Surah: Suratul A’araf

Ayah : 121

قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Suka ce: “Mun yi imani da Ubangijin talikai



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 122

رَبِّ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ

“Ubangijin Musa da Haruna.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 123

قَالَ فِرۡعَوۡنُ ءَامَنتُم بِهِۦ قَبۡلَ أَنۡ ءَاذَنَ لَكُمۡۖ إِنَّ هَٰذَا لَمَكۡرٞ مَّكَرۡتُمُوهُ فِي ٱلۡمَدِينَةِ لِتُخۡرِجُواْ مِنۡهَآ أَهۡلَهَاۖ فَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَ

Sai Fir’auna ya ce: “Yanzu kun yi imani da shi tun kafin in yi muku izini? Lalle wannan tabbas wani makirci ne da kuka qulla shi a nan cikin garin, don ku fitar da mutanensa daga cikinsa; to da sannu za ku sani



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 124

لَأُقَطِّعَنَّ أَيۡدِيَكُمۡ وَأَرۡجُلَكُم مِّنۡ خِلَٰفٖ ثُمَّ لَأُصَلِّبَنَّكُمۡ أَجۡمَعِينَ

“Lalle zan yanyanke hannayenku da qafafuwanku a tarnaqe, sannan kuma gaba xaya zan gicciye ku.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 125

قَالُوٓاْ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا مُنقَلِبُونَ

Sai suka ce: “Mu kam lalle masu komawa ne ga Ubangijinmu.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 126

وَمَا تَنقِمُ مِنَّآ إِلَّآ أَنۡ ءَامَنَّا بِـَٔايَٰتِ رَبِّنَا لَمَّا جَآءَتۡنَاۚ رَبَّنَآ أَفۡرِغۡ عَلَيۡنَا صَبۡرٗا وَتَوَفَّنَا مُسۡلِمِينَ

“Kuma ba don komai za ka azabtar da mu ba sai don kawai mun yi imani da ayoyin Ubangijinmu yayin da suka zo mana. Ya Ubangijinmu, Ka zubo mana haquri, kuma Ka karvi rayukanmu muna Musulmi.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 127

وَقَالَ ٱلۡمَلَأُ مِن قَوۡمِ فِرۡعَوۡنَ أَتَذَرُ مُوسَىٰ وَقَوۡمَهُۥ لِيُفۡسِدُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَيَذَرَكَ وَءَالِهَتَكَۚ قَالَ سَنُقَتِّلُ أَبۡنَآءَهُمۡ وَنَسۡتَحۡيِۦ نِسَآءَهُمۡ وَإِنَّا فَوۡقَهُمۡ قَٰهِرُونَ

Sai manyan gari cikin mutanen Fir’auna suka ce: “Yanzu za ka qyale Musa da mutanensa, don su yi varna a bayan qasa, kuma ya watsar da kai da abubuwan bautarka?”[1] Sai ya ce: “Lalle za mu karkashe ‘ya’yansu maza, mu qyale ‘ya’yansu mata da rai[2], kuma lalle mu masu rinjaye ne a kansu.”


1- Bahaushe yana cewa, ba a mugun sarki sai mugun bafade. Manyan fadawan Fir’auna ne suke zuga shi a kan ya gaggauta xaukar mataki a kan Musa () da mabiyansa.


2- Da alama yanzu zai riqa kashe ‘ya’yan muminai ne kaxai. Ba kamar yadda yake kuxin goro da farko ba ba tare da bambancewa tsakanin Banu Isra’ila waxanda suka bi shi da waxanda ba su bi shi ba.


Surah: Suratul A’araf

Ayah : 128

قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِ ٱسۡتَعِينُواْ بِٱللَّهِ وَٱصۡبِرُوٓاْۖ إِنَّ ٱلۡأَرۡضَ لِلَّهِ يُورِثُهَا مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۖ وَٱلۡعَٰقِبَةُ لِلۡمُتَّقِينَ

Sai Musa ya ce da mutanensa: “Ku nemi taimakon Allah, kuma ku yi haquri; lalle qasa mulkin Allah ce, Yana gadar da ita ga wanda Ya ga dama daga cikin bayinsa; kuma kyakkyawan qarshe yana tabbata ne ga masu taqawa.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 129

