Surah: Suratul Qasas

Ayah : 81

فَخَسَفۡنَا بِهِۦ وَبِدَارِهِ ٱلۡأَرۡضَ فَمَا كَانَ لَهُۥ مِن فِئَةٖ يَنصُرُونَهُۥ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلۡمُنتَصِرِينَ

Sannan muka kifar da shi (Qaruna) tare da gidansa cikin qasa, kuma ba shi da wata jama’a da za su taimake shi ba Allah ba, kuma bai kasance daga masu taimaka wa kawunansu ba



Surah: Suratul Qasas

Ayah : 82

وَأَصۡبَحَ ٱلَّذِينَ تَمَنَّوۡاْ مَكَانَهُۥ بِٱلۡأَمۡسِ يَقُولُونَ وَيۡكَأَنَّ ٱللَّهَ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦ وَيَقۡدِرُۖ لَوۡلَآ أَن مَّنَّ ٱللَّهُ عَلَيۡنَا لَخَسَفَ بِنَاۖ وَيۡكَأَنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلۡكَٰفِرُونَ

Kuma waxanda suka yi burin matsayinsa a jiya suka wayi gari suna cewa: “Wai, yau mun ga abin al’ajabi! Allah Yana yalwata arziki ga wanda Ya ga dama daga bayinsa, Yana kuma quntatawa ga wanda Ya ga dama; ba don Allah Ya ba mu sa’a ba da mu ma Ya kifar da mu. Wai, abin mamaki, lalle kafurai ba sa rabauta!”



Surah: Suratul Qasas

Ayah : 83

تِلۡكَ ٱلدَّارُ ٱلۡأٓخِرَةُ نَجۡعَلُهَا لِلَّذِينَ لَا يُرِيدُونَ عُلُوّٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا فَسَادٗاۚ وَٱلۡعَٰقِبَةُ لِلۡمُتَّقِينَ

Wancan gida na lahira Muna ba da shi ga waxanda ba sa nufin girman kai da varna a bayan qasa. Kyakkyawan qarshe kuma yana ga masu kiyaye dokokin Allah ne



Surah: Suratul Qasas

Ayah : 84

مَن جَآءَ بِٱلۡحَسَنَةِ فَلَهُۥ خَيۡرٞ مِّنۡهَاۖ وَمَن جَآءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَلَا يُجۡزَى ٱلَّذِينَ عَمِلُواْ ٱلسَّيِّـَٔاتِ إِلَّا مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Duk wanda ya zo da kyakkyawan aiki, to yana da (lada) fiye da aikinsa; wanda kuma ya zo da mummunan aiki, to ba za a saka wa waxanda suka aikata munanan ayyuka ba face daidai da abin da suka kasance suna aikatawa



Surah: Suratul Qasas

Ayah : 85

إِنَّ ٱلَّذِي فَرَضَ عَلَيۡكَ ٱلۡقُرۡءَانَ لَرَآدُّكَ إِلَىٰ مَعَادٖۚ قُل رَّبِّيٓ أَعۡلَمُ مَن جَآءَ بِٱلۡهُدَىٰ وَمَنۡ هُوَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ

Lalle Wanda Ya saukar maka da Alqur’ani tabbas zai mayar da kai zuwa makomarka[1]. Ka ce: “Ubangijina Shi Ya san wanda ya zo da shiriya da kuma wanda yake cikin vata mabayyani.”


1- Watau zai mayar da shi mahaifarsa garin Makka; ko kuma zai mayar da shi makomarsa ta qarshe watau Aljanna.


Surah: Suratul Qasas

Ayah : 86

وَمَا كُنتَ تَرۡجُوٓاْ أَن يُلۡقَىٰٓ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبُ إِلَّا رَحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَۖ فَلَا تَكُونَنَّ ظَهِيرٗا لِّلۡكَٰفِرِينَ

Kuma ba ka kasance kana fatan a saukar maka da littafi ba, sai dai (an yi haka ne) don rahama daga Ubangijinka; to don haka kada ka zamanto mai taimakon kafirai



Surah: Suratul Qasas

Ayah : 87

وَلَا يَصُدُّنَّكَ عَنۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ بَعۡدَ إِذۡ أُنزِلَتۡ إِلَيۡكَۖ وَٱدۡعُ إِلَىٰ رَبِّكَۖ وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

Kuma lallai kada su hana ka (isar da) ayoyin Allah bayan an riga an saukar maka da su; kuma ka yi kira zuwa ga Ubangijinka; kuma lallai kada ka zamanto daga mushrikai



Surah: Suratul Qasas

Ayah : 88

وَلَا تَدۡعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَۘ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ كُلُّ شَيۡءٍ هَالِكٌ إِلَّا وَجۡهَهُۥۚ لَهُ ٱلۡحُكۡمُ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Kuma kada ka bauta wa wani abin bauta daban tare da Allah. Babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Kowane abu mai halaka ne sai Fuskarsa kawai. Hukunci (duk) nasa ne, zuwa gare Shi kuma za a mayar da ku



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 1

الٓمٓ

ALIF LAM MIM[1]


1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.


Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 2

أَحَسِبَ ٱلنَّاسُ أَن يُتۡرَكُوٓاْ أَن يَقُولُوٓاْ ءَامَنَّا وَهُمۡ لَا يُفۡتَنُونَ

Yanzu mutane suna tsammanin za a qyale su ne saboda suna cewa: “Mun yi imani,” kuma ba za a fitine su ba?



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 3

وَلَقَدۡ فَتَنَّا ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۖ فَلَيَعۡلَمَنَّ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ صَدَقُواْ وَلَيَعۡلَمَنَّ ٱلۡكَٰذِبِينَ

Haqiqa kuwa Mun fitini waxanda suke gabaninsu; to tabbas kuwa Allah zai bayyana waxanda suka yi gaskiya, lalle kuma zai bayyana maqaryata



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 4

أَمۡ حَسِبَ ٱلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلسَّيِّـَٔاتِ أَن يَسۡبِقُونَاۚ سَآءَ مَا يَحۡكُمُونَ

Ko kuma waxanda suke aikata munanan ayyuka suna tsammanin za su gagare Mu ne? Abin da suke hukuntawa ya munana



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 5

مَن كَانَ يَرۡجُواْ لِقَآءَ ٱللَّهِ فَإِنَّ أَجَلَ ٱللَّهِ لَأٓتٖۚ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

Wanda ya zama yana fatan haxuwa da Allah, to lalle lokacin (haxuwa da) Allah tabbas mai zuwa ne. Kuma Shi ne Mai ji, Masani



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 6

وَمَن جَٰهَدَ فَإِنَّمَا يُجَٰهِدُ لِنَفۡسِهِۦٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَغَنِيٌّ عَنِ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Duk wanda kuwa ya yi jihadi, to yana jihadin ne don kansa. Lalle Allah tabbas Mawadaci ne daga talikai



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 7

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَنُكَفِّرَنَّ عَنۡهُمۡ سَيِّـَٔاتِهِمۡ وَلَنَجۡزِيَنَّهُمۡ أَحۡسَنَ ٱلَّذِي كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Waxanda kuma suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, tabbas za Mu kankare musu munanan ayyukansu, kuma tabbas za Mu saka musu da mafi kyan abin da suka kasance suna aikatawa



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 8

وَوَصَّيۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ بِوَٰلِدَيۡهِ حُسۡنٗاۖ وَإِن جَٰهَدَاكَ لِتُشۡرِكَ بِي مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٞ فَلَا تُطِعۡهُمَآۚ إِلَيَّ مَرۡجِعُكُمۡ فَأُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Kuma Mun yi wa mutum wasiyya da kyautata wa iyayensa; idan kuma suka yaqe ka kan ka yi shirka da Ni game da abin da ba ka da sani a kansa, to kada ka bi su. Wurina ne makomarku take kawai, sannan zan ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 9

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَنُدۡخِلَنَّهُمۡ فِي ٱلصَّـٰلِحِينَ

Waxanda kuma suka yi imani suka yi ayyuka nagari tabbas za Mu shigar da su cikin salihai



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 10

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَقُولُ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ فَإِذَآ أُوذِيَ فِي ٱللَّهِ جَعَلَ فِتۡنَةَ ٱلنَّاسِ كَعَذَابِ ٱللَّهِۖ وَلَئِن جَآءَ نَصۡرٞ مِّن رَّبِّكَ لَيَقُولُنَّ إِنَّا كُنَّا مَعَكُمۡۚ أَوَلَيۡسَ ٱللَّهُ بِأَعۡلَمَ بِمَا فِي صُدُورِ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Kuma cikin mutane akwai mai cewa: “Mun yi imani da Allah,” to idan aka cuce shi a kan hanyar Allah sai yakan xauki fitinar mutane kamar azabar Allah, lalle kuwa idan wata nasara ta zo daga Ubangijinka, tabbas zai riqa cewa: “Lalle mu mun kasance tare da ku.” Yanzu Allah ba Shi Ya fi kowa sanin abin da ke cikin zukatan talikai ba?



