۞وَهُوَ ٱلَّذِيٓ أَنشَأَ جَنَّـٰتٖ مَّعۡرُوشَٰتٖ وَغَيۡرَ مَعۡرُوشَٰتٖ وَٱلنَّخۡلَ وَٱلزَّرۡعَ مُخۡتَلِفًا أُكُلُهُۥ وَٱلزَّيۡتُونَ وَٱلرُّمَّانَ مُتَشَٰبِهٗا وَغَيۡرَ مُتَشَٰبِهٖۚ كُلُواْ مِن ثَمَرِهِۦٓ إِذَآ أَثۡمَرَ وَءَاتُواْ حَقَّهُۥ يَوۡمَ حَصَادِهِۦۖ وَلَا تُسۡرِفُوٓاْۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُسۡرِفِينَ
Kuma Shi ne Wanda Ya halicci lambuna waxanda suke da tsirrai masu yaxo da marasa yaxo da kuma dabino da shukoki waxanda suka sha bamban da juna wajen xanxanonsu, da kuma zaitun da ruman, mai kama da juna, da wanda ba ya kama da juna. Ku ci daga ‘ya’yansa, idan ya yi ‘ya’ya, kuma ku bayar da zakkarsa a ranar girbinsa, kuma kada ku yi almubazzaranci. Lalle Shi (Allah) ba Ya son masu almubazzaranci
وَمِنَ ٱلۡأَنۡعَٰمِ حَمُولَةٗ وَفَرۡشٗاۚ كُلُواْ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُ وَلَا تَتَّبِعُواْ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِۚ إِنَّهُۥ لَكُمۡ عَدُوّٞ مُّبِينٞ
Daga cikin dabbobin gida kuma akwai masu xaukan kaya da kuma qanana. Ku ci daga abin da Allah Ya arzuta ku da shi, kuma kada ku bi hanyoyin Shaixan. Lalle shi maqiyi ne mai bayyana qiyayya a gare ku
ثَمَٰنِيَةَ أَزۡوَٰجٖۖ مِّنَ ٱلضَّأۡنِ ٱثۡنَيۡنِ وَمِنَ ٱلۡمَعۡزِ ٱثۡنَيۡنِۗ قُلۡ ءَآلذَّكَرَيۡنِ حَرَّمَ أَمِ ٱلۡأُنثَيَيۡنِ أَمَّا ٱشۡتَمَلَتۡ عَلَيۡهِ أَرۡحَامُ ٱلۡأُنثَيَيۡنِۖ نَبِّـُٔونِي بِعِلۡمٍ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
(Dabbobin) nau’i takwas ne, daga tumaki akwai jinsi biyu, haka kuma daga awaki akwai jinsi biyu. Ka ce: “Shin mazan biyu ne Ya haramta ko kuma matan biyu ko kuma abin da yake cikin mahaifar matan biyu? Ku ba ni labari da ilimi in kun kasance ku masu gaskiya ne.”
