وَٱلَّيۡلِ إِذَا يَغۡشَىٰ
Na rantse da dare idan ya lulluve (da duhunsa)
Share :
وَٱلنَّهَارِ إِذَا تَجَلَّىٰ
Da kuma wuni idan ya bayyana
وَمَا خَلَقَ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰٓ
Da kuma halittar namiji da mace
إِنَّ سَعۡيَكُمۡ لَشَتَّىٰ
Lalle aikinku ya sha bamban
فَأَمَّا مَنۡ أَعۡطَىٰ وَٱتَّقَىٰ
To wanda ya ba da (haqqoqin da ke kansa) ya kuma yi taqawa
وَصَدَّقَ بِٱلۡحُسۡنَىٰ
Ya kuma gaskata (sakamako) mafi kyau
فَسَنُيَسِّرُهُۥ لِلۡيُسۡرَىٰ
To lalle ne za Mu sauqaqa masa (hanyar) Aljanna
وَأَمَّا مَنۢ بَخِلَ وَٱسۡتَغۡنَىٰ
Amma kuma wanda ya yi rowa (da haqqin Allah) ya kuma wadatu (da neman lada)
وَكَذَّبَ بِٱلۡحُسۡنَىٰ
Kuma ya qaryata (sakamako) mafi kyau
فَسَنُيَسِّرُهُۥ لِلۡعُسۡرَىٰ
To lalle ne za Mu hore masa (hanyar) wuta
وَمَا يُغۡنِي عَنۡهُ مَالُهُۥٓ إِذَا تَرَدَّىٰٓ
Dukiyarsa kuma ba za ta amfane shi ba idan ya gangara (cikin wuta)
إِنَّ عَلَيۡنَا لَلۡهُدَىٰ
Lalle bayyana hanyar shiriya a kanmu yake
وَإِنَّ لَنَا لَلۡأٓخِرَةَ وَٱلۡأُولَىٰ
Kuma lalle lahira da duniya namu ne
فَأَنذَرۡتُكُمۡ نَارٗا تَلَظَّىٰ
Don haka ina yi muku gargaxin wata wuta mai ruruwa
لَا يَصۡلَىٰهَآ إِلَّا ٱلۡأَشۡقَى
Ba mai shigar ta sai mafi tsiyacewa
ٱلَّذِي كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ
Wanda ya qaryata ya kuma ba da baya
وَسَيُجَنَّبُهَا ٱلۡأَتۡقَى
Kuma lalle za a nesantar da mafi taqawa[1] daga gare ta
1- Da dama daga cikin malaman tafsiri sun bayyana cewa a nan ana nufin Abubakar As-Siddiq ().
ٱلَّذِي يُؤۡتِي مَالَهُۥ يَتَزَكَّىٰ
Wanda yake ba da dukiyarsa yana neman tsarkaka
وَمَا لِأَحَدٍ عِندَهُۥ مِن نِّعۡمَةٖ تُجۡزَىٰٓ
Ba kuwa wani da ya yi masa wata ni’ima da za a saka masa (a kanta)[1]
1- Watau ba yana ciyar da dukiyarsa ne don ya saka wa wani a kan wata ni’ima da ya yi masa ba.
إِلَّا ٱبۡتِغَآءَ وَجۡهِ رَبِّهِ ٱلۡأَعۡلَىٰ
Sai dai don neman Fuskar Ubangijinsa Maxaukaki
وَلَسَوۡفَ يَرۡضَىٰ
Kuma lalle zai yarda (da sakamakon da za a ba shi)[1]
1- Watau gidan Aljanna a lahira.