Surah: Suratul Balad

Ayah : 1

لَآ أُقۡسِمُ بِهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ

Na rantse da wannan gari (na Makka)



Surah: Suratul Balad

Ayah : 2

وَأَنتَ حِلُّۢ بِهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ

Alhali kuwa kai an halatta maka wannan gari[1]


1- Watau an halatta masa kashe wanda ya cancanci kisa a garin Makka. Ko kuma ana nufin Allah ya yi rantsuwa da Makka musamman lokacin da Annabi () yake zaune a cikinta.


Surah: Suratul Balad

Ayah : 3

وَوَالِدٖ وَمَا وَلَدَ

(Na rantse) da mahaifi da abin da ya haifa[1]


1- Watau Annabi Adamu () da zurriyarsa. Ko kuma duk wani mahaifi da duk wani wanda aka haifa.


Surah: Suratul Balad

Ayah : 4

لَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ فِي كَبَدٍ

Haqiqa Mun halicci mutum cikin wahala



Surah: Suratul Balad

Ayah : 5

أَيَحۡسَبُ أَن لَّن يَقۡدِرَ عَلَيۡهِ أَحَدٞ

Yanzu mutum yana tsammanin cewa wani ba zai sami iko a kansa ba?



Surah: Suratul Balad

Ayah : 6

يَقُولُ أَهۡلَكۡتُ مَالٗا لُّبَدًا

Yana cewa: “Na vatar da dukiya mai ximbin yawa.”



Surah: Suratul Balad

Ayah : 7

أَيَحۡسَبُ أَن لَّمۡ يَرَهُۥٓ أَحَدٌ

Shin yana tsammanin cewa ba wanda ya gan shi?



Surah: Suratul Balad

Ayah : 8

أَلَمۡ نَجۡعَل لَّهُۥ عَيۡنَيۡنِ

Shin ba Mu sanya masa idanuwa biyu ba ne?



Surah: Suratul Balad

Ayah : 9

وَلِسَانٗا وَشَفَتَيۡنِ

Da harshe da kuma lavva biyu?



Surah: Suratul Balad

Ayah : 10

وَهَدَيۡنَٰهُ ٱلنَّجۡدَيۡنِ

Muka kuma bayyana masa hanyoyi biyu[1]?


1- Watau hanyar alheri da hanyar sharri.


Surah: Suratul Balad

Ayah : 11

فَلَا ٱقۡتَحَمَ ٱلۡعَقَبَةَ

Sai bai qetare hanya mai wahala[1] ba?


1- Watau hanyar da ta raba tsakaninsa da gidan Aljanna.


Surah: Suratul Balad

Ayah : 12

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡعَقَبَةُ

Me kuma ya sanar da kai mece ce hanya mai wahala?



Surah: Suratul Balad

Ayah : 13

فَكُّ رَقَبَةٍ

(Watau) ‘yanta wuyaye (bawa ko baiwa)



Surah: Suratul Balad

Ayah : 14

أَوۡ إِطۡعَٰمٞ فِي يَوۡمٖ ذِي مَسۡغَبَةٖ

Ko kuma ciyarwa a wata rana ta yunwa



Surah: Suratul Balad

Ayah : 15

يَتِيمٗا ذَا مَقۡرَبَةٍ

Ga maraya ma’abocin kusanci



Surah: Suratul Balad

Ayah : 16

أَوۡ مِسۡكِينٗا ذَا مَتۡرَبَةٖ

Ko miskini ma’abocin talauci



Surah: Suratul Balad

Ayah : 17

ثُمَّ كَانَ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَتَوَاصَوۡاْ بِٱلصَّبۡرِ وَتَوَاصَوۡاْ بِٱلۡمَرۡحَمَةِ

Sannan kuma ya zama daga waxanda suka yi imani, suka yi wa junansu wasiyya da yin haquri kuma suka yi wa juna wasiyya da tausayawa



Surah: Suratul Balad

Ayah : 18

أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ

Waxannan su ne ma’abota dama[1]


1- Watau ‘yan Aljanna.


Surah: Suratul Balad

Ayah : 19

وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِنَا هُمۡ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ

Waxanda kuwa suka kafirce wa ayoyinmu, su ne ma’abota hagu[1]


1- Watau ‘yan wuta.


Surah: Suratul Balad

Ayah : 20

عَلَيۡهِمۡ نَارٞ مُّؤۡصَدَةُۢ

A kansu akwai wuta abar kullewa