وَمِنَ ٱلۡإِبِلِ ٱثۡنَيۡنِ وَمِنَ ٱلۡبَقَرِ ٱثۡنَيۡنِۗ قُلۡ ءَآلذَّكَرَيۡنِ حَرَّمَ أَمِ ٱلۡأُنثَيَيۡنِ أَمَّا ٱشۡتَمَلَتۡ عَلَيۡهِ أَرۡحَامُ ٱلۡأُنثَيَيۡنِۖ أَمۡ كُنتُمۡ شُهَدَآءَ إِذۡ وَصَّىٰكُمُ ٱللَّهُ بِهَٰذَاۚ فَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبٗا لِّيُضِلَّ ٱلنَّاسَ بِغَيۡرِ عِلۡمٍۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Haka kuma raquma akwai jinsi biyu, daga cikin shanu ma akwai jinsi biyu. Ka ce: “Shin mazan guda biyu Ya haramta ko matan biyu ko kuma abin da yake cikin mahaifar matan biyu ya haramta ko kuma kun zama shaidu yayin da Allah Ya yi muku wasicci da wannan abin?” To ba wanda ya fi zaluntar kansa fiye da wanda ya qirqiri qarya, ya jingina wa Allah don ya vatar da mutane ba tare da ilimi ba. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai
قُل لَّآ أَجِدُ فِي مَآ أُوحِيَ إِلَيَّ مُحَرَّمًا عَلَىٰ طَاعِمٖ يَطۡعَمُهُۥٓ إِلَّآ أَن يَكُونَ مَيۡتَةً أَوۡ دَمٗا مَّسۡفُوحًا أَوۡ لَحۡمَ خِنزِيرٖ فَإِنَّهُۥ رِجۡسٌ أَوۡ فِسۡقًا أُهِلَّ لِغَيۡرِ ٱللَّهِ بِهِۦۚ فَمَنِ ٱضۡطُرَّ غَيۡرَ بَاغٖ وَلَا عَادٖ فَإِنَّ رَبَّكَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Ka ce: “Daga cikin abin da aka sauqar mini na manzanci ban samu wani abinci da aka haramta cinsa ba, sai fa idan ya zamo mushe ne ko jini mai kwarara, ko kuma naman alade, to lalle wannan qazanta ne, ko kuma abin da ya zamo fasiqanci ne wanda aka yanka shi ba da sunan Allah ba.” Sannan wanda ya matsu, ba tare da shisshigi ba, kuma ba yana mai qetare iyaka ba, to lalle Ubangijinka Mai gafara ne, Mai jin qai
وَعَلَى ٱلَّذِينَ هَادُواْ حَرَّمۡنَا كُلَّ ذِي ظُفُرٖۖ وَمِنَ ٱلۡبَقَرِ وَٱلۡغَنَمِ حَرَّمۡنَا عَلَيۡهِمۡ شُحُومَهُمَآ إِلَّا مَا حَمَلَتۡ ظُهُورُهُمَآ أَوِ ٱلۡحَوَايَآ أَوۡ مَا ٱخۡتَلَطَ بِعَظۡمٖۚ ذَٰلِكَ جَزَيۡنَٰهُم بِبَغۡيِهِمۡۖ وَإِنَّا لَصَٰدِقُونَ
Kuma Mun haramta wa Yahudawa duk wata dabba mai kofato; daga shanu da tumaki kuwa Mun haramta musu kitsensu, sai abin da gadon bayansu yake xauke da shi ko kayan cikinsu ko abin da ya cakuxu da qashi[1]. Wannan Mun Yi musu sakamako da shi ne saboda zaluncinsu; kuma lalle Mu tabbas Masu gaskiya ne
1- Watau an haramta musu kitsen shanu da tumaki sai dai kitsen da ke gadon bayan waxannan dabbobi ko wanda yake tare da kayan ciki ko wanda ya haxe da qashi.
فَإِن كَذَّبُوكَ فَقُل رَّبُّكُمۡ ذُو رَحۡمَةٖ وَٰسِعَةٖ وَلَا يُرَدُّ بَأۡسُهُۥ عَنِ ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ
Sannan idan sun qaryata ka, to ka ce: “Ubangijinku Ma’abocin rahama mayalwaciya ne. Kuma ba a iya mayar da azabarsa daga mutanen da suke masu laifi.”
سَيَقُولُ ٱلَّذِينَ أَشۡرَكُواْ لَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَآ أَشۡرَكۡنَا وَلَآ ءَابَآؤُنَا وَلَا حَرَّمۡنَا مِن شَيۡءٖۚ كَذَٰلِكَ كَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ حَتَّىٰ ذَاقُواْ بَأۡسَنَاۗ قُلۡ هَلۡ عِندَكُم مِّنۡ عِلۡمٖ فَتُخۡرِجُوهُ لَنَآۖ إِن تَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَإِنۡ أَنتُمۡ إِلَّا تَخۡرُصُونَ
Waxanda suke yin shirka za su ce: “Da Allah Ya ga dama, da ba mu yi shirka ba, haka iyayenmu ma da ba su yi ba, kuma da ba mu haramta wani abu ba.” Kamar haka ne waxanda suka gabace su suka qaryata (manzanni), har sai da suka xanxani azabarmu. Ka ce: “Shin kuna da wata hujja ce da za ku fito mana da ita? Ba fa abin da kuke bi sai zato, kuma ku (ba a kan komai kuke ba) face shaci-faxi.”
