حمٓ
HA MIM[1]
1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.
وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ
Na rantse da Littafi mabayyani (Alqur’ani)
إِنَّا جَعَلۡنَٰهُ قُرۡءَٰنًا عَرَبِيّٗا لَّعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ
Lalle Mu Mun sanya shi ya zamo abin karantawa cikin harshen Larabci domin ku hankalta
وَإِنَّهُۥ فِيٓ أُمِّ ٱلۡكِتَٰبِ لَدَيۡنَا لَعَلِيٌّ حَكِيمٌ
Lalle kuma shi (Alqur’ani) a cikin Littafi Lauhul-Mahafuzu a wurinmu tabbas maxaukaki ne, mai hikima
أَفَنَضۡرِبُ عَنكُمُ ٱلذِّكۡرَ صَفۡحًا أَن كُنتُمۡ قَوۡمٗا مُّسۡرِفِينَ
Yanzu Ma fasa saukar muku da Alqur’ani Mu watsar da ku, don kun kasance mutane masu yawan varna?
وَكَمۡ أَرۡسَلۡنَا مِن نَّبِيّٖ فِي ٱلۡأَوَّلِينَ
Annabi nawa Muka aika wa mutanen farko
وَمَا يَأۡتِيهِم مِّن نَّبِيٍّ إِلَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ
Ba kuma wani annabi da yakan zo musu sai sun kasance suna yi masa izgili
فَأَهۡلَكۡنَآ أَشَدَّ مِنۡهُم بَطۡشٗا وَمَضَىٰ مَثَلُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Sai Muka hallakar da waxanda suka fi su tsananin qarfi[1], kuma bayanin yadda aka hallakar da mutanen farko ya riga ya shuxe
1- Watau kamar qabilun Adawa da Samudawa da mutanen Annabi Luxu ().
وَلَئِن سَأَلۡتَهُم مَّنۡ خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ لَيَقُولُنَّ خَلَقَهُنَّ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡعَلِيمُ
Lalle kuma idan ka tambaye su wane ne ya halicci sammai da qasa, to tabbas za su ce: “(Allah) ne Mabuwayi, Masani Ya halicce su.”
ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ مَهۡدٗا وَجَعَلَ لَكُمۡ فِيهَا سُبُلٗا لَّعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ
Wanda Ya sanya muku qasa ta zama shimfixa, Ya kuma sanya muku hanyoyi a cikinta don ku gane (inda za ku dosa)
وَٱلَّذِي نَزَّلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءَۢ بِقَدَرٖ فَأَنشَرۡنَا بِهِۦ بَلۡدَةٗ مَّيۡتٗاۚ كَذَٰلِكَ تُخۡرَجُونَ
Wanda kuma Ya saukar da ruwa daidai gwargwado daga sama sannan Muka raya mataccen gari da shi. Kamar haka ne za a fito da ku (daga qabarurruka)
وَٱلَّذِي خَلَقَ ٱلۡأَزۡوَٰجَ كُلَّهَا وَجَعَلَ لَكُم مِّنَ ٱلۡفُلۡكِ وَٱلۡأَنۡعَٰمِ مَا تَرۡكَبُونَ
Kuma wanda Ya halicci dukkan dangogin abubuwa bibbiyu, Ya kuma sanya muku daga jiragen ruwa da kuma dabbobin ni’ima, abubuwan da kuke hawa
لِتَسۡتَوُۥاْ عَلَىٰ ظُهُورِهِۦ ثُمَّ تَذۡكُرُواْ نِعۡمَةَ رَبِّكُمۡ إِذَا ٱسۡتَوَيۡتُمۡ عَلَيۡهِ وَتَقُولُواْ سُبۡحَٰنَ ٱلَّذِي سَخَّرَ لَنَا هَٰذَا وَمَا كُنَّا لَهُۥ مُقۡرِنِينَ
Don ku daidaita a kan bayansu, sannan ku tuna ni’imar Ubangijinku lokacin da kuka daidaita a kansu kuma ku ce: “Tsarki ya tabbata ga wanda Ya hore mana wannan, ba mu zamanto masu ikon sarrafa shi ba
وَإِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا لَمُنقَلِبُونَ
“Kuma lalle zuwa ga Ubangijinmu tabbas za mu koma.”
وَجَعَلُواْ لَهُۥ مِنۡ عِبَادِهِۦ جُزۡءًاۚ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَكَفُورٞ مُّبِينٌ
Kuma suka mai da wasu daga cikin bayinsa wani vangare nasa (wato `ya`yansa). Lalle mutum mai yawan butulci ne mai bayyana (butulcinsa)
أَمِ ٱتَّخَذَ مِمَّا يَخۡلُقُ بَنَاتٖ وَأَصۡفَىٰكُم بِٱلۡبَنِينَ
Yanzu Ya xauki `ya`ya mata daga abubuwan da Yake halitta, ku kuma Ya zava muku `ya`ya maza?
وَإِذَا بُشِّرَ أَحَدُهُم بِمَا ضَرَبَ لِلرَّحۡمَٰنِ مَثَلٗا ظَلَّ وَجۡهُهُۥ مُسۡوَدّٗا وَهُوَ كَظِيمٌ
Idan kuma aka yi wa xayansu albishir da abin da ya buga misali cewa na (Allah) Arrahmanu ne, sai fuskarsa ta yini a murtuke yana cike da baqin ciki
أَوَمَن يُنَشَّؤُاْ فِي ٱلۡحِلۡيَةِ وَهُوَ فِي ٱلۡخِصَامِ غَيۡرُ مُبِينٖ
Yanzu (sa danganta wa Allah) wanda da ake renon sa cikin kwalliya, alhali kuma idan an zo wajen husuma ba zai iya bayyana kansa (wajan ba da hujja) ba?
