Surah: Suratut Taghabun

Ayah : 1

يُسَبِّحُ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۖ لَهُ ٱلۡمُلۡكُ وَلَهُ ٱلۡحَمۡدُۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

Abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa yana tasbihi ga Allah; mulki nasa ne kuma yabo ya tabbata a gare Shi; kuma Shi Mai iko ne a kan komai



Surah: Suratut Taghabun

Ayah : 2

هُوَ ٱلَّذِي خَلَقَكُمۡ فَمِنكُمۡ كَافِرٞ وَمِنكُم مُّؤۡمِنٞۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٌ

Shi ne Wanda Ya halicce ku, don haka daga cikinku akwai kafiri, daga cikinku kuma akwai mumini. Allah kuwa Mai ganin abin da kuke aikatawa ne



Surah: Suratut Taghabun

Ayah : 3

خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِٱلۡحَقِّ وَصَوَّرَكُمۡ فَأَحۡسَنَ صُوَرَكُمۡۖ وَإِلَيۡهِ ٱلۡمَصِيرُ

Ya halicci sammai da qasa da gaskiya, kuma Ya suranta ku, sannan Ya kyautata surorinku; zuwa gare Shi ne kuma makomarku take



Surah: Suratut Taghabun

Ayah : 4

يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَيَعۡلَمُ مَا تُسِرُّونَ وَمَا تُعۡلِنُونَۚ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ

Yana sane da abin da yake cikin sammai da qasa, kuma Yana sane da abin da kuke voyewa da abin da kuke bayyanawa. Allah kuma Masanin abubuwan da suke cikin zukata ne



Surah: Suratut Taghabun

Ayah : 5

أَلَمۡ يَأۡتِكُمۡ نَبَؤُاْ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن قَبۡلُ فَذَاقُواْ وَبَالَ أَمۡرِهِمۡ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Yanzu labarin waxanda suka kafirta gabaninku bai zo muku ba? Ai sun xanxani uqubar kafircinsu (a duniya), suna kuma da azaba mai raxaxi (a lahira)



Surah: Suratut Taghabun

Ayah : 6

ذَٰلِكَ بِأَنَّهُۥ كَانَت تَّأۡتِيهِمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَقَالُوٓاْ أَبَشَرٞ يَهۡدُونَنَا فَكَفَرُواْ وَتَوَلَّواْۖ وَّٱسۡتَغۡنَى ٱللَّهُۚ وَٱللَّهُ غَنِيٌّ حَمِيدٞ

Wannan kuwa saboda lalle manzanninsu sun kasance suna zuwa musu da ayoyi bayyanannu, sai suka ce: “Yanzu mutane ne za su shiryar da mu?” Saboda haka suka kafirce suka kuma ba da baya, Allah kuma Ya wadatu. Allah kuma Mawadaci ne Sha-yabo



Surah: Suratut Taghabun

Ayah : 7

زَعَمَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَن لَّن يُبۡعَثُواْۚ قُلۡ بَلَىٰ وَرَبِّي لَتُبۡعَثُنَّ ثُمَّ لَتُنَبَّؤُنَّ بِمَا عَمِلۡتُمۡۚ وَذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ

Waxanda suka kafirta sun riya cewa ba za a tashe su ba har abada. Ka ce: “A’a, na rantse da Ubangijina tabbas za a tashe ku, sannan kuma tabbas za a ba ku labarin abin da kuka aikata. Wannan kuwa mai sauqi ne a wurin Allah



Surah: Suratut Taghabun

Ayah : 8

فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَٱلنُّورِ ٱلَّذِيٓ أَنزَلۡنَاۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ

“To ku yi imani da Allah da Manzonsa da kuma hasken da Muka saukar (watau Alqur’ani). Allah kuma Masanin abin da kuke aikatawa ne



Surah: Suratut Taghabun

Ayah : 9

يَوۡمَ يَجۡمَعُكُمۡ لِيَوۡمِ ٱلۡجَمۡعِۖ ذَٰلِكَ يَوۡمُ ٱلتَّغَابُنِۗ وَمَن يُؤۡمِنۢ بِٱللَّهِ وَيَعۡمَلۡ صَٰلِحٗا يُكَفِّرۡ عَنۡهُ سَيِّـَٔاتِهِۦ وَيُدۡخِلۡهُ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۚ ذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ

“A ranar da zai tara ku a ranar taruwa; wannan kuwa ita ce ranar kamunga[1]. Duk kuwa wanda ya yi imani da Allah ya kuma yi aiki nagari zai kankare masa zunubansa, Ya kuma shigar da shi gidajen Aljanna (waxanda) qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har abada. Wannan shi ne babban rabo.”


