Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 1

قَدۡ سَمِعَ ٱللَّهُ قَوۡلَ ٱلَّتِي تُجَٰدِلُكَ فِي زَوۡجِهَا وَتَشۡتَكِيٓ إِلَى ٱللَّهِ وَٱللَّهُ يَسۡمَعُ تَحَاوُرَكُمَآۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعُۢ بَصِيرٌ

Haqiqa Allah ya ji zancen wadda take muhawara da kai game da (lamarin) mijinta[1], tana kuma kai qara zuwa ga Allah, Allah kuma Yana jin muhawararku. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani


1- Ita ce Khaulatu ‘yar Sa’alaba (), mijinta kuwa shi ne Ausu xan Samit ().


Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 2

ٱلَّذِينَ يُظَٰهِرُونَ مِنكُم مِّن نِّسَآئِهِم مَّا هُنَّ أُمَّهَٰتِهِمۡۖ إِنۡ أُمَّهَٰتُهُمۡ إِلَّا ٱلَّـٰٓـِٔي وَلَدۡنَهُمۡۚ وَإِنَّهُمۡ لَيَقُولُونَ مُنكَرٗا مِّنَ ٱلۡقَوۡلِ وَزُورٗاۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَعَفُوٌّ غَفُورٞ

Waxanda suke yin zihari[1] daga cikinku ga matansu, su ba iyayensu mata ba ne; iyayensu mata su ne waxanda kawai suka haife su. Lalle kuma su tabbas suna faxar muguwar magana ne da tsagwaron qarya. Kuma lalle Allah tabbas Mai afuwa ne, Mai gafara


1- Shi ne miji ya kwatanta matarsa da mahaifiyarsa ya ce: “Ke a wurina kamar bayan mahaifiyata ne”. A zamanin jahiliyya idan miji ya faxa wa matarsa haka, to ta haramta a gare shi har abada.


Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 3

وَٱلَّذِينَ يُظَٰهِرُونَ مِن نِّسَآئِهِمۡ ثُمَّ يَعُودُونَ لِمَا قَالُواْ فَتَحۡرِيرُ رَقَبَةٖ مِّن قَبۡلِ أَن يَتَمَآسَّاۚ ذَٰلِكُمۡ تُوعَظُونَ بِهِۦۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ

Waxanda kuwa suke yin zihari ga matansu sannan suka yi niyyar janye abin da suka faxa, to sai su ‘yanta wuyaye (bawa namiji ko mace), tun kafin su sadu. Wannan (shi ne abin da) ake yi muku wa’azi da shi. Allah kuma Masanin abin da kuke aikatawa ne



Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 4

فَمَن لَّمۡ يَجِدۡ فَصِيَامُ شَهۡرَيۡنِ مُتَتَابِعَيۡنِ مِن قَبۡلِ أَن يَتَمَآسَّاۖ فَمَن لَّمۡ يَسۡتَطِعۡ فَإِطۡعَامُ سِتِّينَ مِسۡكِينٗاۚ ذَٰلِكَ لِتُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦۚ وَتِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِۗ وَلِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٌ أَلِيمٌ

Sannan wanda bai samu ba, to sai ya yi azumin wata biyu a jere tun kafin su sadu; sannan wanda bai sami iko ba sai ya ciyar da miskini sittin. Wannan kuwa don ku yi imani da Allah da Manzonsa. Waxannan kuma su ne iyakokin Allah. Kafirai kuma suna da azaba mai raxaxi



Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 5

إِنَّ ٱلَّذِينَ يُحَآدُّونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ كُبِتُواْ كَمَا كُبِتَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ وَقَدۡ أَنزَلۡنَآ ءَايَٰتِۭ بَيِّنَٰتٖۚ وَلِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٞ مُّهِينٞ

Lalle waxanda suke sava wa Allah da Manzonsa an qasqantar da su kamar yadda aka qasqantar da waxanda suke gabaninsu. Kuma haqiqa Mun saukar da ayoyi bayyanannu. Kafirai kuma suna da azaba mai wulaqantarwa



Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 6

يَوۡمَ يَبۡعَثُهُمُ ٱللَّهُ جَمِيعٗا فَيُنَبِّئُهُم بِمَا عَمِلُوٓاْۚ أَحۡصَىٰهُ ٱللَّهُ وَنَسُوهُۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٌ

A ranar da Allah zai tashe su gaba xaya, sannan Ya ba su labarin abin da suka aikata. Allah Ya qididdige shi, su kuwa sun manta shi. Allah kuwa Mai ganin kowane abu ne



Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 7

أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۖ مَا يَكُونُ مِن نَّجۡوَىٰ ثَلَٰثَةٍ إِلَّا هُوَ رَابِعُهُمۡ وَلَا خَمۡسَةٍ إِلَّا هُوَ سَادِسُهُمۡ وَلَآ أَدۡنَىٰ مِن ذَٰلِكَ وَلَآ أَكۡثَرَ إِلَّا هُوَ مَعَهُمۡ أَيۡنَ مَا كَانُواْۖ ثُمَّ يُنَبِّئُهُم بِمَا عَمِلُواْ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٌ

Shin ba ka sani ba ne cewa Allah Ya san abin da yake cikin sammai da abi da yake cikin qasa? Babu wata ganawa tsakanin mutum uku da za ta faru sai Shi ne na huxunsu[1], da kuma (tsakanin mutum) biyar sai Shi ne na shidansu, da kuma abin da ya kasa (haka) ko ya fi, sai Shi (Allah) Yana tare da su a duk inda suke[2]; sannan Ya ba su labarin abin da suka aikata a ranar alqiyama. Lalle Allah Masanin komai ne


1- Watau da iliminsa.


2- Watau yana tare da su da saninsa da ganinsa.


Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 8

أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ نُهُواْ عَنِ ٱلنَّجۡوَىٰ ثُمَّ يَعُودُونَ لِمَا نُهُواْ عَنۡهُ وَيَتَنَٰجَوۡنَ بِٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَٰنِ وَمَعۡصِيَتِ ٱلرَّسُولِۖ وَإِذَا جَآءُوكَ حَيَّوۡكَ بِمَا لَمۡ يُحَيِّكَ بِهِ ٱللَّهُ وَيَقُولُونَ فِيٓ أَنفُسِهِمۡ لَوۡلَا يُعَذِّبُنَا ٱللَّهُ بِمَا نَقُولُۚ حَسۡبُهُمۡ جَهَنَّمُ يَصۡلَوۡنَهَاۖ فَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

Shin ba ka ga waxanda aka hana su ganawa ba, sannan suke koma wa abin da aka hane su yinsa, suke kuma ganawa a kan savo da ta’addanci, da kuma sava wa Manzo? Idan kuma suka zo wurinka sai su gaishe ka da lafazin da Allah bai gaishe ka da shi ba[1], su riqa cewa a ransu: “Me ya hana Allah Ya azabtar da mu saboda abin da muka faxa?” Jahannama ta ishe su, za su shige ta; saboda haka makoma ta munana


1- Watau suna ce masa: Assamu alaika, ma’ana mutuwa ta tabbata a kanka.


Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 9

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا تَنَٰجَيۡتُمۡ فَلَا تَتَنَٰجَوۡاْ بِٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَٰنِ وَمَعۡصِيَتِ ٱلرَّسُولِ وَتَنَٰجَوۡاْ بِٱلۡبِرِّ وَٱلتَّقۡوَىٰۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ ٱلَّذِيٓ إِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, idan za ku gana to kada ku yi ganawar savo da ta’addanci da kuma sava wa Manzo. (A maimakon haka) ku gana a kan ayyukan alheri da taqawa; kuma ku kiyaye dokokin Allah wanda zuwa gare Shi ne za a tattaro ku



Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 10

إِنَّمَا ٱلنَّجۡوَىٰ مِنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ لِيَحۡزُنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَلَيۡسَ بِضَآرِّهِمۡ شَيۡـًٔا إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ

