إِذَا ٱلشَّمۡسُ كُوِّرَتۡ
Idan rana aka naxe ta[1]
1- Watau aka haxa ta da wata wuri xaya, aka kuma tafiyar da haskenta.
Share :
وَإِذَا ٱلنُّجُومُ ٱنكَدَرَتۡ
Idan kuma taurari suka farfaxo
وَإِذَا ٱلۡجِبَالُ سُيِّرَتۡ
Idan kuma duwatsu aka tafiyar da su
وَإِذَا ٱلۡعِشَارُ عُطِّلَتۡ
Idan kuma raquma masu ciki aka bar su ba makiyayi
وَإِذَا ٱلۡوُحُوشُ حُشِرَتۡ
Idan kuma namun daji aka tattara su[1]
1- Watau aka tattara su wuri guda tare da ‘yan’adam.
وَإِذَا ٱلۡبِحَارُ سُجِّرَتۡ
Idan kuma koguna aka rura su (suka zama wuta)
وَإِذَا ٱلنُّفُوسُ زُوِّجَتۡ
Idan kuma rayuka aka haxa su (da jinsinsu)
وَإِذَا ٱلۡمَوۡءُۥدَةُ سُئِلَتۡ
Idan kuma yarinyar da aka binne da rai aka tambaye ta
بِأَيِّ ذَنۢبٖ قُتِلَتۡ
Da wane laifi ne aka kashe ta?
وَإِذَا ٱلصُّحُفُ نُشِرَتۡ
Idan kuma takardun (ayyuka) aka baza su[1]
1- Watau don kowa ya karanta takardarsa da kansa.
وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ كُشِطَتۡ
Idan kuma sama aka xaye ta
وَإِذَا ٱلۡجَحِيمُ سُعِّرَتۡ
Idan kuma wutar Jahimu aka hura ta
وَإِذَا ٱلۡجَنَّةُ أُزۡلِفَتۡ
Idan kuma Aljanna aka kusanto da ita[1]
1- Watau aka matso da ita dab da masu taqawa.
عَلِمَتۡ نَفۡسٞ مَّآ أَحۡضَرَتۡ
To kowane rai ya san abin da ya halarto (da shi na ayyuka)
فَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلۡخُنَّسِ
To ina rantsuwa da taurari masu vuya[1]
1- Watau suna vuya lokacin hudowar hasken asuba, kamar yadda gada take voyewa a cikin gidanta.
ٱلۡجَوَارِ ٱلۡكُنَّسِ
Masu gudu zuwa masaukansu
وَٱلَّيۡلِ إِذَا عَسۡعَسَ
Da kuma dare idan ya yi duhu
وَٱلصُّبۡحِ إِذَا تَنَفَّسَ
Da kuma asuba idan ta keto
إِنَّهُۥ لَقَوۡلُ رَسُولٖ كَرِيمٖ
Lalle shi (Alqur’ani) magana ce ta Manzo mai karamci[1]
1- Watau Mala’ika Jibrilu () wanda Allah ya amince masa ya isar wa da Manzon Allah () zancensa.
ذِي قُوَّةٍ عِندَ ذِي ٱلۡعَرۡشِ مَكِينٖ
Ma’abocin qarfi a wurin Mai Al’arshi, kuma mai babban matsayi
مُّطَاعٖ ثَمَّ أَمِينٖ
Wanda ake yi wa biyayya ne a can (sama), amintacce
وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجۡنُونٖ
Mutumin naku kuma (watau Ma’aiki) ba mahaukaci ba ne
وَلَقَدۡ رَءَاهُ بِٱلۡأُفُقِ ٱلۡمُبِينِ
Haqiqa kuma ya gan shi a sararin sama mabayyani[1]
1- Watau Annabi () ya ga Mala’ika Jibrilu () a surarsa ta asali a sararin samaniya.
وَمَا هُوَ عَلَى ٱلۡغَيۡبِ بِضَنِينٖ
Shi kuma ba mai rowa ba ne game da wahayi
وَمَا هُوَ بِقَوۡلِ شَيۡطَٰنٖ رَّجِيمٖ
Kuma shi (Alqur’ani) ba zancen Shaixan ne la’ananne ba
فَأَيۡنَ تَذۡهَبُونَ
To ina za ku dosa ne[1]?
1- Watau ina mushirikai suka dosa wajen qaryata Alqur’an bayan sun ji hujjoji masu qarfi?
إِنۡ هُوَ إِلَّا ذِكۡرٞ لِّلۡعَٰلَمِينَ
Shi ba wani abu ba ne sai wa’azi ga talikai
لِمَن شَآءَ مِنكُمۡ أَن يَسۡتَقِيمَ
Ga wanda ya ga dama daga cikinku ya bi hanya madaidaiciya
وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Ku kuma ba za ku iya ganin dama ba sai Allah Ubangijin talikai Ya ga dama