وَأَبۡصِرۡهُمۡ فَسَوۡفَ يُبۡصِرُونَ
Kuma ka ganar da su (sakamakon kafirci), sannan ba da daxewa ba za su gani
أَفَبِعَذَابِنَا يَسۡتَعۡجِلُونَ
Yanzu azabarmu suke neman gaggautowa?
فَإِذَا نَزَلَ بِسَاحَتِهِمۡ فَسَآءَ صَبَاحُ ٱلۡمُنذَرِينَ
To lokacin da (azabar) ta sauka a sararin gidajensu, ai asubar waxanda aka yi wa gargaxi ta munana
وَتَوَلَّ عَنۡهُمۡ حَتَّىٰ حِينٖ
Kuma ka rabu da su har zuwa wani lokaci
وَأَبۡصِرۡ فَسَوۡفَ يُبۡصِرُونَ
Ka kuma ganar (da su sakamakon kafirci), ba da daxewa ba za su gani
سُبۡحَٰنَ رَبِّكَ رَبِّ ٱلۡعِزَّةِ عَمَّا يَصِفُونَ
Ubangijinka wanda yake Ubangiji ne Mabuwayi Ya tsarkaka daga abin da suke sifanta (Shi da shi)
وَسَلَٰمٌ عَلَى ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Aminci kuma ya tabbata bisa ga manzanni
وَٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai
صٓۚ وَٱلۡقُرۡءَانِ ذِي ٱلذِّكۡرِ
SAD[1]. “Na rantse da Alqur’ani ma’abocin xaukaka
1- Duba Suratul Baqara aya ta 1, hashiya ta 8.
بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فِي عِزَّةٖ وَشِقَاقٖ
Sai dai waxanda suka kafirta suna cikin girman kai ne da jayayya
كَمۡ أَهۡلَكۡنَا مِن قَبۡلِهِم مِّن قَرۡنٖ فَنَادَواْ وَّلَاتَ حِينَ مَنَاصٖ
Al’ummu nawa Muka hallaka gabaninsu, sai suka yi ta kururuwar neman agaji, alhali kuwa lokacin ba na neman tsira ba ne
وَعَجِبُوٓاْ أَن جَآءَهُم مُّنذِرٞ مِّنۡهُمۡۖ وَقَالَ ٱلۡكَٰفِرُونَ هَٰذَا سَٰحِرٞ كَذَّابٌ
Suka kuma yi mamaki don mai gargaxi ya zo musu daga cikinsu; kuma kafirai suka ce: “Wannan mai sihiri ne babban maqaryaci
أَجَعَلَ ٱلۡأٓلِهَةَ إِلَٰهٗا وَٰحِدًاۖ إِنَّ هَٰذَا لَشَيۡءٌ عُجَابٞ
“Yanzu yaya zai mayar da alloli Allah guda xaya? Lalle wannan abu ne mai ban mamaki.”
وَٱنطَلَقَ ٱلۡمَلَأُ مِنۡهُمۡ أَنِ ٱمۡشُواْ وَٱصۡبِرُواْ عَلَىٰٓ ءَالِهَتِكُمۡۖ إِنَّ هَٰذَا لَشَيۡءٞ يُرَادُ
Manyansu kuma suka tafi (suna cewa): “Ku yi tafiyarku, kuma ku yi haquri a kan (bautar) allolinku; lalle wannan wani shiryayyen abu ne ake nufi
مَا سَمِعۡنَا بِهَٰذَا فِي ٱلۡمِلَّةِ ٱلۡأٓخِرَةِ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا ٱخۡتِلَٰقٌ
“Ba mu tava jin irin wannan ba a addinin da ya wuce[1], wannan ba komai ba ne sai qage
1- Watau addinin Annabi Isa ().
أَءُنزِلَ عَلَيۡهِ ٱلذِّكۡرُ مِنۢ بَيۡنِنَاۚ بَلۡ هُمۡ فِي شَكّٖ مِّن ذِكۡرِيۚ بَل لَّمَّا يَذُوقُواْ عَذَابِ
“Yanzu a saukar masa da Alqur’ani a tsakaninmu?” Ba haka ba ne, su dai suna kokwanto ne game da tunatarwata; bar su, ai har yanzu ba su xanxani azabata ba ne
أَمۡ عِندَهُمۡ خَزَآئِنُ رَحۡمَةِ رَبِّكَ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡوَهَّابِ
Ko kuwa a wurinsu ne taskokin rahamar Ubangijinka Mabuwayi Mai baiwa suke?