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 11

وَلَيَعۡلَمَنَّ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَلَيَعۡلَمَنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ

Tabbas kuma Allah zai bayyana waxanda suka yi imani, kuma tabbas zai bayyana munafukai



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 12

وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّبِعُواْ سَبِيلَنَا وَلۡنَحۡمِلۡ خَطَٰيَٰكُمۡ وَمَا هُم بِحَٰمِلِينَ مِنۡ خَطَٰيَٰهُم مِّن شَيۡءٍۖ إِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ

Kuma waxanda suka kafirta suka ce da waxanda suka yi imani: “Ku bi tafarkinmu, (mu) lalle za mu xauke muku laifuffukanku,” alhali kuwa su ba za su iya xauke wani abu na laifuffukansu ba; lalle su dai tabbas maqaryata ne



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 13

وَلَيَحۡمِلُنَّ أَثۡقَالَهُمۡ وَأَثۡقَالٗا مَّعَ أَثۡقَالِهِمۡۖ وَلَيُسۡـَٔلُنَّ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ عَمَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ

Tabbas kuma za su xauki zunubansu da kuma wasu zunuban tare da zunubansu[1]; kuma tabbas za a tambaye su a ranar alqiyama game da abin da suka kasance suna qirqira


1- Watau tare da zunuban waxanda suka yaudara suka vatar da su, ba kuma tare da an rage zunuban mabiyansu ba.


Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 14

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوۡمِهِۦ فَلَبِثَ فِيهِمۡ أَلۡفَ سَنَةٍ إِلَّا خَمۡسِينَ عَامٗا فَأَخَذَهُمُ ٱلطُّوفَانُ وَهُمۡ ظَٰلِمُونَ

Kuma haqiqa Mun aiko Nuhu zuwa ga mutanensa, sai ya zauna cikinsu shekara dubu ba hamsin, sai (ruwan) Xufana ya ci su, alhalin suna azzalumai



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 15

فَأَنجَيۡنَٰهُ وَأَصۡحَٰبَ ٱلسَّفِينَةِ وَجَعَلۡنَٰهَآ ءَايَةٗ لِّلۡعَٰلَمِينَ

Sai Muka tserar da shi tare da mutanen jirgin ruwa, Muka kuma sanya shi (jirgin) aya ga talikai



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 16

وَإِبۡرَٰهِيمَ إِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَٱتَّقُوهُۖ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

Kuma (ka tuna) Ibrahimu lokacin da ya ce da mutanensa: “Ku bauta wa Allah, kuma ku kiyaye dokokinsa, wannan shi ya fi muku alheri in kun kasance kun san (haka)



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 17

إِنَّمَا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَوۡثَٰنٗا وَتَخۡلُقُونَ إِفۡكًاۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَا يَمۡلِكُونَ لَكُمۡ رِزۡقٗا فَٱبۡتَغُواْ عِندَ ٱللَّهِ ٱلرِّزۡقَ وَٱعۡبُدُوهُ وَٱشۡكُرُواْ لَهُۥٓۖ إِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Lalle abin da kuke bauta wa ba Allah ba gumaka ne kawai, kuna kuma qirqirar qarya ne[1]. Lalle waxanda kuke bauta wa ba Allah ba, ba su mallaki wani arziki ba gare ku, sai ku nemi arziki a wurin Allah, kuma ku bauta masa, ku kuma gode masa; gare Shi ne kawai za a mayar da ku


1- Domin su ne suke sassaqa su da hannayensu suke kuma sanya musu sunaye sannan su bauta musu.


Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 18

وَإِن تُكَذِّبُواْ فَقَدۡ كَذَّبَ أُمَمٞ مِّن قَبۡلِكُمۡۖ وَمَا عَلَى ٱلرَّسُولِ إِلَّا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ

Idan kuma kuka qaryata, to haqiqa da ma wasu al’ummun da suke gabaninku sun qaryata; ba abin da yake kan Manzo sai isar da saqo mabayyani



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 19

أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ كَيۡفَ يُبۡدِئُ ٱللَّهُ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥٓۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ

Yanzu ba su ga yadda Allah Yake farar halitta ba, sannan Shi ne kuma zai mayar da ita? Lalle wannan mai sauqi ne a wurin Allah



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 20

قُلۡ سِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَٱنظُرُواْ كَيۡفَ بَدَأَ ٱلۡخَلۡقَۚ ثُمَّ ٱللَّهُ يُنشِئُ ٱلنَّشۡأَةَ ٱلۡأٓخِرَةَۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Ka ce: “Ku yi tafiya a bayan qasa sai ku duba ku ga yadda Allah Ya fari halittu. Sannan Allah ne zai sake samar da su samarwar qarshe. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 21

يُعَذِّبُ مَن يَشَآءُ وَيَرۡحَمُ مَن يَشَآءُۖ وَإِلَيۡهِ تُقۡلَبُونَ

“Yana azabtar da wanda Ya ga dama, Yana kuma jin qan wanda Ya ga dama; kuma wurinsa kawai za a mayar da ku



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 22

وَمَآ أَنتُم بِمُعۡجِزِينَ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا فِي ٱلسَّمَآءِۖ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ مِن وَلِيّٖ وَلَا نَصِيرٖ

“Kuma ku ba za ku gagara ba a qasa ko kuma a sama; kuma ba ku da wani majivinci ko mataimaki in ba Allah ba.”