٔا إِمۡرٗا
Sai suka tafi, har lokacin da suka shiga cikin jirgin ruwa, to sai ya huda shi; sai (Musa) ya ce: “Yanzu ka huda shi ne don ka nutsar da waxanda suke cikinsa? Haqiqa ka zo da babban abu.”
قَالَ أَلَمۡ أَقُلۡ إِنَّكَ لَن تَسۡتَطِيعَ مَعِيَ صَبۡرٗا
Ya ce: “Ban faxa maka ba cewa kai ba za ka iya haquri da ni ba?”
قَالَ لَا تُؤَاخِذۡنِي بِمَا نَسِيتُ وَلَا تُرۡهِقۡنِي مِنۡ أَمۡرِي عُسۡرٗا
(Musa) ya ce: “Kada ka kama ni da abin da na manta, kada kuma ka xora mini abu mai wahala game da al’amarina.”
فَٱنطَلَقَا حَتَّىٰٓ إِذَا لَقِيَا غُلَٰمٗا فَقَتَلَهُۥ قَالَ أَقَتَلۡتَ نَفۡسٗا زَكِيَّةَۢ بِغَيۡرِ نَفۡسٖ لَّقَدۡ جِئۡتَ شَيۡـٔٗا نُّكۡرٗا
Sai suka ci gaba da tafiya har dai suka gamu da wani yaro, to sai ya kashe shi, (Musa) ya ce: “Yanzu ka kashe rai tsarkakakke ba tare da (ya kashe) wani rai ba? Haqiqa ka zo da wani abu mummuna!”