وَٱلۡفَجۡرِ
Na rantse da alfijir
Share :
وَلَيَالٍ عَشۡرٖ
Da kuma darare goma[1]
1- Watau kwanaki goma na farkon watan Zulhijja.
وَٱلشَّفۡعِ وَٱلۡوَتۡرِ
Da kuma abin da yake cika[1] da kuma mara[2]
1- Watau bibbiyu ko hurhuxu ko shida-shida da sauransu.2- Watau xaya ko uku ko biyar da sauransu.
وَٱلَّيۡلِ إِذَا يَسۡرِ
Da kuma dare lokacin da yake tafiya (cikin duhu)
هَلۡ فِي ذَٰلِكَ قَسَمٞ لِّذِي حِجۡرٍ
Shin a game da waxannan akwai rantsuwa (mai gamsarwa) ga mai hankali[1]?
1- Watau duk mai hankali zai gamsu da waxannan rantse-rantse.
أَلَمۡ تَرَ كَيۡفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِعَادٍ
Shin ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ba ga Adawa?
إِرَمَ ذَاتِ ٱلۡعِمَادِ
(Watau qabilar) Iramu ma’abociyar tsawo
ٱلَّتِي لَمۡ يُخۡلَقۡ مِثۡلُهَا فِي ٱلۡبِلَٰدِ
Wadda ba a halicci irinta ba a cikin garuruwa (a tsananin qarfi)
وَثَمُودَ ٱلَّذِينَ جَابُواْ ٱلصَّخۡرَ بِٱلۡوَادِ
Da kuma Samudawa waxanda suka fafe duwatsu a wurin da ake kira Wadil-Qura
وَفِرۡعَوۡنَ ذِي ٱلۡأَوۡتَادِ
Da kuma Fir’auna ma’abocin turaku
ٱلَّذِينَ طَغَوۡاْ فِي ٱلۡبِلَٰدِ
Waxanda suka yi xagawa a cikin garuruwa
فَأَكۡثَرُواْ فِيهَا ٱلۡفَسَادَ
Suka kuma yawaita varna a cikinsu
فَصَبَّ عَلَيۡهِمۡ رَبُّكَ سَوۡطَ عَذَابٍ
Sai Ubangijinka Ya saukar musu azaba mai tsanani
إِنَّ رَبَّكَ لَبِٱلۡمِرۡصَادِ
Lalle Ubangijinka tabbas Yana nan a madakata[1]
1- Watau yana wurin da yake hangen xaukacin ayyukan bayinsa.
فَأَمَّا ٱلۡإِنسَٰنُ إِذَا مَا ٱبۡتَلَىٰهُ رَبُّهُۥ فَأَكۡرَمَهُۥ وَنَعَّمَهُۥ فَيَقُولُ رَبِّيٓ أَكۡرَمَنِ
Amma kuma mutum idan Ubangijinsa Ya jarrabe shi sai Ya karrama shi, Ya kuma yi masa ni’ima, sai ya ce: “Ubangijina Ya karrama ni.”
وَأَمَّآ إِذَا مَا ٱبۡتَلَىٰهُ فَقَدَرَ عَلَيۡهِ رِزۡقَهُۥ فَيَقُولُ رَبِّيٓ أَهَٰنَنِ
Amma kuma idan Ya jarrabe shi sai Ya quntata masa a arzikinsa, sai ya ce: “Ubangijina Ya wulaqanta ni.”
كَلَّاۖ بَل لَّا تُكۡرِمُونَ ٱلۡيَتِيمَ
Faufau, ba haka ba ne; ku ba kwa karrama maraya ne
وَلَا تَحَـٰٓضُّونَ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلۡمِسۡكِينِ
Kuma ba kwa kwaxaitar da juna kan ciyar da miskinai
وَتَأۡكُلُونَ ٱلتُّرَاثَ أَكۡلٗا لَّمّٗا
Kuma kuna cinye dukiyar gadon marayu mummunan ci
وَتُحِبُّونَ ٱلۡمَالَ حُبّٗا جَمّٗا
Kuma kuna son dukiya so mai yawa
كَلَّآۖ إِذَا دُكَّتِ ٱلۡأَرۡضُ دَكّٗا دَكّٗا
Ba haka ne ba, idan aka girgiza qasa matuqar girgiza
وَجَآءَ رَبُّكَ وَٱلۡمَلَكُ صَفّٗا صَفّٗا
Ubangijinka kuma Ya zo[1] tare da mala’iku sahu-sahu
1- Watau don yin hukunci a tsakanin bayinsa.
وَجِاْيٓءَ يَوۡمَئِذِۭ بِجَهَنَّمَۚ يَوۡمَئِذٖ يَتَذَكَّرُ ٱلۡإِنسَٰنُ وَأَنَّىٰ لَهُ ٱلذِّكۡرَىٰ
Aka kuma zo da Jahannama a wannan ranar. To fa a wannan ranar ne mutum zai tuna (sakacinsa), ta yaya wannan tunawar za ta yi masa amfani?
يَقُولُ يَٰلَيۡتَنِي قَدَّمۡتُ لِحَيَاتِي
Zai ce: “Kaitona, ina ma da na gabatar (da ayyukan alheri) a rayuwata!”
فَيَوۡمَئِذٖ لَّا يُعَذِّبُ عَذَابَهُۥٓ أَحَدٞ
To a wannan ranar ba wani xaya da zai yi azaba irin azabarsa (watau Allah)
وَلَا يُوثِقُ وَثَاقَهُۥٓ أَحَدٞ
Ba kuma xaya da zai yi xauri irin xaurinsa
يَـٰٓأَيَّتُهَا ٱلنَّفۡسُ ٱلۡمُطۡمَئِنَّةُ
(Za a ce): Ya kai wannan rai mai nutsuwa
ٱرۡجِعِيٓ إِلَىٰ رَبِّكِ رَاضِيَةٗ مَّرۡضِيَّةٗ
Ka koma zuwa ga Ubangijinka kana mai yarda (da sakamako), abin yarda
فَٱدۡخُلِي فِي عِبَٰدِي
Don haka ka shiga cikin bayina
وَٱدۡخُلِي جَنَّتِي
Ka kuma shiga Aljannata