1- Watau ranar da za su ga asara ta bayyana a gare su a fili, inda muminai za su gaje gidajen kafirai a Aljanna, su kuma kafirai su gaje gidajen ‘yan Aljanna a wuta.


Surah: Suratut Taghabun

Ayah : 10

وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَآ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِ خَٰلِدِينَ فِيهَاۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

Waxanda kuwa suka kafirce suka kuma qaryata ayoyinmu, waxannan su ne ‘yan wuta, suna masu dawwama a cikinta; makoma kuwa ta munana



Surah: Suratut Taghabun

Ayah : 11

مَآ أَصَابَ مِن مُّصِيبَةٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۗ وَمَن يُؤۡمِنۢ بِٱللَّهِ يَهۡدِ قَلۡبَهُۥۚ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ

Ba wata musiba da ta samu sai da izinin Allah. Duk kuwa wanda ya yi imani da Allah zai shiryi zuciyarsa. Allah kuma Masanin komai ne



Surah: Suratut Taghabun

Ayah : 12

وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَۚ فَإِن تَوَلَّيۡتُمۡ فَإِنَّمَا عَلَىٰ رَسُولِنَا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ

Ku bi Allah kuma ku bi Manzon. To idan kuka ba da baya to abin da yake kan Manzonmu kawai shi ne isar da aike



Surah: Suratut Taghabun

Ayah : 13

ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ

Allah, babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, to sai muminai su dogara ga Allah kawai



Surah: Suratut Taghabun

Ayah : 14

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّ مِنۡ أَزۡوَٰجِكُمۡ وَأَوۡلَٰدِكُمۡ عَدُوّٗا لَّكُمۡ فَٱحۡذَرُوهُمۡۚ وَإِن تَعۡفُواْ وَتَصۡفَحُواْ وَتَغۡفِرُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ

Ya ku waxanda suka yi imani, lalle wasu daga matanku da ‘ya’yanku maqiyanku ne[1], sai ku yi hattara da su. Idan kuma kuka yafe kuka kau da kai, to lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai


1- Watau waxanda suke qoqarin hana su xa’ar Allah ko su jefa su cikin savon Allah.


Surah: Suratut Taghabun

Ayah : 15

إِنَّمَآ أَمۡوَٰلُكُمۡ وَأَوۡلَٰدُكُمۡ فِتۡنَةٞۚ وَٱللَّهُ عِندَهُۥٓ أَجۡرٌ عَظِيمٞ

Dukiyoyinku da ‘ya’yanku fitina ne kawai (a gare ku). Kuma a wurin Allah lada mai girma yake



Surah: Suratut Taghabun

Ayah : 16

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ مَا ٱسۡتَطَعۡتُمۡ وَٱسۡمَعُواْ وَأَطِيعُواْ وَأَنفِقُواْ خَيۡرٗا لِّأَنفُسِكُمۡۗ وَمَن يُوقَ شُحَّ نَفۡسِهِۦ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ

Saboda haka ku kiyaye dokokin Allah gwargwadon ikonku, kuma ku yi sauraro, ku bi, ku kuma ciyar, shi ya fi alheri a gare ku. Duk kuwa wanda aka kare shi daga tsananin son kansa, to waxannan su ne masu babban rabo



Surah: Suratut Taghabun

Ayah : 17

إِن تُقۡرِضُواْ ٱللَّهَ قَرۡضًا حَسَنٗا يُضَٰعِفۡهُ لَكُمۡ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡۚ وَٱللَّهُ شَكُورٌ حَلِيمٌ

Idan kuka ranta wa Allah kyakkyawan rance, to zai ninninka muku shi[1], Ya kuma gafarta muku. Allah kuma Mai godewa ne, Mai haquri


1- Watau duk wani kyakkyawan aiki xaya zai ninka musu shi gida goma, har zuwa ninki xari bakwai, har zuwa ninkin ba ninkin mai yawa.


Surah: Suratut Taghabun

Ayah : 18

عَٰلِمُ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

Masanin voye da sarari ne, Mabuwayi, Mai hikima