Surah: Suratu Nuh

Ayah : 1

إِنَّآ أَرۡسَلۡنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوۡمِهِۦٓ أَنۡ أَنذِرۡ قَوۡمَكَ مِن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Lalle Mu Mun aika Nuhu zuwa ga mutanensa cewa: “Ka gargaxi mutanenka tun kafin azaba mai raxaxi ta zo musu.”



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 2

قَالَ يَٰقَوۡمِ إِنِّي لَكُمۡ نَذِيرٞ مُّبِينٌ

Ya ce: “Ya ku mutanena, lalle ni mai gargaxi ne mabayyani a gare ku



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 3

أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَٱتَّقُوهُ وَأَطِيعُونِ

“Kan ku bauta wa Allah, ku kiyaye dokokinsa, kuma ku bi ni



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 4

يَغۡفِرۡ لَكُم مِّن ذُنُوبِكُمۡ وَيُؤَخِّرۡكُمۡ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمًّىۚ إِنَّ أَجَلَ ٱللَّهِ إِذَا جَآءَ لَا يُؤَخَّرُۚ لَوۡ كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

“Zai gafarta muku zunubanku, Ya kuma jinkirta muku har zuwa wani lokaci iyakantacce. Lalle ajalin Allah idan ya zo ba a saurarawa; da kun kasance kun san (haka)



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 5

قَالَ رَبِّ إِنِّي دَعَوۡتُ قَوۡمِي لَيۡلٗا وَنَهَارٗا

Ya ce: “Ya Ubangijina, lalle ni na kira mutanena dare da rana



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 6

فَلَمۡ يَزِدۡهُمۡ دُعَآءِيٓ إِلَّا فِرَارٗا

“To kiran nawa ba abin da ya qara musu sai tawaye



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 7

وَإِنِّي كُلَّمَا دَعَوۡتُهُمۡ لِتَغۡفِرَ لَهُمۡ جَعَلُوٓاْ أَصَٰبِعَهُمۡ فِيٓ ءَاذَانِهِمۡ وَٱسۡتَغۡشَوۡاْ ثِيَابَهُمۡ وَأَصَرُّواْ وَٱسۡتَكۡبَرُواْ ٱسۡتِكۡبَارٗا

“Lalle ni kuma duk sanda na kira su don Ka gafarta musu, sai su sanya ‘yan yatsunsu a cikin kunnuwansu, su kuma lulluvu da tufafinsu[1] kuma su kafe (a kan haka), su yi girman kai matuqar girman kai


1- Watau don kada su saurari abin da yake faxa musu, kada kuma su gan shi da idanuwansu.


Surah: Suratu Nuh

Ayah : 8

ثُمَّ إِنِّي دَعَوۡتُهُمۡ جِهَارٗا

“Sannan lalle na yi kiran su da babbar murya



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 9

ثُمَّ إِنِّيٓ أَعۡلَنتُ لَهُمۡ وَأَسۡرَرۡتُ لَهُمۡ إِسۡرَارٗا

“Sannan lalle na yi musu a bayyane, na kuma yi musu a voye sosai



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 10

فَقُلۡتُ ٱسۡتَغۡفِرُواْ رَبَّكُمۡ إِنَّهُۥ كَانَ غَفَّارٗا

“Sai na ce: “Ku nemi gafarar Ubangijinku, lalle Shi Ya kasance Mai yawan gafara ne



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 11

يُرۡسِلِ ٱلسَّمَآءَ عَلَيۡكُم مِّدۡرَارٗا

“Zai saukar muku da ruwan sama mai yawa



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 12

وَيُمۡدِدۡكُم بِأَمۡوَٰلٖ وَبَنِينَ وَيَجۡعَل لَّكُمۡ جَنَّـٰتٖ وَيَجۡعَل لَّكُمۡ أَنۡهَٰرٗا

“Kuma Ya daxe ku da dukiyoyi da ‘ya’yaye, Ya kuma sanya muku gonaki Ya kuma gudanar muku da qoramu



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 13

مَّا لَكُمۡ لَا تَرۡجُونَ لِلَّهِ وَقَارٗا

“Me ya same ku ne ba kwa ganin girman Allah?



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 14

وَقَدۡ خَلَقَكُمۡ أَطۡوَارًا

“Haqiqa kuma Ya halicce ku ta mataki-mataki



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 15

أَلَمۡ تَرَوۡاْ كَيۡفَ خَلَقَ ٱللَّهُ سَبۡعَ سَمَٰوَٰتٖ طِبَاقٗا

“Shin ba kwa ganin yadda Allah Ya halicci sammai bakwai rufi-rufi?



