طسٓمٓ
XA SIN MIM
تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ
Waxannan ayoyi ne na Littafi mabayyani
لَعَلَّكَ بَٰخِعٞ نَّفۡسَكَ أَلَّا يَكُونُواْ مُؤۡمِنِينَ
Ko za ka kashe kanka ne don ba su zama muminai ba?
إِن نَّشَأۡ نُنَزِّلۡ عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ ءَايَةٗ فَظَلَّتۡ أَعۡنَٰقُهُمۡ لَهَا خَٰضِعِينَ
Da Mun ga dama da sai Mu saukar musu da aya daga sama sai wuyoyinsu su zamo masu qanqan da kai gare ta[1]
1- Watau mu’ujizar da za ta tilasta musu su miqa wuya ko ba sa so.
وَمَا يَأۡتِيهِم مِّن ذِكۡرٖ مِّنَ ٱلرَّحۡمَٰنِ مُحۡدَثٍ إِلَّا كَانُواْ عَنۡهُ مُعۡرِضِينَ
Kuma ba wani wa’azi sabo da zai zo musu daga (Allah) Mai rahama sai sun kasance masu bijire masa
فَقَدۡ كَذَّبُواْ فَسَيَأۡتِيهِمۡ أَنۢبَـٰٓؤُاْ مَا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ
To haqiqa sun qaryata, ba da daxewa ba labaran aqibar abin da suke yi wa izgili za su zo musu
أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ إِلَى ٱلۡأَرۡضِ كَمۡ أَنۢبَتۡنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوۡجٖ كَرِيمٍ
Shin ba su yi duba zuwa ga qasa ba, (su ga) dangogin tsirrai masu kyau nawa ne Muka tsirar daga cikinta?
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Lalle a game da wannan tabbas akwai aya (mai nuna cikar ikon Allah); kuma yawancinsu ba su zamanto masu imani ba
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Kuma lalle Ubangijinka tabbas Shi Mabuwayi ne, Mai rahama
وَإِذۡ نَادَىٰ رَبُّكَ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱئۡتِ ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Kuma (ka tuna) lokacin da Ubangijinka Ya kira Musa cewa: “Ka tafi wajen mutanen nan azzalumai
قَوۡمَ فِرۡعَوۡنَۚ أَلَا يَتَّقُونَ
“(Watau) mutanen Fir’auna. Yanzu ba za su kiyaye dokokin Allah ba?”
قَالَ رَبِّ إِنِّيٓ أَخَافُ أَن يُكَذِّبُونِ
(Musa) ya ce: “Ya Ubangijina, lalle ni ina tsoron su qaryata ni
وَيَضِيقُ صَدۡرِي وَلَا يَنطَلِقُ لِسَانِي فَأَرۡسِلۡ إِلَىٰ هَٰرُونَ
“Kuma qirjina yana quntata, kuma harshena ba ya sakuwa, sai Ka aika zuwa ga (xan’uwana) Haruna
وَلَهُمۡ عَلَيَّ ذَنۢبٞ فَأَخَافُ أَن يَقۡتُلُونِ
“Ni kuma akwai wani laifi da na yi musu, sai nake tsoron su kashe ni.”
قَالَ كَلَّاۖ فَٱذۡهَبَا بِـَٔايَٰتِنَآۖ إِنَّا مَعَكُم مُّسۡتَمِعُونَ
(Allah) Ya ce: “A’a; (ba abin da zai same ka), sai ku tafi (kai da xan’uwanka) da ayoyinmu; lalle Mu masu jin (komai da zai faru) ne tare da ku
فَأۡتِيَا فِرۡعَوۡنَ فَقُولَآ إِنَّا رَسُولُ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
“Ku je wajen Fir’auna sai ku faxa masa cewa: ‘Lalle mu manzannin Ubangijin talikai ne
أَنۡ أَرۡسِلۡ مَعَنَا بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ
“‘Cewa, ka sako mana da Banu-Isra’ila’.”