أَمۡ لَهُم مُّلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَاۖ فَلۡيَرۡتَقُواْ فِي ٱلۡأَسۡبَٰبِ
Ko kuma mulkin sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu nasu ne? To sai su kama hanyoyin zuwa sama (domin su aikata abin da suke so)
جُندٞ مَّا هُنَالِكَ مَهۡزُومٞ مِّنَ ٱلۡأَحۡزَابِ
(Waxannan) wata runduna ce da za a murqushe ta, kamar sauran al’ummun da suka gabata (waxanda suka qaryata manzanninsu)
كَذَّبَتۡ قَبۡلَهُمۡ قَوۡمُ نُوحٖ وَعَادٞ وَفِرۡعَوۡنُ ذُو ٱلۡأَوۡتَادِ
Mutanen Nuhu sun qaryata kafin su (mutan Makka) da Adawa da Fir’auna mai turaku
وَثَمُودُ وَقَوۡمُ لُوطٖ وَأَصۡحَٰبُ لۡـَٔيۡكَةِۚ أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلۡأَحۡزَابُ
Da kuma Samudawa da mutanen Luxu da mutanen Sarqaqiya[1]. Waxannan su ne al’ummun
1- Su ne mutanen Annabi Shu’aibu ().
إِن كُلٌّ إِلَّا كَذَّبَ ٱلرُّسُلَ فَحَقَّ عِقَابِ
Babu xaya daga cikinsu wanda bai qaryata manzanni ba, sai uqubata ta wajaba (a kansu)
وَمَا يَنظُرُ هَـٰٓؤُلَآءِ إِلَّا صَيۡحَةٗ وَٰحِدَةٗ مَّا لَهَا مِن فَوَاقٖ
Kuma ba abin da waxannan suke sauraro sai busa guda xaya wadda ba ta da makawa
وَقَالُواْ رَبَّنَا عَجِّل لَّنَا قِطَّنَا قَبۡلَ يَوۡمِ ٱلۡحِسَابِ
Suka kuma ce: “Ya Ubangijinmu, Ka gaggauto mana rabonmu (na azaba) tun kafin ranar hisabi!”
ٱصۡبِرۡ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَٱذۡكُرۡ عَبۡدَنَا دَاوُۥدَ ذَا ٱلۡأَيۡدِۖ إِنَّهُۥٓ أَوَّابٌ
(Sai Allah Ya ce): “Ka yi haquri a kan abin da suke faxa, ka kuma tuna bawanmu Dawuda ma’abocin qarfi; lalle shi ya kasance mai yawan komawa ne (ga Allah)
إِنَّا سَخَّرۡنَا ٱلۡجِبَالَ مَعَهُۥ يُسَبِّحۡنَ بِٱلۡعَشِيِّ وَٱلۡإِشۡرَاقِ
Lalle Mu Mun hore masa duwatsu suna yin tasbihi tare da shi a yamma da hantsi
وَٱلطَّيۡرَ مَحۡشُورَةٗۖ كُلّٞ لَّهُۥٓ أَوَّابٞ
Da kuma tsuntsaye a tattare; dukkaninsu suna biyayya a gare shi
وَشَدَدۡنَا مُلۡكَهُۥ وَءَاتَيۡنَٰهُ ٱلۡحِكۡمَةَ وَفَصۡلَ ٱلۡخِطَابِ
Kuma Muka qarfafa mulkinsa, Muka kuma ba shi hikima da bayyana hukunce-hukunce (tsakanin masu husuma)
۞وَهَلۡ أَتَىٰكَ نَبَؤُاْ ٱلۡخَصۡمِ إِذۡ تَسَوَّرُواْ ٱلۡمِحۡرَابَ
Shin labarin abokan husuma ya zo maka, yayin da suka haura wurin ibada?
إِذۡ دَخَلُواْ عَلَىٰ دَاوُۥدَ فَفَزِعَ مِنۡهُمۡۖ قَالُواْ لَا تَخَفۡۖ خَصۡمَانِ بَغَىٰ بَعۡضُنَا عَلَىٰ بَعۡضٖ فَٱحۡكُم بَيۡنَنَا بِٱلۡحَقِّ وَلَا تُشۡطِطۡ وَٱهۡدِنَآ إِلَىٰ سَوَآءِ ٱلصِّرَٰطِ
Yayin da suka shiga wurin Dawuda sai ya tsorata da su, suka ce: “Kada ka tsorata, (mu biyun nan) masu husuma ne, xayanmu ya zalunci xaya, sai ka yi hukunci a tsakaninmu da gaskiya, kada kuma ka yi zalunci, kuma ka shiryar da mu hanya madaidaiciya