الٓمٓ
ALIF LAM MIM[1]
1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.
غُلِبَتِ ٱلرُّومُ
An yi galaba a kan Rumawa[1]
1- Watau Farisawa masu bautar wuta sun yi galaba a kan Rumawa masu bin addinin Annabi Isa () a wani yaqi da ya varke tsakaninsu.
فِيٓ أَدۡنَى ٱلۡأَرۡضِ وَهُم مِّنۢ بَعۡدِ غَلَبِهِمۡ سَيَغۡلِبُونَ
A qasa mafi kusa (da su), su kuma da sannu za su yi galaba (a kan Farisa) bayan galabar da aka yi a kansu
فِي بِضۡعِ سِنِينَۗ لِلَّهِ ٱلۡأَمۡرُ مِن قَبۡلُ وَمِنۢ بَعۡدُۚ وَيَوۡمَئِذٖ يَفۡرَحُ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ
A cikin ‘yan tsirarun shekarun (da ba su kai goma ba). Al’amari a da can da nan gaba na Allah ne. A wannan ranar ne muminai za su yi farin ciki
بِنَصۡرِ ٱللَّهِۚ يَنصُرُ مَن يَشَآءُۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Da samun nasar Allah (a kan Farisa). Shi Yake taimakon wanda Ya ga dama; domin kuwa Shi ne Mabuwayi, Mai rahama
وَعۡدَ ٱللَّهِۖ لَا يُخۡلِفُ ٱللَّهُ وَعۡدَهُۥ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ
(Wannan ya kasance) alqawarin Allah ne; Allah ba Ya sava alqawarinsa, sai dai kuma yawancin mutane ba su san (haka) ba
يَعۡلَمُونَ ظَٰهِرٗا مِّنَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَهُمۡ عَنِ ٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ غَٰفِلُونَ
Suna sanin abin da yake a sarari na rayuwar duniya ne, alhali kuwa su gafalallu ne game da lahira
أَوَلَمۡ يَتَفَكَّرُواْ فِيٓ أَنفُسِهِمۗ مَّا خَلَقَ ٱللَّهُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَآ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَأَجَلٖ مُّسَمّٗىۗ وَإِنَّ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلنَّاسِ بِلِقَآيِٕ رَبِّهِمۡ لَكَٰفِرُونَ
Yanzu ba su yi tunani a kan kansu ba? Allah bai halicci sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu ba sai da gaskiya kuma (ya yi su zuwa) lokaci qayyadajje. Lalle mafi yawan mutane masu kafircewa ne da haxuwa da Ubangijinsu
أَوَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَانُوٓاْ أَشَدَّ مِنۡهُمۡ قُوَّةٗ وَأَثَارُواْ ٱلۡأَرۡضَ وَعَمَرُوهَآ أَكۡثَرَ مِمَّا عَمَرُوهَا وَجَآءَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِۖ فَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيَظۡلِمَهُمۡ وَلَٰكِن كَانُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ
Shin ba za su yi tafiya a bayan qasa ba su ga yadda qarshen waxanda suka gabace su ya zama? Sun kasance sun fi su tsananin qarfi, sun kuma tona qasa suka kuma raya ta fiye da yadda su (mutanen Makka) suka raya ta, kuma manzanninsu sun zo musu da (ayoyi) bayyanannu; to Allah bai kasance Mai zaluntar su ba, sai dai su ne suka kasance suna zaluntar kawunansu
ثُمَّ كَانَ عَٰقِبَةَ ٱلَّذِينَ أَسَـٰٓـُٔواْ ٱلسُّوٓأَىٰٓ أَن كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَكَانُواْ بِهَا يَسۡتَهۡزِءُونَ
Sannan kuma qarshen waxanda suka munana (ayyukansu) ya kasance mummunan (sakamako), don sun qaryata ayoyin Allah, kuma sun kasance suna yin izgili gare su
ٱللَّهُ يَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ ثُمَّ إِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
Allah ne Yake farar halitta sannan Ya dawo da ita (bayan mutuwa), sannan kuma gare Shi za a komar da ku
وَيَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يُبۡلِسُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ
Kuma ranar da alqiyama za ta tashi, a wannan ranar ne masu manyan laifuka (kafirai) za su yanke qauna daga rahama
وَلَمۡ يَكُن لَّهُم مِّن شُرَكَآئِهِمۡ شُفَعَـٰٓؤُاْ وَكَانُواْ بِشُرَكَآئِهِمۡ كَٰفِرِينَ
Daga abokan tarayyar tasu kuwa ba su da wasu masu ceton su, za su ma kasance masu kafirce wa abokan tarayyar tasu
وَيَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يَوۡمَئِذٖ يَتَفَرَّقُونَ
Kuma ranar da alqiyama za ta tashi, a wannan ranar ne (mutane) za su rarrabu[1]
1- Watau qungiya biyu, qungiyar muminai masu shiga Aljanna da ta kafirai masu shiga wuta.
فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ فَهُمۡ فِي رَوۡضَةٖ يُحۡبَرُونَ
To amma waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari, to su kam suna cikin dausayin (Aljanna) ana faranta musu rai
وَأَمَّا ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَلِقَآيِٕ ٱلۡأٓخِرَةِ فَأُوْلَـٰٓئِكَ فِي ٱلۡعَذَابِ مُحۡضَرُونَ
Amma kuma waxanda suka kafirta suka kuma qaryata ayoyinmu da haxuwa da ranar lahira, to waxannan za a halartar da su cikin azaba
فَسُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ حِينَ تُمۡسُونَ وَحِينَ تُصۡبِحُونَ
To tsarki ya tabbata ga Allah yayin kuka shiga lokacin maraice, da kuma yayin da kuka wayi gari
وَلَهُ ٱلۡحَمۡدُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَعَشِيّٗا وَحِينَ تُظۡهِرُونَ
Yabo kuma nasa ne a cikin sammai da qasa, da kuma yayin da kuka yi yammaci da kuma shigowarku lokacin azahar
يُخۡرِجُ ٱلۡحَيَّ مِنَ ٱلۡمَيِّتِ وَيُخۡرِجُ ٱلۡمَيِّتَ مِنَ ٱلۡحَيِّ وَيُحۡيِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَاۚ وَكَذَٰلِكَ تُخۡرَجُونَ
Yana fitar da rayayye daga matacce, Yana kuma fitar da matacce daga rayayye, kuma Yana raya qasa bayan mutuwarta. Kamar haka ne kuma za a fito da ku (daga qaburburanku)
وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَنۡ خَلَقَكُم مِّن تُرَابٖ ثُمَّ إِذَآ أَنتُم بَشَرٞ تَنتَشِرُونَ
Yana daga ayoyinsa cewa Ya halicce ku daga turvaya, sannan kuma sai ga ku mutane kun warwatsu (a ko’ina)
وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَنۡ خَلَقَ لَكُم مِّنۡ أَنفُسِكُمۡ أَزۡوَٰجٗا لِّتَسۡكُنُوٓاْ إِلَيۡهَا وَجَعَلَ بَيۡنَكُم مَّوَدَّةٗ وَرَحۡمَةًۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ
Yana kuma daga ayoyinsa cewa Ya halitta muku mata daga jinsinku don ku samu nutsuwa gare su, Ya kuma sanya soyayya da jin qai tsakaninku. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutane masu tunani
وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦ خَلۡقُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَٱخۡتِلَٰفُ أَلۡسِنَتِكُمۡ وَأَلۡوَٰنِكُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّلۡعَٰلِمِينَ
Yana kuma daga cikin ayoyinsa halittar sammai da qasa da kuma sassavawar harsunanku da launukanku. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga ma’abota ilimi
وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦ مَنَامُكُم بِٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ وَٱبۡتِغَآؤُكُم مِّن فَضۡلِهِۦٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَسۡمَعُونَ
Yana kuma daga cikin ayoyinsa barcinku da daddare da kuma rana da neman falalarsa da kuke yi. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga masu ji (na lura)
وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦ يُرِيكُمُ ٱلۡبَرۡقَ خَوۡفٗا وَطَمَعٗا وَيُنَزِّلُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَيُحۡيِۦ بِهِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَآۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ
Yana kuma daga cikin ayoyinsa nuna muku walqiya da Yake yi don tsoratarwa da kwaxaitarwa, Ya kuma saukar da ruwa daga sama, sai Ya raya qasa da shi bayan mutuwarta. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutane da suke hankalta
وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَن تَقُومَ ٱلسَّمَآءُ وَٱلۡأَرۡضُ بِأَمۡرِهِۦۚ ثُمَّ إِذَا دَعَاكُمۡ دَعۡوَةٗ مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ إِذَآ أَنتُمۡ تَخۡرُجُونَ
Yana kuma daga cikin ayoyinsa sama da qasa su tsaya da umarninsa. Sannan kuma yayin da Ya kira ku (don ku tashi) daga qasa sai ga ku kuna fitowa
وَلَهُۥ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ كُلّٞ لَّهُۥ قَٰنِتُونَ
Kuma duk waxanda suke cikin sammai da qasa nasa ne; dukkaninsu masu biyayya ne gare Shi
وَهُوَ ٱلَّذِي يَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ وَهُوَ أَهۡوَنُ عَلَيۡهِۚ وَلَهُ ٱلۡمَثَلُ ٱلۡأَعۡلَىٰ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Shi ne wanda Yake farar halittu, sannan Ya dawo da su (bayan mutuwa. Yin haka) kuwa shi ya fi sauqi a gare Shi. Kuma siffofi mafiya xaukaka sun tabbata gare Shi a cikin sammai da qasa, kuma Shi ne Mabuwayi, Mai hikima
ضَرَبَ لَكُم مَّثَلٗا مِّنۡ أَنفُسِكُمۡۖ هَل لَّكُم مِّن مَّا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُم مِّن شُرَكَآءَ فِي مَا رَزَقۡنَٰكُمۡ فَأَنتُمۡ فِيهِ سَوَآءٞ تَخَافُونَهُمۡ كَخِيفَتِكُمۡ أَنفُسَكُمۡۚ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ
Ya ba ku misali daga kawunanku; shin kuna da wasu abokan tarayya daga bayinku da kuka mallaka a kan abin da Muka arzuta ku (da shi), ku da su ku zama daidai kuke game da wannan; kuna ma jin tsoron su kamar yanda kuke tsoron junanku? Kamar haka Muke rarrabe ayoyin (filla-filla) ga mutanen da suke hankalta
بَلِ ٱتَّبَعَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ أَهۡوَآءَهُم بِغَيۡرِ عِلۡمٖۖ فَمَن يَهۡدِي مَنۡ أَضَلَّ ٱللَّهُۖ وَمَا لَهُم مِّن نَّـٰصِرِينَ
Ba haka ba ne, waxanda suka yi zalunci dai sun bi son ransu ne ba tare da wani ilimi ba; to wane ne zai shiryar da wanda Allah Ya vatar? Kuma ba su da wasu mataimaka
فَأَقِمۡ وَجۡهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفٗاۚ فِطۡرَتَ ٱللَّهِ ٱلَّتِي فَطَرَ ٱلنَّاسَ عَلَيۡهَاۚ لَا تَبۡدِيلَ لِخَلۡقِ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ ٱلدِّينُ ٱلۡقَيِّمُ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ
To sai ka tsayar da fuskarka ga addini mai kauce wa varna. (Shi ne) asalin halittar da Allah Ya halicci mutane a kanta[1]. Ba wani canji ga halittar Allah. Wannan shi ne miqaqqen addini, sai dai kuma yawancin mutane ba su san (haka ba)
1- Watau kaxaita Allah da bauta. Addinin Musulunci shi ne addinin da ya dace da halittar xan’adam ta asali, watau fixra.