قُلۡ فَلِلَّهِ ٱلۡحُجَّةُ ٱلۡبَٰلِغَةُۖ فَلَوۡ شَآءَ لَهَدَىٰكُمۡ أَجۡمَعِينَ
Ka ce: “To a wurin Allah ne cikakkiyar hujja take; kuma da Ya ga dama, tabbas da Ya shiryar da ku gaba xaya.”
قُلۡ هَلُمَّ شُهَدَآءَكُمُ ٱلَّذِينَ يَشۡهَدُونَ أَنَّ ٱللَّهَ حَرَّمَ هَٰذَاۖ فَإِن شَهِدُواْ فَلَا تَشۡهَدۡ مَعَهُمۡۚ وَلَا تَتَّبِعۡ أَهۡوَآءَ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ وَهُم بِرَبِّهِمۡ يَعۡدِلُونَ
Ka ce: “Ku kawo shaidunku waxanda za su ba da shaidar cewa, Allah Shi Ya haramta wannan.” Sannan idan har sun ba da shaidar, to kai kada ka bayar da shaida tare da su. Kuma kada ka bi soye-soyen zukatan waxanda suka qaryata ayoyinmu, waxanda kuma ba sa yin imani da ranar lahira, su ne kuwa masu daidaita Ubangijinsu (da wani abu)
۞قُلۡ تَعَالَوۡاْ أَتۡلُ مَا حَرَّمَ رَبُّكُمۡ عَلَيۡكُمۡۖ أَلَّا تُشۡرِكُواْ بِهِۦ شَيۡـٔٗاۖ وَبِٱلۡوَٰلِدَيۡنِ إِحۡسَٰنٗاۖ وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَوۡلَٰدَكُم مِّنۡ إِمۡلَٰقٖ نَّحۡنُ نَرۡزُقُكُمۡ وَإِيَّاهُمۡۖ وَلَا تَقۡرَبُواْ ٱلۡفَوَٰحِشَ مَا ظَهَرَ مِنۡهَا وَمَا بَطَنَۖ وَلَا تَقۡتُلُواْ ٱلنَّفۡسَ ٱلَّتِي حَرَّمَ ٱللَّهُ إِلَّا بِٱلۡحَقِّۚ ذَٰلِكُمۡ وَصَّىٰكُم بِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ
Ka ce: “Ku taho in karanta muku abin da Ubangijinku Ya haramta muku; kada ku haxa Shi da wani; kuma ku kyautata wa mahaifa; kuma kar ku kashe ‘ya’yanku saboda talauci; Mu ne za Mu arzuta ku har da su; kuma kada ku kusanci munanan (ayyuka) na sarari da na voye; kuma kada ku kashe ran da Allah Ya haramta (a kashe shi), sai idan da wani hakki. Wannan shi ne abin da (Allah) Ya yi muku wasiyya da shi, don ku zamo masu hankali
وَلَا تَقۡرَبُواْ مَالَ ٱلۡيَتِيمِ إِلَّا بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ أَشُدَّهُۥۚ وَأَوۡفُواْ ٱلۡكَيۡلَ وَٱلۡمِيزَانَ بِٱلۡقِسۡطِۖ لَا نُكَلِّفُ نَفۡسًا إِلَّا وُسۡعَهَاۖ وَإِذَا قُلۡتُمۡ فَٱعۡدِلُواْ وَلَوۡ كَانَ ذَا قُرۡبَىٰۖ وَبِعَهۡدِ ٱللَّهِ أَوۡفُواْۚ ذَٰلِكُمۡ وَصَّىٰكُم بِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ
“Kuma kada ku kusanci dukiyar maraya sai da kyakkyawar niyya, har sai qarfinsa ya kawo; kuma ku cika ma’auni na mudu da na nauyi bisa adalci; ba ma xora wa rai sai abin da zai iya. Kuma idan za ku yi magana to ku yi adalci, ko da kuwa a kan xan’uwa ne na kusa; kuma lalle ku cika alqawarin Allah. Wannan ne abin da (Allah) Yake yi muku wasicci da shi, don ku wa’azantu.”