قَالُوٓاْ أُوذِينَا مِن قَبۡلِ أَن تَأۡتِيَنَا وَمِنۢ بَعۡدِ مَا جِئۡتَنَاۚ قَالَ عَسَىٰ رَبُّكُمۡ أَن يُهۡلِكَ عَدُوَّكُمۡ وَيَسۡتَخۡلِفَكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرَ كَيۡفَ تَعۡمَلُونَ

Sai suka ce: “An cutar da mu tun kafin ka zo mana, da kuma bayan ka zo mana.” Sai ya ce: “Ta yiwu Ubangijinku Ya halakar da abokan gabarku, kuma Ya mayar da ku halifofi a bayan qasa, sai Ya ga kuma, me za ku aikata?”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 130

وَلَقَدۡ أَخَذۡنَآ ءَالَ فِرۡعَوۡنَ بِٱلسِّنِينَ وَنَقۡصٖ مِّنَ ٱلثَّمَرَٰتِ لَعَلَّهُمۡ يَذَّكَّرُونَ

Kuma lalle haqiqa Mun jarrabi iyalin gidan Fir’auna da shekaru na fari da kuma tawayar ‘ya’yan itace, ko sa yi tuntuntuni



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 131

فَإِذَا جَآءَتۡهُمُ ٱلۡحَسَنَةُ قَالُواْ لَنَا هَٰذِهِۦۖ وَإِن تُصِبۡهُمۡ سَيِّئَةٞ يَطَّيَّرُواْ بِمُوسَىٰ وَمَن مَّعَهُۥٓۗ أَلَآ إِنَّمَا طَـٰٓئِرُهُمۡ عِندَ ٱللَّهِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

Amma yayin da daddaxan abu ya zo musu, sai su ce: “Da ma wannan namu ne.” Idan kuma mummunan abu ya same su, sai su camfa Musa da waxanda suke tare da shi. Ku saurara, kawai dai mummunan abin da ya same su daga wajen Allah yake, amma yawancinsu ba sa sanin (haka)



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 132

وَقَالُواْ مَهۡمَا تَأۡتِنَا بِهِۦ مِنۡ ءَايَةٖ لِّتَسۡحَرَنَا بِهَا فَمَا نَحۡنُ لَكَ بِمُؤۡمِنِينَ

Kuma suka ce: “Kowace irin aya ka zo mana da ita, don ka sihirce mu da ita, to fa mu ba za mu yi imani da kai ba.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 133

فَأَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمُ ٱلطُّوفَانَ وَٱلۡجَرَادَ وَٱلۡقُمَّلَ وَٱلضَّفَادِعَ وَٱلدَّمَ ءَايَٰتٖ مُّفَصَّلَٰتٖ فَٱسۡتَكۡبَرُواْ وَكَانُواْ قَوۡمٗا مُّجۡرِمِينَ

Sai Muka aika musu da ambaliyar ruwa da fara da qwarqwata da kwaxi da jini, a matsayin ayoyi daki-daki, sai suka yi girman kai, kuma suka kasance mutane masu babban laifi



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 134

وَلَمَّا وَقَعَ عَلَيۡهِمُ ٱلرِّجۡزُ قَالُواْ يَٰمُوسَى ٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ بِمَا عَهِدَ عِندَكَۖ لَئِن كَشَفۡتَ عَنَّا ٱلرِّجۡزَ لَنُؤۡمِنَنَّ لَكَ وَلَنُرۡسِلَنَّ مَعَكَ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ

Kuma yayin da azaba ta sauka a kansu, sai suka ce: “Ya kai Musa, ka roqa mana Ubangijinka, saboda alqawarin da Ya yi maka; lalle idan har ka yaye mana wannan azaba, to tabbas za mu yi imani da kai, kuma za mu sakar maka Banu Isra’ila.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 135

فَلَمَّا كَشَفۡنَا عَنۡهُمُ ٱلرِّجۡزَ إِلَىٰٓ أَجَلٍ هُم بَٰلِغُوهُ إِذَا هُمۡ يَنكُثُونَ

To yayin da Muka yaye musu wannan azaba zuwa wani lokacin da za su kai gare shi, sai ga shi suna warware alqawarin da suka yi



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 136

فَٱنتَقَمۡنَا مِنۡهُمۡ فَأَغۡرَقۡنَٰهُمۡ فِي ٱلۡيَمِّ بِأَنَّهُمۡ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَكَانُواْ عَنۡهَا غَٰفِلِينَ