قَالَ أَلَمۡ نُرَبِّكَ فِينَا وَلِيدٗا وَلَبِثۡتَ فِينَا مِنۡ عُمُرِكَ سِنِينَ
(Fir’auna) ya ce: “Yanzu ba mu muka raine ka a cikinmu tun kana jariri ba, kuma ka zauna ka yi wasu shekaru na rayuwarka a cikinmu?
وَفَعَلۡتَ فَعۡلَتَكَ ٱلَّتِي فَعَلۡتَ وَأَنتَ مِنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ
“Ka kuma aikata aika-aikarka da ka aikata[1] alhali kuwa kana daga masu butulce wa (ni’imata)?”
1- Yana nufin kashe Baqibxe da ya yi lokacin da ya same shi yana faxa da Ba’isra’ile. Duba Suratul Qasas, ayat ta 15.
قَالَ فَعَلۡتُهَآ إِذٗا وَأَنَا۠ مِنَ ٱلضَّآلِّينَ
(Musa) ya ce: “Na aikata haka ne a lokacin ina cikin marasa shiriya (ta rashin wahayi)
فَفَرَرۡتُ مِنكُمۡ لَمَّا خِفۡتُكُمۡ فَوَهَبَ لِي رَبِّي حُكۡمٗا وَجَعَلَنِي مِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
“Sannan na guje muku lokacin da na tsorata da ku, sai Ubangijina Ya ba ni kyautar ilimi Ya kuma sanya ni daga manzanni
وَتِلۡكَ نِعۡمَةٞ تَمُنُّهَا عَلَيَّ أَنۡ عَبَّدتَّ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ
“Waccen ni’imar kuwa da kake goranta min ita saboda ka bautar da Bani-Isra’ila ne.”
قَالَ فِرۡعَوۡنُ وَمَا رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Fir’auna ya ce: “To wane ne Ubangijin talikai?”
قَالَ رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَآۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ
(Musa) ya ce: “(Shi ne) Ubangijin sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu, idan har kun kasance masu sakankancewa (da hakan)”
قَالَ لِمَنۡ حَوۡلَهُۥٓ أَلَا تَسۡتَمِعُونَ
(Fir’auna) ya ce da waxanda suke kewaye da shi: “Shin ba kwa jin (abin da yake faxa)?”
قَالَ رَبُّكُمۡ وَرَبُّ ءَابَآئِكُمُ ٱلۡأَوَّلِينَ
(Musa) ya ce: “Shi ne Ubangijinku kuma Ubangijin iyayenku na farko!”
قَالَ إِنَّ رَسُولَكُمُ ٱلَّذِيٓ أُرۡسِلَ إِلَيۡكُمۡ لَمَجۡنُونٞ
(Fir’auna) ya ce: “Lalle Manzon da aka aiko muku tabbas mai tavin hankali ne!”
قَالَ رَبُّ ٱلۡمَشۡرِقِ وَٱلۡمَغۡرِبِ وَمَا بَيۡنَهُمَآۖ إِن كُنتُمۡ تَعۡقِلُونَ
(Musa) ya ce: “(Shi ne) Ubangijin mahudar rana da mafaxarta da kuma abin da yake tsakaninsu; in kun zamanto masu hankalta.”
قَالَ لَئِنِ ٱتَّخَذۡتَ إِلَٰهًا غَيۡرِي لَأَجۡعَلَنَّكَ مِنَ ٱلۡمَسۡجُونِينَ
(Fir’auna) ya ce: “Na rantse in har ka riqi wani abin bauta ba ni ba, tabbas zan jefa ka cikin ‘yan kurkuku!”
قَالَ أَوَلَوۡ جِئۡتُكَ بِشَيۡءٖ مُّبِينٖ
(Musa) ya ce: “Ko da na zo maka da wani abu bayyananne?”