Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 1

ٱلۡحَآقَّةُ

Mai tabbata (watau alqiyama)



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 2

مَا ٱلۡحَآقَّةُ

Mece ce mai tabbata?



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 3

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡحَآقَّةُ

Me ya sanar da kai abin da ake kira mai tabbata?



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 4

كَذَّبَتۡ ثَمُودُ وَعَادُۢ بِٱلۡقَارِعَةِ

Samudawa da Adawa sun qaryata mai qwanqwasa (zukata da tsoro)



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 5

فَأَمَّا ثَمُودُ فَأُهۡلِكُواْ بِٱلطَّاغِيَةِ

To amma Samudawa sai aka halaka su da tsawa mai tsanani



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 6

وَأَمَّا عَادٞ فَأُهۡلِكُواْ بِرِيحٖ صَرۡصَرٍ عَاتِيَةٖ

Adawa kuma sai aka hallaka su da iska mai tsananin sanyi mai qarfi



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 7

سَخَّرَهَا عَلَيۡهِمۡ سَبۡعَ لَيَالٖ وَثَمَٰنِيَةَ أَيَّامٍ حُسُومٗاۖ فَتَرَى ٱلۡقَوۡمَ فِيهَا صَرۡعَىٰ كَأَنَّهُمۡ أَعۡجَازُ نَخۡلٍ خَاوِيَةٖ

Ya aiko musu da ita dare bakwai da wuni takwas a jere, sai ka riqa ganin mutane a cikinta matattu a yashe, kai ka ce rarakakkun kututturan dabinai ne (a zube)



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 8

فَهَلۡ تَرَىٰ لَهُم مِّنۢ بَاقِيَةٖ

To shin za ka iya ganin sauran vurvushinsu?



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 9

وَجَآءَ فِرۡعَوۡنُ وَمَن قَبۡلَهُۥ وَٱلۡمُؤۡتَفِكَٰتُ بِٱلۡخَاطِئَةِ

Fir’auna kuma da waxanda suke gabaninsa da (alqaryar) da aka kifar[1], sun zo da manyan laifuka


1- Watau alqaryun Annabi Lux () waxanda Allah () ya kifar da su saboda miyagun laifuffukansu.


Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 10

فَعَصَوۡاْ رَسُولَ رَبِّهِمۡ فَأَخَذَهُمۡ أَخۡذَةٗ رَّابِيَةً

Sai suka sava wa Manzon Ubangijinsu, sai Muka kama su kamawa mai qaruwa



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 11

إِنَّا لَمَّا طَغَا ٱلۡمَآءُ حَمَلۡنَٰكُمۡ فِي ٱلۡجَارِيَةِ

Mu lalle yayin da ruwa ya mamaye komai Mun xauke ku a cikin jirgin ruwa[1]


1- Watau ya xauki iyayensu waxanda suke cikin tsatsonsu a cikin jirgin ruwan Annabi Nuhu ().


Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 12

لِنَجۡعَلَهَا لَكُمۡ تَذۡكِرَةٗ وَتَعِيَهَآ أُذُنٞ وَٰعِيَةٞ

Don Mu sanya shi wa’azi a gare ku, kuma kunne mai kiyayewa ya kiyaye shi



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 13

فَإِذَا نُفِخَ فِي ٱلصُّورِ نَفۡخَةٞ وَٰحِدَةٞ

To idan aka busa qaho busa xaya



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 14

وَحُمِلَتِ ٱلۡأَرۡضُ وَٱلۡجِبَالُ فَدُكَّتَا دَكَّةٗ وَٰحِدَةٗ

Aka kuma xaga qasa da duwatsu sai aka dandaqe su dandaqewa baki xaya



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 15

فَيَوۡمَئِذٖ وَقَعَتِ ٱلۡوَاقِعَةُ

To a wannan rana ce mai afkuwa ta afku (watau alqiyama)



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 16

وَٱنشَقَّتِ ٱلسَّمَآءُ فَهِيَ يَوۡمَئِذٖ وَاهِيَةٞ

Sama kuma ta kekkece, don kuwa a wannan ranar ita mai rauni ce



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 17

وَٱلۡمَلَكُ عَلَىٰٓ أَرۡجَآئِهَاۚ وَيَحۡمِلُ عَرۡشَ رَبِّكَ فَوۡقَهُمۡ يَوۡمَئِذٖ ثَمَٰنِيَةٞ

Mala’iku kuma suna a sasanninta. A wannan ranar kuma (mala’iku) takwas za su xauki Al’arshin Ubangijinka a samansu



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 18

يَوۡمَئِذٖ تُعۡرَضُونَ لَا تَخۡفَىٰ مِنكُمۡ خَافِيَةٞ

A wannan ranar ne kuma za a bujuro da ku, ba wani abu naku mai vuya



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 19

فَأَمَّا مَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ فَيَقُولُ هَآؤُمُ ٱقۡرَءُواْ كِتَٰبِيَهۡ

To duk wanda aka bai wa littafinsa a hannunsa na dama zai ce: “Ku karvi littafina ku karanta



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 20

إِنِّي ظَنَنتُ أَنِّي مُلَٰقٍ حِسَابِيَهۡ

“Lalle ni na tabbata haka zan haxu da sakamakona.”



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 21

فَهُوَ فِي عِيشَةٖ رَّاضِيَةٖ

To shi zai zama cikin rayuwa abar yarda



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 22

فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٖ

Cikin Aljanna maxaukakiya



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 23

قُطُوفُهَا دَانِيَةٞ

‘Ya’yan itatuwanta dab da dab suke



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 24

كُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ هَنِيٓـَٔۢا بِمَآ أَسۡلَفۡتُمۡ فِي ٱلۡأَيَّامِ ٱلۡخَالِيَةِ

(A ce da su): “Ku ci ku sha kuna masu farin ciki saboda abin da kuka gabatar a kwanakinku da suka shuxe (na duniya).”



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 25

وَأَمَّا مَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ بِشِمَالِهِۦ فَيَقُولُ يَٰلَيۡتَنِي لَمۡ أُوتَ كِتَٰبِيَهۡ

Amma kuma wanda aka bai wa littafinsa a hannunsa na hagun sai ya ce: “Kaicona, ina ma da ba a ba ni littafina ba!



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 26

وَلَمۡ أَدۡرِ مَا حِسَابِيَهۡ

“Kuma ban san mene ne sakamakona ba



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 27

يَٰلَيۡتَهَا كَانَتِ ٱلۡقَاضِيَةَ

“Kaiconta (watau mutuwa), ina ma da ta zama ita ce qarshe!



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 28

مَآ أَغۡنَىٰ عَنِّي مَالِيَهۡۜ

“Dukiyata ba ta wadata min komai ba



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 29

هَلَكَ عَنِّي سُلۡطَٰنِيَهۡ

“Mulkina ya vace min da gani.”



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 30

خُذُوهُ فَغُلُّوهُ

(Sai a ce da mala’iku): Ku kama shi ku ququnce shi!