Surah: Suratu Hud

Ayah : 66

فَلَمَّا جَآءَ أَمۡرُنَا نَجَّيۡنَا صَٰلِحٗا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ بِرَحۡمَةٖ مِّنَّا وَمِنۡ خِزۡيِ يَوۡمِئِذٍۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ ٱلۡقَوِيُّ ٱلۡعَزِيزُ

To lokacin da umarninmu ya zo sai Muka tserar da Salihu shi da waxanda suka yi imani tare da shi saboda wata rahama daga gare mu, kuma (Muka tserar da su) daga kunyatar wannan rana. Lalle Ubangijinka Shi ne Mai qarfi Mabuwayi



Surah: Suratu Hud

Ayah : 67

وَأَخَذَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ ٱلصَّيۡحَةُ فَأَصۡبَحُواْ فِي دِيَٰرِهِمۡ جَٰثِمِينَ

Kuma tsawa ta kama waxanda suka yi zalunci, sai suka wayi gari cikin gidajensu a duddurqushe (babu rai)



Surah: Suratu Hud

Ayah : 68

كَأَن لَّمۡ يَغۡنَوۡاْ فِيهَآۗ أَلَآ إِنَّ ثَمُودَاْ كَفَرُواْ رَبَّهُمۡۗ أَلَا بُعۡدٗا لِّثَمُودَ

Kamar daxai ba su tava zama a cikinsu ba (gidajen). Ku saurara! Lalle Samudawa kam sun kafirce wa Ubangijinsu. Ku saurara! Halaka ta tabbata ga Samudawa



Surah: Suratu Hud

Ayah : 69

وَلَقَدۡ جَآءَتۡ رُسُلُنَآ إِبۡرَٰهِيمَ بِٱلۡبُشۡرَىٰ قَالُواْ سَلَٰمٗاۖ قَالَ سَلَٰمٞۖ فَمَا لَبِثَ أَن جَآءَ بِعِجۡلٍ حَنِيذٖ

Haqiqa kuma mazanninmu sun zo wa Ibrahimu da albishir, suka ce: “Aminci (a gare ku)”, ya ce: “Aminci (a gare ku kuma).” To bai zauna ba sai da ya kawo musu soyayyen xan maraqi



Surah: Suratu Hud

Ayah : 70

فَلَمَّا رَءَآ أَيۡدِيَهُمۡ لَا تَصِلُ إِلَيۡهِ نَكِرَهُمۡ وَأَوۡجَسَ مِنۡهُمۡ خِيفَةٗۚ قَالُواْ لَا تَخَفۡ إِنَّآ أُرۡسِلۡنَآ إِلَىٰ قَوۡمِ لُوطٖ

To lokacin da ya ga hannayensu ba sa isa gare shi (soyayyen xan maraqin), sai ya shiga yin xari-xari da su[1], kuma ya voye jin tsoronsu a zuciyarsa, suka ce: “Kar ka tsorata; mu an aiko mu ne zuwa ga mutanen Luxu.”


1- Idan baqo ya ci abincin da aka kawo masa wannan yakan sanya nutsuwa a zukatan masu gida da yarda da shi.


Surah: Suratu Hud

Ayah : 71

وَٱمۡرَأَتُهُۥ قَآئِمَةٞ فَضَحِكَتۡ فَبَشَّرۡنَٰهَا بِإِسۡحَٰقَ وَمِن وَرَآءِ إِسۡحَٰقَ يَعۡقُوبَ

Matarsa kuwa tana tsaye sai ta yi dariya, sai Muka yi mata albishir da Is’haqa, bayan kuma Is’haqa (sai) Yakubu



Surah: Suratu Hud

Ayah : 72

قَالَتۡ يَٰوَيۡلَتَىٰٓ ءَأَلِدُ وَأَنَا۠ عَجُوزٞ وَهَٰذَا بَعۡلِي شَيۡخًاۖ إِنَّ هَٰذَا لَشَيۡءٌ عَجِيبٞ

Ta ce: “Kaicona! Yanzu zan iya haihuwa, ga ni tsohuwa kuma ga mijina nan ma tsoho? Lalle wannan abin mamaki ne!”



Surah: Suratu Hud

Ayah : 73

قَالُوٓاْ أَتَعۡجَبِينَ مِنۡ أَمۡرِ ٱللَّهِۖ رَحۡمَتُ ٱللَّهِ وَبَرَكَٰتُهُۥ عَلَيۡكُمۡ أَهۡلَ ٱلۡبَيۡتِۚ إِنَّهُۥ حَمِيدٞ مَّجِيدٞ

Suka ce: “Yanzu kya riqa mamaki game da al’amarin Allah? Rahamar Allah da albarkarsa su tabbata a gare ku mutanen wannan gidan. Lalle shi (Allah) Sha-yabo ne Mai girma.”



Surah: Suratu Hud

Ayah : 74

فَلَمَّا ذَهَبَ عَنۡ إِبۡرَٰهِيمَ ٱلرَّوۡعُ وَجَآءَتۡهُ ٱلۡبُشۡرَىٰ يُجَٰدِلُنَا فِي قَوۡمِ لُوطٍ

To lokacin da tsoro ya rabu da Ibrahimu, kuma albishir ya zo masa, (sai ya zama) yana muhawara da Mu[1] game da mutanen Luxu


1- Watau yana muhawara da mala’ikun Allah.