وَأَنَّ هَٰذَا صِرَٰطِي مُسۡتَقِيمٗا فَٱتَّبِعُوهُۖ وَلَا تَتَّبِعُواْ ٱلسُّبُلَ فَتَفَرَّقَ بِكُمۡ عَن سَبِيلِهِۦۚ ذَٰلِكُمۡ وَصَّىٰكُم بِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ
“Kuma lalle wannan shi ne tafarkina miqaqqe, don haka ku bi shi; kada ku bi waxansu hanyoyi daban, sai su raba ku da hanyarsa. Wannan shi ne abin da (Allah) Yake yi muku wasicci da shi don ku samu taqawa.”
ثُمَّ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ تَمَامًا عَلَى ٱلَّذِيٓ أَحۡسَنَ وَتَفۡصِيلٗا لِّكُلِّ شَيۡءٖ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٗ لَّعَلَّهُم بِلِقَآءِ رَبِّهِمۡ يُؤۡمِنُونَ
Sannan Muka bai wa Musa littafin (Attaura) don cika (ni’imarmu) ga wanda ya kyautata, kuma bayani ne na kowane irin abu, kuma shiriya ne da rahama, domin su zamo masu imani da haxuwa da Ubangijinsu
وَهَٰذَا كِتَٰبٌ أَنزَلۡنَٰهُ مُبَارَكٞ فَٱتَّبِعُوهُ وَٱتَّقُواْ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ
Kuma wannan Littafi (Alqur’ani) Mun saukar da shi, yana mai cike da albarka, don haka ku bi shi, kuma ku kiyaye dokokin (Allah), domin a ji qan ku
أَن تَقُولُوٓاْ إِنَّمَآ أُنزِلَ ٱلۡكِتَٰبُ عَلَىٰ طَآئِفَتَيۡنِ مِن قَبۡلِنَا وَإِن كُنَّا عَن دِرَاسَتِهِمۡ لَغَٰفِلِينَ
Don kada ku ce: “Qungiya biyu ne waxanda suka gabace mu kawai aka sauqar wa da Littafi, mu kuma ba mu san komai game da abin da suka karanta ba.”
أَوۡ تَقُولُواْ لَوۡ أَنَّآ أُنزِلَ عَلَيۡنَا ٱلۡكِتَٰبُ لَكُنَّآ أَهۡدَىٰ مِنۡهُمۡۚ فَقَدۡ جَآءَكُم بَيِّنَةٞ مِّن رَّبِّكُمۡ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٞۚ فَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن كَذَّبَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَصَدَفَ عَنۡهَاۗ سَنَجۡزِي ٱلَّذِينَ يَصۡدِفُونَ عَنۡ ءَايَٰتِنَا سُوٓءَ ٱلۡعَذَابِ بِمَا كَانُواْ يَصۡدِفُونَ
Ko kuma ku ce: “In da mu aka saukar wa da littafin, to da lalle mun fi su shiryuwa.” To ai haqiqa hujja ta riga ta zo muku daga Ubangijinku, da kuma shiriya da rahama; don haka babu wanda ya fi zalunci fiye da wanda ya qaryata ayoyin Allah, kuma ya yi watsi da su. Da sannu za Mu saka wa waxanda suke bijire wa ayoyinmu da mummunar azaba, saboda bijirewar da suke yi
هَلۡ يَنظُرُونَ إِلَّآ أَن تَأۡتِيَهُمُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ أَوۡ يَأۡتِيَ رَبُّكَ أَوۡ يَأۡتِيَ بَعۡضُ ءَايَٰتِ رَبِّكَۗ يَوۡمَ يَأۡتِي بَعۡضُ ءَايَٰتِ رَبِّكَ لَا يَنفَعُ نَفۡسًا إِيمَٰنُهَا لَمۡ تَكُنۡ ءَامَنَتۡ مِن قَبۡلُ أَوۡ كَسَبَتۡ فِيٓ إِيمَٰنِهَا خَيۡرٗاۗ قُلِ ٱنتَظِرُوٓاْ إِنَّا مُنتَظِرُونَ
Sannan ba abin da suke sauraro face mala’iku su zo musu ko Ubangijinka Ya zo musu ko wani sashi na ayoyin Ubangijinka su zo. Ranar da wasu daga ayoyin Ubangijinka za su zo, to babu wani rai da imaninsa zai yi amfani, idan a da can bai yi imani ba ko bai yi aikin alheri ba cikin imaninsa. Ka ce: “Ku jira, mu ma masu jira ne.”