Sai Muka azabtar da su, Muka dulmiyar da su a cikin kogi saboda sun qaryata ayoyinmu, kuma sun kasance gafalallu game da su



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 137

وَأَوۡرَثۡنَا ٱلۡقَوۡمَ ٱلَّذِينَ كَانُواْ يُسۡتَضۡعَفُونَ مَشَٰرِقَ ٱلۡأَرۡضِ وَمَغَٰرِبَهَا ٱلَّتِي بَٰرَكۡنَا فِيهَاۖ وَتَمَّتۡ كَلِمَتُ رَبِّكَ ٱلۡحُسۡنَىٰ عَلَىٰ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ بِمَا صَبَرُواْۖ وَدَمَّرۡنَا مَا كَانَ يَصۡنَعُ فِرۡعَوۡنُ وَقَوۡمُهُۥ وَمَا كَانُواْ يَعۡرِشُونَ

Mutanen kuma da ake nuna musu fin qarfi a da, Muka gadar musu gabashi da yammacin qasar da Muka yi wa albarka; kuma kalmar Ubangijinka kyakkyawa sai ta tabbata a kan Banu Isra’ila saboda haqurin da suka yi; kuma Muka rushe abin da Fir’auna ya kasance yana yi shi da mutanensa, da abin da suka kasance suna ginawa



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 138

وَجَٰوَزۡنَا بِبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ ٱلۡبَحۡرَ فَأَتَوۡاْ عَلَىٰ قَوۡمٖ يَعۡكُفُونَ عَلَىٰٓ أَصۡنَامٖ لَّهُمۡۚ قَالُواْ يَٰمُوسَى ٱجۡعَل لَّنَآ إِلَٰهٗا كَمَا لَهُمۡ ءَالِهَةٞۚ قَالَ إِنَّكُمۡ قَوۡمٞ تَجۡهَلُونَ

Kuma sai Muka tsallakar da Banu Isra’ila kogi, sai suka tarar da waxansu mutane da suka duqufa a kan (bautar) gumakansu, suka ce: “Ya kai Musa, ka sa mana wani abin bauta, irin yadda waxannan suke da abubuwan bauta.” Sai ya ce: “Lalle ku mutane ne da kuke da jahilci



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 139

إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ مُتَبَّرٞ مَّا هُمۡ فِيهِ وَبَٰطِلٞ مَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

“Lalle waxannan abin da suke cikinsa halaka ne, kuma abin da suke aikatawa varna ce.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 140

قَالَ أَغَيۡرَ ٱللَّهِ أَبۡغِيكُمۡ إِلَٰهٗا وَهُوَ فَضَّلَكُمۡ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ

Ya ce: “Shin yanzu wani wanda ba Allah ba zan nemo muku a matsayin abin bauta, alhali Shi ne Ya fifita ku a kan sauran talikai?”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 141

وَإِذۡ أَنجَيۡنَٰكُم مِّنۡ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ يَسُومُونَكُمۡ سُوٓءَ ٱلۡعَذَابِ يُقَتِّلُونَ أَبۡنَآءَكُمۡ وَيَسۡتَحۡيُونَ نِسَآءَكُمۡۚ وَفِي ذَٰلِكُم بَلَآءٞ مِّن رَّبِّكُمۡ عَظِيمٞ

Kuma ku tuna lokacin da Muka tserar da ku daga mutanen Fir’auna, (waxanda) suke xanxana muku mummunar azaba; suna karkashe ‘ya’yanku maza, kuma suna barin ‘ya’yanku mata da rai, kuma lalle a cikin wannan akwai wata jarraba babba daga Ubangijinku



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 142

۞وَوَٰعَدۡنَا مُوسَىٰ ثَلَٰثِينَ لَيۡلَةٗ وَأَتۡمَمۡنَٰهَا بِعَشۡرٖ فَتَمَّ مِيقَٰتُ رَبِّهِۦٓ أَرۡبَعِينَ لَيۡلَةٗۚ وَقَالَ مُوسَىٰ لِأَخِيهِ هَٰرُونَ ٱخۡلُفۡنِي فِي قَوۡمِي وَأَصۡلِحۡ وَلَا تَتَّبِعۡ سَبِيلَ ٱلۡمُفۡسِدِينَ