وَجَعَلُواْ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ ٱلَّذِينَ هُمۡ عِبَٰدُ ٱلرَّحۡمَٰنِ إِنَٰثًاۚ أَشَهِدُواْ خَلۡقَهُمۡۚ سَتُكۡتَبُ شَهَٰدَتُهُمۡ وَيُسۡـَٔلُونَ
Suka kuma mai da mala’iku waxanda suke bayin (Allah) Arrahmanu ne `ya`ya mata. Shin sun halarci sanda aka halicce su ne? To za a rubuta shaidarsu, za kuma a tambaye su (a lahira)
وَقَالُواْ لَوۡ شَآءَ ٱلرَّحۡمَٰنُ مَا عَبَدۡنَٰهُمۗ مَّا لَهُم بِذَٰلِكَ مِنۡ عِلۡمٍۖ إِنۡ هُمۡ إِلَّا يَخۡرُصُونَ
Suka kuma ce: “Da (Allah) Arrahmanu Ya ga dama, da ba mu bauta musu ba (wato mala’ikun).” Ba su da wani takamaiman ilimi a kan hakan; ba abin da suke yi sai shaci-faxi
أَمۡ ءَاتَيۡنَٰهُمۡ كِتَٰبٗا مِّن قَبۡلِهِۦ فَهُم بِهِۦ مُسۡتَمۡسِكُونَ
Ko kuma Mun ba su wani littafi ne gabaninsa (Alqur’ani), saboda haka suke riqe da shi qam-qam?
بَلۡ قَالُوٓاْ إِنَّا وَجَدۡنَآ ءَابَآءَنَا عَلَىٰٓ أُمَّةٖ وَإِنَّا عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِم مُّهۡتَدُونَ
A’a, cewa dai suka yi: “Lalle mu mun sami iyayenmu a kan wani addini ne, mu kuma lalle sawunsu muke bi.”
وَكَذَٰلِكَ مَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ فِي قَرۡيَةٖ مِّن نَّذِيرٍ إِلَّا قَالَ مُتۡرَفُوهَآ إِنَّا وَجَدۡنَآ ءَابَآءَنَا عَلَىٰٓ أُمَّةٖ وَإِنَّا عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِم مُّقۡتَدُونَ
Kuma kamar haka ne, ba Mu tava aiko wani mai gargaxi ba a wata alqarya a gabaninka sai ‘yan ta-moren cikinsu sun ce: “Lalle mu mun sami iyayenmu a kan wani addini, kuma lalle mu hanyarsu muke kwaikwayo.”
۞قَٰلَ أَوَلَوۡ جِئۡتُكُم بِأَهۡدَىٰ مِمَّا وَجَدتُّمۡ عَلَيۡهِ ءَابَآءَكُمۡۖ قَالُوٓاْ إِنَّا بِمَآ أُرۡسِلۡتُم بِهِۦ كَٰفِرُونَ
Ya ce (da su: “Yanzu za ku yi koyi da su) ko da na zo muku da abin da ya fi zama shiriya a kan abin da kuka sami iyayenku a kansa?” Suka ce: “Lalle mu masu kafirce wa abin da aka aiko ku da shi ne.”
فَٱنتَقَمۡنَا مِنۡهُمۡۖ فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُكَذِّبِينَ
Sai Muka saka musu da azaba; to duba ka ga yadda qarshen masu qaryatawa ya kasance
وَإِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِيمُ لِأَبِيهِ وَقَوۡمِهِۦٓ إِنَّنِي بَرَآءٞ مِّمَّا تَعۡبُدُونَ
Kuma ka tuna lokacin da Ibrahimu ya ce da Babansa da mutanensa: “Lalle ni ba ruwana da abin da kuke bautawa
إِلَّا ٱلَّذِي فَطَرَنِي فَإِنَّهُۥ سَيَهۡدِينِ
“Sai dai wanda Ya halicce ni, to lalle Shi ne Zai shirye ni.”
وَجَعَلَهَا كَلِمَةَۢ بَاقِيَةٗ فِي عَقِبِهِۦ لَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ
Ya kuma sanya ta (kalmar Tauhidi ta zama) kalma ce mai wanzuwa a cikin zuri’arsa don (mutanen Makka) su komo (kan hanya).”
بَلۡ مَتَّعۡتُ هَـٰٓؤُلَآءِ وَءَابَآءَهُمۡ حَتَّىٰ جَآءَهُمُ ٱلۡحَقُّ وَرَسُولٞ مُّبِينٞ
A’a, Na jiyar da waxannan daxi tare da iyayensu ne har gaskiya ta zo musu da wani manzo mai bayyanawa
وَلَمَّا جَآءَهُمُ ٱلۡحَقُّ قَالُواْ هَٰذَا سِحۡرٞ وَإِنَّا بِهِۦ كَٰفِرُونَ
Yayin da gaskiyar ta zo musu sai suka ce: “Wannan sihiri ne, kuma lalle mu masu kafirce masa ne.”