Surah: Suratu Hud

Ayah : 75

إِنَّ إِبۡرَٰهِيمَ لَحَلِيمٌ أَوَّـٰهٞ مُّنِيبٞ

Lalle Ibrahimu tabbas mai haquri ne mai yawan ambato Allah mai yawan komawa gare Shi



Surah: Suratu Hud

Ayah : 76

يَـٰٓإِبۡرَٰهِيمُ أَعۡرِضۡ عَنۡ هَٰذَآۖ إِنَّهُۥ قَدۡ جَآءَ أَمۡرُ رَبِّكَۖ وَإِنَّهُمۡ ءَاتِيهِمۡ عَذَابٌ غَيۡرُ مَرۡدُودٖ

Ya kai Ibrahimu, ka kau da kai daga wannan. Lalle umarnin Ubangijinka ya zo; lalle kuwa azaba wadda ba mai kawar da ita za ta zo musu



Surah: Suratu Hud

Ayah : 77

وَلَمَّا جَآءَتۡ رُسُلُنَا لُوطٗا سِيٓءَ بِهِمۡ وَضَاقَ بِهِمۡ ذَرۡعٗا وَقَالَ هَٰذَا يَوۡمٌ عَصِيبٞ

Lokacin kuma da manzanninmu suka zo wa Luxu, sai aka vata masa rai saboda su, kuma zuciyarsa ta yi qunci saboda su[1], ya kuma ce: “Wannan rana ce mawuyaciya!”


1- Watau ya shiga damuwa domin ya san mutanensa ba za su qyale su ba.


Surah: Suratu Hud

Ayah : 78

وَجَآءَهُۥ قَوۡمُهُۥ يُهۡرَعُونَ إِلَيۡهِ وَمِن قَبۡلُ كَانُواْ يَعۡمَلُونَ ٱلسَّيِّـَٔاتِۚ قَالَ يَٰقَوۡمِ هَـٰٓؤُلَآءِ بَنَاتِي هُنَّ أَطۡهَرُ لَكُمۡۖ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَلَا تُخۡزُونِ فِي ضَيۡفِيٓۖ أَلَيۡسَ مِنكُمۡ رَجُلٞ رَّشِيدٞ

Mutanensa kuwa suka zo masa suna gaggawa, da ma ko can sun zamanto suna yin munanan ayyuka[1]. Ya ce: “Ya ku mutanena, ga ‘ya’yana nan mata, su suka fi tsarkaka a gare ku (ba maza ba), to ku kiyayi Allah, kada ku kunyata ni game da baqina. Yanzu a cikinku ba wani mutum mai hankali?”


1- Watau neman maza da yi musu fyaxe.


Surah: Suratu Hud

Ayah : 79

قَالُواْ لَقَدۡ عَلِمۡتَ مَا لَنَا فِي بَنَاتِكَ مِنۡ حَقّٖ وَإِنَّكَ لَتَعۡلَمُ مَا نُرِيدُ

Suka ce: “Haqiqa ka sani ba mu da wani haqqi (na sha’awa) ga ‘ya’yanka mata, lalle kuma tabbas ka san abin da muke nufi!”



Surah: Suratu Hud

Ayah : 80

قَالَ لَوۡ أَنَّ لِي بِكُمۡ قُوَّةً أَوۡ ءَاوِيٓ إِلَىٰ رُكۡنٖ شَدِيدٖ

Ya ce: “Ina ma ina da qarfi da zan hana ku, ko kuwa ina da wata qaqqarfar majingina (da zan dogara da ita)?”



Surah: Suratu Hud

Ayah : 81

قَالُواْ يَٰلُوطُ إِنَّا رُسُلُ رَبِّكَ لَن يَصِلُوٓاْ إِلَيۡكَۖ فَأَسۡرِ بِأَهۡلِكَ بِقِطۡعٖ مِّنَ ٱلَّيۡلِ وَلَا يَلۡتَفِتۡ مِنكُمۡ أَحَدٌ إِلَّا ٱمۡرَأَتَكَۖ إِنَّهُۥ مُصِيبُهَا مَآ أَصَابَهُمۡۚ إِنَّ مَوۡعِدَهُمُ ٱلصُّبۡحُۚ أَلَيۡسَ ٱلصُّبۡحُ بِقَرِيبٖ

(Baqin) suka ce: “Ya Luxu, lalle mu manzannin Ubangijinka ne; ba za su iya isowa gare ka ba; don haka sai ka tafi kai da iyalanka cikin wani yanki na dare, kada kuwa xaya daga cikinku ya waiwaya, sai matarka kawai. Lalle ita kam abin da ya same su zai same ta. Lalle lokacin da aka xebar musu asuba ne kawai; shin asuba ba kurkusa take ba?



Surah: Suratu Hud

Ayah : 82

فَلَمَّا جَآءَ أَمۡرُنَا جَعَلۡنَا عَٰلِيَهَا سَافِلَهَا وَأَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهَا حِجَارَةٗ مِّن سِجِّيلٖ مَّنضُودٖ

To lokacin da umarninmu ya zo sai Muka mai da samanta qasa (wato alqaryar), Muka kuma yi mata ruwan duwatsu irin na soyayyen yumvu wasu bayan wasu



Surah: Suratu Hud

Ayah : 83

مُّسَوَّمَةً عِندَ رَبِّكَۖ وَمَا هِيَ مِنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ بِبَعِيدٖ

Waxanda aka yi wa alama daga Ubangijinka. Ba kuwa nesa (dutsen) yake da azzalumai ba