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 16

وَجَعَلَ ٱلۡقَمَرَ فِيهِنَّ نُورٗا وَجَعَلَ ٱلشَّمۡسَ سِرَاجٗا

“Ya kuma sanya wata mai haske a cikinsu; rana kuma Ya sanya ta fitila?



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 17

وَٱللَّهُ أَنۢبَتَكُم مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ نَبَاتٗا

“Allah ne kuma Ya tsiro da ku daga qasa a tsirowa (ta halitta)[1]


1- Watau ya halicce su daga qasa ta hanyar halittar babansu Annabi Adamu (), suna kuma cin abin da qasar ta tsiro da shi.


Surah: Suratu Nuh

Ayah : 18

ثُمَّ يُعِيدُكُمۡ فِيهَا وَيُخۡرِجُكُمۡ إِخۡرَاجٗا

“Sannan Ya mayar da ku cikinta, zai kuma fitar da ku haqiqar fitarwa



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 19

وَٱللَّهُ جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ بِسَاطٗا

“Kuma Allah Ya sanya muku qasa a shimfixe



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 20

لِّتَسۡلُكُواْ مِنۡهَا سُبُلٗا فِجَاجٗا

“Don ku riqa bin manya-manyan hanyoyi a cikinta.”



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 21

قَالَ نُوحٞ رَّبِّ إِنَّهُمۡ عَصَوۡنِي وَٱتَّبَعُواْ مَن لَّمۡ يَزِدۡهُ مَالُهُۥ وَوَلَدُهُۥٓ إِلَّا خَسَارٗا

Nuhu ya ce, “Ya Ubangijina, lalle su sun sava mini, sun kuma bi duk wanda dukiyarsa da ‘ya’yansa ba su qara masa komai ba sai asara



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 22

وَمَكَرُواْ مَكۡرٗا كُبَّارٗا

“Suka kuma shirya makirci babba



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 23

وَقَالُواْ لَا تَذَرُنَّ ءَالِهَتَكُمۡ وَلَا تَذَرُنَّ وَدّٗا وَلَا سُوَاعٗا وَلَا يَغُوثَ وَيَعُوقَ وَنَسۡرٗا

“Suka kuma ce: ‘Kada ku bar abubuwan bautarku, kuma lalle kada ku bar Waddu da Suwa’u da Yagusu da Ya’uqu da Nasaru[1].’


1- Waxannan duk sunayen wasu mutanen kirki ne waliyyai da mutanen Annabi Nuhu () suka sassaqa gumaka da sunayensu suna bauta musu.


Surah: Suratu Nuh

Ayah : 24

وَقَدۡ أَضَلُّواْ كَثِيرٗاۖ وَلَا تَزِدِ ٱلظَّـٰلِمِينَ إِلَّا ضَلَٰلٗا

“Haqiqa kuwa sun vatar da adadi mai yawa; kar kuma Ka qari kafirai da komai sai vata.”



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 25

مِّمَّا خَطِيٓـَٰٔتِهِمۡ أُغۡرِقُواْ فَأُدۡخِلُواْ نَارٗا فَلَمۡ يَجِدُواْ لَهُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ أَنصَارٗا

Saboda savonsu ne aka nutsar da su, sai aka shigar da su wuta, don haka, ba su sami wasu mataimaka ba Allah ba



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 26

وَقَالَ نُوحٞ رَّبِّ لَا تَذَرۡ عَلَى ٱلۡأَرۡضِ مِنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ دَيَّارًا

Nuhu ya ce: “Ya Ubangijina, kada Ka bar wani mutum xaya daga kafirai a bayan qasa



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 27

إِنَّكَ إِن تَذَرۡهُمۡ يُضِلُّواْ عِبَادَكَ وَلَا يَلِدُوٓاْ إِلَّا فَاجِرٗا كَفَّارٗا

“Lalle idan har Ka bar su, to za su vatar da bayinka, kuma ba za su haifi kowa ba sai fajiri mai tsananin kafirci



Surah: Suratu Nuh

Ayah : 28

رَّبِّ ٱغۡفِرۡ لِي وَلِوَٰلِدَيَّ وَلِمَن دَخَلَ بَيۡتِيَ مُؤۡمِنٗا وَلِلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِۖ وَلَا تَزِدِ ٱلظَّـٰلِمِينَ إِلَّا تَبَارَۢا

“Ya Ubangijina, Ka gafarta min ni da mahaifana da kuma waxanda suka shiga gidana suna muminai, da kuma (sauran) muminai maza da mata, kada kuma Ka qari kafirai da komai sai hallaka.”