Surah: Suratut Tauba

Ayah : 26

ثُمَّ أَنزَلَ ٱللَّهُ سَكِينَتَهُۥ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ وَعَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَأَنزَلَ جُنُودٗا لَّمۡ تَرَوۡهَا وَعَذَّبَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۚ وَذَٰلِكَ جَزَآءُ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Sannan Allah Ya sauqar wa da Manzonsa da kuma muminai nutsuwarsa, Ya kuma saukar da wasu rundunoni da ba kwa gani, Ya kuma azabtar da waxanda suka kafirta. Wannan kuwa shi ne sakamakon kafirai



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 27

ثُمَّ يَتُوبُ ٱللَّهُ مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ عَلَىٰ مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Sannan bayan wannan Allah zai karvi tuban wanda Ya ga dama. Allah kuwa Mai gafara ne, Mai rahama



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 28

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّمَا ٱلۡمُشۡرِكُونَ نَجَسٞ فَلَا يَقۡرَبُواْ ٱلۡمَسۡجِدَ ٱلۡحَرَامَ بَعۡدَ عَامِهِمۡ هَٰذَاۚ وَإِنۡ خِفۡتُمۡ عَيۡلَةٗ فَسَوۡفَ يُغۡنِيكُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦٓ إِن شَآءَۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, lalle mushrikai najasa ne kawai, saboda haka kada su kusanci Masallaci mai alfarma bayan wannan shekarar tasu. Idan kuma kuna tsoron talauci ne to Allah zai wadata ku daga falalarsa idan Ya ga dama. Lalle Allah Masani ne, Mai hikima



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 29

قَٰتِلُواْ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَلَا بِٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَلَا يُحَرِّمُونَ مَا حَرَّمَ ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥ وَلَا يَدِينُونَ دِينَ ٱلۡحَقِّ مِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ حَتَّىٰ يُعۡطُواْ ٱلۡجِزۡيَةَ عَن يَدٖ وَهُمۡ صَٰغِرُونَ

Ku yaqi waxanda ba sa yin imani da Allah da ranar lahira, ba kuma sa haramta abin da Allah da Manzonsa suka haramta, kuma ba sa yin addini na gaskiya, daga waxanda aka bai wa littafi har sai (sun yarda) za su ba da jizya[1] da hannunsu a qasqance


1- Jizya, ita ce dukiyar da ake karva daga hannun Yahudu da Nasara waxanda ake zaune da su lafiya a qasar Musulmi, domin xauke mu shiga rundunar Musulmi, sannan a ba su kariya daga abokan gaba. Ba a karvar zakka daga hannunsu, wannan haqqi ne da ya shafi Musulmi kaxai.


Surah: Suratut Tauba

Ayah : 30

وَقَالَتِ ٱلۡيَهُودُ عُزَيۡرٌ ٱبۡنُ ٱللَّهِ وَقَالَتِ ٱلنَّصَٰرَى ٱلۡمَسِيحُ ٱبۡنُ ٱللَّهِۖ ذَٰلِكَ قَوۡلُهُم بِأَفۡوَٰهِهِمۡۖ يُضَٰهِـُٔونَ قَوۡلَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن قَبۡلُۚ قَٰتَلَهُمُ ٱللَّهُۖ أَنَّىٰ يُؤۡفَكُونَ

Yahudawa sun ce: “Uzairu xan Allah ne.” Nasara kuma suka ce: “Almasihu xan Allah ne.” Wannan faxarsu ce kawai da bakunansu; suna kwaikwayon faxar kafiran da suka gabace su ne. Allah Ya tsine musu. Ta qaqa ake kautar da su daga gaskiya?



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 31

ٱتَّخَذُوٓاْ أَحۡبَارَهُمۡ وَرُهۡبَٰنَهُمۡ أَرۡبَابٗا مِّن دُونِ ٱللَّهِ وَٱلۡمَسِيحَ ٱبۡنَ مَرۡيَمَ وَمَآ أُمِرُوٓاْ إِلَّا لِيَعۡبُدُوٓاْ إِلَٰهٗا وَٰحِدٗاۖ لَّآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ سُبۡحَٰنَهُۥ عَمَّا يُشۡرِكُونَ

Sun xauki malamansu da masu ibadarsu da kuma Almasihu xan Maryamu iyayen giji maimakon Allah[1], alhali kuwa ba abin da aka umarce su sai su bauta wa Abin bauta Xaya, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Ya tsarkaka daga abin da suke tara Shi da shi


1- Watau suna yi wa malamansu da masu bauta a cikinsu makauniyar biyayya, suna haramta musu halal, su kuma halatta musu haram. Nasara sun xauki Annabi Isa () abin bauta ba Allah ba.


Surah: Suratut Tauba

Ayah : 32

يُرِيدُونَ أَن يُطۡفِـُٔواْ نُورَ ٱللَّهِ بِأَفۡوَٰهِهِمۡ وَيَأۡبَى ٱللَّهُ إِلَّآ أَن يُتِمَّ نُورَهُۥ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡكَٰفِرُونَ

Suna nufi ne su dushashe hasken Allah da bakunansu, Allah kuwa ba zai qyale ba har sai Ya cika haskensa ko da kuwa kafirai sun qi



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 33

هُوَ ٱلَّذِيٓ أَرۡسَلَ رَسُولَهُۥ بِٱلۡهُدَىٰ وَدِينِ ٱلۡحَقِّ لِيُظۡهِرَهُۥ عَلَى ٱلدِّينِ كُلِّهِۦ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡمُشۡرِكُونَ

Shi ne wanda Ya aiko Manzonsa da shiriya da kuma addini na gaskiya don Ya xora shi a kan dukkanin addinai, ko da kuwa mushrikai sun qi