إِنَّ ٱلَّذِينَ فَرَّقُواْ دِينَهُمۡ وَكَانُواْ شِيَعٗا لَّسۡتَ مِنۡهُمۡ فِي شَيۡءٍۚ إِنَّمَآ أَمۡرُهُمۡ إِلَى ٱللَّهِ ثُمَّ يُنَبِّئُهُم بِمَا كَانُواْ يَفۡعَلُونَ
Lalle waxanda suka rarraba addininsu kuma suka kasance qungiya-qungiya, to ba ruwanka da su. Al’amarinsu yana ga Allah ne kawai, sannan zai ba su labarin abin da suka kasance suna aikatawa
مَن جَآءَ بِٱلۡحَسَنَةِ فَلَهُۥ عَشۡرُ أَمۡثَالِهَاۖ وَمَن جَآءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَلَا يُجۡزَىٰٓ إِلَّا مِثۡلَهَا وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ
Wanda ya zo da kyakkyawan aiki xaya, to yana da ninkin ladansa goma; wanda kuwa ya zo da mummuna xaya, to ba za a saka masa ba sai daidai da shi, ba kuma za a zalunce su ba
قُلۡ إِنَّنِي هَدَىٰنِي رَبِّيٓ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ دِينٗا قِيَمٗا مِّلَّةَ إِبۡرَٰهِيمَ حَنِيفٗاۚ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ
Ka ce: “Lalle ni, Ubangijina Ya shiryar da ni zuwa ga tafarki madaidaici, shi ne addini miqaqqe, addinin Ibrahimu wanda ya karkace wa varna, kuma bai zama daga masu shirka ba.”
قُلۡ إِنَّ صَلَاتِي وَنُسُكِي وَمَحۡيَايَ وَمَمَاتِي لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Ka ce: “Lalle sallata da yankana da rayuwata da mutuwata, duk na Allah ne Ubangijin talikai
لَا شَرِيكَ لَهُۥۖ وَبِذَٰلِكَ أُمِرۡتُ وَأَنَا۠ أَوَّلُ ٱلۡمُسۡلِمِينَ
“Ba Shi da abokin tarayya; kuma da hakan aka umarce ni, kuma ni ne farkon Musulmai.”
قُلۡ أَغَيۡرَ ٱللَّهِ أَبۡغِي رَبّٗا وَهُوَ رَبُّ كُلِّ شَيۡءٖۚ وَلَا تَكۡسِبُ كُلُّ نَفۡسٍ إِلَّا عَلَيۡهَاۚ وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰۚ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُم مَّرۡجِعُكُمۡ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ فِيهِ تَخۡتَلِفُونَ
Ka ce: “Yanzu wanin Allah zan riqa a matsayin ubangiji, alhalin kuwa Shi ne Ubangijin komai? Kuma ba wani rai da zai aikata wani abu face sai don kansa. Kuma ba wani rai da zai xauki laifin wani rai. Sannan kuma zuwa ga Ubangijinku ne makomarku take, sai Ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna savani a game da shi
وَهُوَ ٱلَّذِي جَعَلَكُمۡ خَلَـٰٓئِفَ ٱلۡأَرۡضِ وَرَفَعَ بَعۡضَكُمۡ فَوۡقَ بَعۡضٖ دَرَجَٰتٖ لِّيَبۡلُوَكُمۡ فِي مَآ ءَاتَىٰكُمۡۗ إِنَّ رَبَّكَ سَرِيعُ ٱلۡعِقَابِ وَإِنَّهُۥ لَغَفُورٞ رَّحِيمُۢ
“Kuma Shi ne Ya sanya ku halifofi a bayan qasa, kuma Ya xaukaka darajar wasunku a kan wasu, don Ya jarrabe ku game da abin da Ya ba ku. Lalle Ubangijinka Mai gaggawar uquba ne, kuma lalle Shi tabbas Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin qai.”