Surah: Suratus Saffat

Ayah : 151

أَلَآ إِنَّهُم مِّنۡ إِفۡكِهِمۡ لَيَقُولُونَ

Ku saurara! Lalle su saboda qaryarsu har suna cewa:



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 152

وَلَدَ ٱللَّهُ وَإِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ

“Allah Ya haihu!” Lalle kuwa su tabbas maqaryata ne



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 153

أَصۡطَفَى ٱلۡبَنَاتِ عَلَى ٱلۡبَنِينَ

Yanzu Ya zavi ‘ya’ya mata a kan ‘ya’ya maza?



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 154

مَا لَكُمۡ كَيۡفَ تَحۡكُمُونَ

Me ya same ku, qaqa kuke yin irin wannan hukunci?



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 155

أَفَلَا تَذَكَّرُونَ

Me ya sa ne ba kwa wa’azantuwa?



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 156

أَمۡ لَكُمۡ سُلۡطَٰنٞ مُّبِينٞ

Ko kuwa kuna da wata hujja ne bayyananniya?



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 157

فَأۡتُواْ بِكِتَٰبِكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

To ku kawo rubutaccen littafinku idan kun kasance masu gaskiya



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 158

وَجَعَلُواْ بَيۡنَهُۥ وَبَيۡنَ ٱلۡجِنَّةِ نَسَبٗاۚ وَلَقَدۡ عَلِمَتِ ٱلۡجِنَّةُ إِنَّهُمۡ لَمُحۡضَرُونَ

Suka kuma sanya dangantakar nasaba tsakaninsa da mala’iku. Lalle kuwa su mala’iku sun san cewa tabbas su (masu wannan da’awar) za a kawo su (cikin wuta)



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 159

سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يَصِفُونَ

Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffanta (Shi da shi)



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 160

إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ

Sai dai bayin Allah waxanda aka tsarkake



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 161

فَإِنَّكُمۡ وَمَا تَعۡبُدُونَ

Lalle ku da abin da kuke bauta wa



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 162

مَآ أَنتُمۡ عَلَيۡهِ بِفَٰتِنِينَ

Ba za ku iya vatar da kowa da shi ba



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 163

إِلَّا مَنۡ هُوَ صَالِ ٱلۡجَحِيمِ

Sai dai wanda zai shiga wutar Jahima



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 164

وَمَامِنَّآ إِلَّا لَهُۥ مَقَامٞ مَّعۡلُومٞ

(Jibrilu ya ce da Mala’iku): “Ba xai daga cikinmu face yana da wani matsayi sananne[1]


1- Watau na bautar Allah da yi masa xa’a.


Surah: Suratus Saffat

Ayah : 165

وَإِنَّا لَنَحۡنُ ٱلصَّآفُّونَ

“Lalle kuma mu masu yin sahu ne



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 166

وَإِنَّا لَنَحۡنُ ٱلۡمُسَبِّحُونَ

“Kuma lalle mu masu yin tasbihi ne.”



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 167

وَإِن كَانُواْ لَيَقُولُونَ

Kuma lalle su (kafirai) sun kasance suna cewa[1]:


1- Watau suna cika baki kafin a aiko musu da Manzon Allah ().


Surah: Suratus Saffat

Ayah : 168

لَوۡ أَنَّ عِندَنَا ذِكۡرٗا مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ

“Da muna da wani littafi irin na mutanen farko



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 169

لَكُنَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ

“Tabbas da mun kasance bayin Allah waxanda aka tsarkake.”



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 170

فَكَفَرُواْ بِهِۦۖ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ

(Yayin da Alqur’ani ya zo musu) sai suka kafirce da shi; to ba da daxewa ba za su sani



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 171

وَلَقَدۡ سَبَقَتۡ كَلِمَتُنَا لِعِبَادِنَا ٱلۡمُرۡسَلِينَ

Haqiqa kuma kalmarmu (ta ba da nasara) ta rigaya ga bayinmu manzanni



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 172

إِنَّهُمۡ لَهُمُ ٱلۡمَنصُورُونَ

Lalle su tabbas su ne ababen taimako



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 173

وَإِنَّ جُندَنَا لَهُمُ ٱلۡغَٰلِبُونَ

Kuma lalle rudunarmu tabbas su ne masu yin galaba



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 174

فَتَوَلَّ عَنۡهُمۡ حَتَّىٰ حِينٖ

Sai ka rabu da su har zuwa wani lokaci



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 175

وَأَبۡصِرۡهُمۡ فَسَوۡفَ يُبۡصِرُونَ

Kuma ka ganar da su (sakamakon kafirci), sannan ba da daxewa ba za su gani



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 176

أَفَبِعَذَابِنَا يَسۡتَعۡجِلُونَ

Yanzu azabarmu suke neman gaggautowa?



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 177

فَإِذَا نَزَلَ بِسَاحَتِهِمۡ فَسَآءَ صَبَاحُ ٱلۡمُنذَرِينَ

To lokacin da (azabar) ta sauka a sararin gidajensu, ai asubar waxanda aka yi wa gargaxi ta munana



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 178

وَتَوَلَّ عَنۡهُمۡ حَتَّىٰ حِينٖ

Kuma ka rabu da su har zuwa wani lokaci



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 179

وَأَبۡصِرۡ فَسَوۡفَ يُبۡصِرُونَ

Ka kuma ganar (da su sakamakon kafirci), ba da daxewa ba za su gani



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 180

سُبۡحَٰنَ رَبِّكَ رَبِّ ٱلۡعِزَّةِ عَمَّا يَصِفُونَ

Ubangijinka wanda yake Ubangiji ne Mabuwayi Ya tsarkaka daga abin da suke sifanta (Shi da shi)