Surah: Suratul Bayyina

Ayah : 1

لَمۡ يَكُنِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ وَٱلۡمُشۡرِكِينَ مُنفَكِّينَ حَتَّىٰ تَأۡتِيَهُمُ ٱلۡبَيِّنَةُ

Waxanda suka kafirta daga ma’abota littafi da mushirikai ba su zamanto masu barin abin da suke kai (na kafirci) ba har sai hujja bayyananniya ta zo musu



Surah: Suratul Bayyina

Ayah : 2

رَسُولٞ مِّنَ ٱللَّهِ يَتۡلُواْ صُحُفٗا مُّطَهَّرَةٗ

(Watau) Manzo daga Allah da zai riqa karanta (musu) takardu masu tsarki



Surah: Suratul Bayyina

Ayah : 3

فِيهَا كُتُبٞ قَيِّمَةٞ

(Waxanda) a cikinsu akwai hukunce-hukunce masu qima



Surah: Suratul Bayyina

Ayah : 4

وَمَا تَفَرَّقَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡهُمُ ٱلۡبَيِّنَةُ

Waxanda kuma aka bai wa littafi ba su rarraba ba[1] sai bayan da hujja bayyananniya ta zo musu


1- Watau Yahudawa da Nasara ba su rarrabu ba suka zama qungiya-qungiya wasu suka yi imani da Manzo Allah (), wasu kuma suka kafirce.


Surah: Suratul Bayyina

Ayah : 5

وَمَآ أُمِرُوٓاْ إِلَّا لِيَعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ حُنَفَآءَ وَيُقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤۡتُواْ ٱلزَّكَوٰةَۚ وَذَٰلِكَ دِينُ ٱلۡقَيِّمَةِ

Ba a kuma umarce su ba sai don su bauta wa Allah suna masu tsantsanta addini gare Shi, suna masu kauce wa varna, suna kuma tsayar da salla, kuma suna ba da zakka. Wannan kuwa shi ne addinin miqaqqiyar hanya



Surah: Suratul Bayyina

Ayah : 6

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ وَٱلۡمُشۡرِكِينَ فِي نَارِ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَآۚ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمۡ شَرُّ ٱلۡبَرِيَّةِ

Lalle waxanda suka kafirta daga ma’abota littafi da mushirikai suna cikin wutar Jahannama suna madawwama a cikinta. Waxannan su ne mafiya sharrin halitta



Surah: Suratul Bayyina

Ayah : 7

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمۡ خَيۡرُ ٱلۡبَرِيَّةِ

Lalle waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, waxannan su ne mafiya alherin halitta



Surah: Suratul Bayyina

Ayah : 8

جَزَآؤُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ جَنَّـٰتُ عَدۡنٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۖ رَّضِيَ ٱللَّهُ عَنۡهُمۡ وَرَضُواْ عَنۡهُۚ ذَٰلِكَ لِمَنۡ خَشِيَ رَبَّهُۥ

Sakamakonsu a wajen Ubangijinsu gidajen Aljanna ne na dawwama waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu suna madawwama a cikinsu har abada; Allah Ya yarda da su, su ma sun yarda da Shi. Wannan kuma (sakamako ne) ga wanda ya ji tsoron Ubangijinsa