Ganawar (tasu) kawai daga Shaixan take, don ya baqanta ran waxanda suka yi imani, ba kuwa zai cuce su da komai ba sai da izinin Allah. Ga Allah ne kuma muminai za su dogara



Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 11

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا قِيلَ لَكُمۡ تَفَسَّحُواْ فِي ٱلۡمَجَٰلِسِ فَٱفۡسَحُواْ يَفۡسَحِ ٱللَّهُ لَكُمۡۖ وَإِذَا قِيلَ ٱنشُزُواْ فَٱنشُزُواْ يَرۡفَعِ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنكُمۡ وَٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ دَرَجَٰتٖۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, idan aka ce da ku: “Ku yalwata a wuraren zama,” to sai ku yalwata, Allah zai yalwata muku[1]; idan kuma aka ce: “Ku tashi (daga wurinku)[2],” to sai ku tashi, Allah zai xaga darajojin waxanda suka yi imani daga cikinku da waxanda aka bai wa ilimi. Allah kuma Masanin abin da kuke aikatawa ne


1- Watau zai buxa musu a rayuwarsu ta duniya da ta lahira.


2- Watau domin wani aiki na addini ko wata buqata da ta taso.


Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 12

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا نَٰجَيۡتُمُ ٱلرَّسُولَ فَقَدِّمُواْ بَيۡنَ يَدَيۡ نَجۡوَىٰكُمۡ صَدَقَةٗۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ لَّكُمۡ وَأَطۡهَرُۚ فَإِن لَّمۡ تَجِدُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ

Ya ku waxanda suka yi imani, idan za ku gana da Manzo, to sai ku gabatar da wata sadaka kafin ganawar taku. Wannan shi ya fi muku alheri da tsarkaka. Sannan idan ba ku samu ba, to lalle Allah Mai gafara ne, Mai rahama



Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 13

ءَأَشۡفَقۡتُمۡ أَن تُقَدِّمُواْ بَيۡنَ يَدَيۡ نَجۡوَىٰكُمۡ صَدَقَٰتٖۚ فَإِذۡ لَمۡ تَفۡعَلُواْ وَتَابَ ٱللَّهُ عَلَيۡكُمۡ فَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥۚ وَٱللَّهُ خَبِيرُۢ بِمَا تَعۡمَلُونَ

Yanzu kun samu damuwa ne ta gabatar da sadaka kafin ganawarku? To idan ba ku aikata haka ba Allah kuma ya karvi tubarku, to sai ku tsayar da salla, ku ba da zakka, ku kuma bi Allah da Manzonsa. Allah kuma Masanin abin da kuke aikatawa ne



Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 14

۞أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ تَوَلَّوۡاْ قَوۡمًا غَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مَّا هُم مِّنكُمۡ وَلَا مِنۡهُمۡ وَيَحۡلِفُونَ عَلَى ٱلۡكَذِبِ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ

Shin ba ka ga waxanda suka yi abota da wasu mutane da Allah Ya yi fushi da su[1] ba, su ba cikinku suke ba, ba kuma cikinsu suke ba; su kuma riqa rantsuwa a kan qarya, alhali kuwa su suna sane (da yin ta)?


1- Su ne Yahudawa waxanda munafukai suke abota da su.


Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 15

أَعَدَّ ٱللَّهُ لَهُمۡ عَذَابٗا شَدِيدًاۖ إِنَّهُمۡ سَآءَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Allah Ya tanadar musu azaba mai tsanani, lalle su abin da suke aikatawa ya munana



Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 16

ٱتَّخَذُوٓاْ أَيۡمَٰنَهُمۡ جُنَّةٗ فَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ فَلَهُمۡ عَذَابٞ مُّهِينٞ

Sun xauki rantse-rantsensu su zama garkuwa, sai suka kange hanyar Allah, saboda haka suna da (sakamakon) azaba mai wulaqantarwa



Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 17

لَّن تُغۡنِيَ عَنۡهُمۡ أَمۡوَٰلُهُمۡ وَلَآ أَوۡلَٰدُهُم مِّنَ ٱللَّهِ شَيۡـًٔاۚ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Dukiyoyinsu da ‘ya’yansu ba za su amfanar musu komai ba a wurin Allah. Waxannan su ne ‘yan wuta; su madawwama ne a cikinta



Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 18

يَوۡمَ يَبۡعَثُهُمُ ٱللَّهُ جَمِيعٗا فَيَحۡلِفُونَ لَهُۥ كَمَا يَحۡلِفُونَ لَكُمۡ وَيَحۡسَبُونَ أَنَّهُمۡ عَلَىٰ شَيۡءٍۚ أَلَآ إِنَّهُمۡ هُمُ ٱلۡكَٰذِبُونَ

A ranar da Allah zai tashe su baki xaya sai su rantse Masa kamar yadda suke rantse muku, su kuma riqa tsammanin su sun yi wani abu (mai amfani). Ku saurara, lalle kam su ne maqaryata



Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 19

ٱسۡتَحۡوَذَ عَلَيۡهِمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ فَأَنسَىٰهُمۡ ذِكۡرَ ٱللَّهِۚ أُوْلَـٰٓئِكَ حِزۡبُ ٱلشَّيۡطَٰنِۚ أَلَآ إِنَّ حِزۡبَ ٱلشَّيۡطَٰنِ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ

Shaixan ya ci qarfinsu, sai ya mantar da su ambaton Allah. Waxannan su ne qungiyar Shaixan. Ku saurara, lalle qungiyar Shaixan su ne tavavvu



Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 20

إِنَّ ٱلَّذِينَ يُحَآدُّونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓ أُوْلَـٰٓئِكَ فِي ٱلۡأَذَلِّينَ

Lalle waxanda suke sava wa Allah da Manzonsa waxannan suna cikin mafiya qasqanci



Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 21

كَتَبَ ٱللَّهُ لَأَغۡلِبَنَّ أَنَا۠ وَرُسُلِيٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ قَوِيٌّ عَزِيزٞ

Allah Ya rubuta cewa: Lalle Ni da manzannina ne za mu yi galaba. Lalle Allah Mai qarfi ne, Mabuwayi



Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 22

لَّا تَجِدُ قَوۡمٗا يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ يُوَآدُّونَ مَنۡ حَآدَّ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَلَوۡ كَانُوٓاْ ءَابَآءَهُمۡ أَوۡ أَبۡنَآءَهُمۡ أَوۡ إِخۡوَٰنَهُمۡ أَوۡ عَشِيرَتَهُمۡۚ أُوْلَـٰٓئِكَ كَتَبَ فِي قُلُوبِهِمُ ٱلۡإِيمَٰنَ وَأَيَّدَهُم بِرُوحٖ مِّنۡهُۖ وَيُدۡخِلُهُمۡ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ رَضِيَ ٱللَّهُ عَنۡهُمۡ وَرَضُواْ عَنۡهُۚ أُوْلَـٰٓئِكَ حِزۡبُ ٱللَّهِۚ أَلَآ إِنَّ حِزۡبَ ٱللَّهِ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ

Ba za ka tava samun wasu mutane da suke yin imani da Allah da ranar lahira ba, su riqa qaunar waxanda suke gaba da Allah da Manzonsa, ko da kuwa sun kasance iyayensu ne ko ‘ya’yansu ko ‘yan’uwansu ko kuma danginsu. Waxannan Allah Ya rubuta imani a cikin zukatansu, Ya kuma qarfafe su da wani ruhi daga wurinsa[1]; zai kuma shigar da su gidajen Aljanna (waxanda) qoramu suke gudana ta qarqashinsu, madawwama a cikinsu. Allah Ya yarda da su, su ma sun yarda da Shi. Waxannan ne qungiyar Allah. Ku saurara, lalle qungiyar Allah su ne masu samun babban rabo


1- Watau zai qarfafe su da wata hujja daga wurinsa da haske.