Mun kuma yi wa Musa alqawarin dare talatin, muka kuma cika su da goma, sai miqatin Ubangijinsa ya cika darare arba’in cif-cif. Sai Musa ya ce da xan’uwansa Haruna: “Ka wakilce ni a cikin mutanena, kuma ka daidaita (tsakaninsu), kada kuma ka bi tafarkin mavarnata.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 143

وَلَمَّا جَآءَ مُوسَىٰ لِمِيقَٰتِنَا وَكَلَّمَهُۥ رَبُّهُۥ قَالَ رَبِّ أَرِنِيٓ أَنظُرۡ إِلَيۡكَۚ قَالَ لَن تَرَىٰنِي وَلَٰكِنِ ٱنظُرۡ إِلَى ٱلۡجَبَلِ فَإِنِ ٱسۡتَقَرَّ مَكَانَهُۥ فَسَوۡفَ تَرَىٰنِيۚ فَلَمَّا تَجَلَّىٰ رَبُّهُۥ لِلۡجَبَلِ جَعَلَهُۥ دَكّٗا وَخَرَّ مُوسَىٰ صَعِقٗاۚ فَلَمَّآ أَفَاقَ قَالَ سُبۡحَٰنَكَ تُبۡتُ إِلَيۡكَ وَأَنَا۠ أَوَّلُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Lokacin Kuma da Musa ya zo wajen da muka yi alqawari da shi, Ubangijinsa kuma Ya yi magana da shi, sai ya ce: “Ya Ubangijina, nuna mini kanka in gan Ka.” Sai ya ce: “Ba za ka iya gani Na ba[1], amma dubi dutsen nan, idan ya tabbata a bigirensa, to da sannu za ka gan Ni.” To lokacin da Ubangijinsa Ya bayyana (da haskensa) ga dutsen, sai Ya mayar da shi rugu-rugu, sai Musa ya faxi sumamme. To yayin da ya farfaxo, sai ya ce: “Tsarki ya tabbata gare Ka, na tuba zuwa gare Ka, kuma ni ne farkon muminai.”


1- Muminai a nan duniya ba za su iya ganin Allah () a fili ba, amma a lahira za su gan shi kamar yadda hadisai da yawa suka tabbatar.


Surah: Suratul A’araf

Ayah : 144

قَالَ يَٰمُوسَىٰٓ إِنِّي ٱصۡطَفَيۡتُكَ عَلَى ٱلنَّاسِ بِرِسَٰلَٰتِي وَبِكَلَٰمِي فَخُذۡ مَآ ءَاتَيۡتُكَ وَكُن مِّنَ ٱلشَّـٰكِرِينَ

Ya ce: “Ya kai Musa, Lalle Ni na zave ka a kan sauran mutane da saqona da kuma zancena, don haka ka riqe abin da na ba ka, kuma ka kasance cikin masu godiya.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 145

وَكَتَبۡنَا لَهُۥ فِي ٱلۡأَلۡوَاحِ مِن كُلِّ شَيۡءٖ مَّوۡعِظَةٗ وَتَفۡصِيلٗا لِّكُلِّ شَيۡءٖ فَخُذۡهَا بِقُوَّةٖ وَأۡمُرۡ قَوۡمَكَ يَأۡخُذُواْ بِأَحۡسَنِهَاۚ سَأُوْرِيكُمۡ دَارَ ٱلۡفَٰسِقِينَ

Mun kuma rubuta masa komai a cikin allunan (Attaura) don wa’azi da bayani filla-filla na kowane irin abu, don haka ka riqe su da kyau, kuma ka umarci mutanenka su yi riqo da mafi kyawun abin da yake cikinsu. Da sannu zan nuna muku gidajen fasiqai[1].”


1- Wasu sun ce ana nufin wutar Jahannama. Wasu kuma sun ce, ana nufin Baitul Maqdis, saboda mazaunanta a wannan lokaci mushirikai ne. Wasu kuma sun ce, ana nufin qasar Masar da Baitul Maqdisi baki xaya.


Surah: Suratul A’araf

Ayah : 146

سَأَصۡرِفُ عَنۡ ءَايَٰتِيَ ٱلَّذِينَ يَتَكَبَّرُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَإِن يَرَوۡاْ كُلَّ ءَايَةٖ لَّا يُؤۡمِنُواْ بِهَا وَإِن يَرَوۡاْ سَبِيلَ ٱلرُّشۡدِ لَا يَتَّخِذُوهُ سَبِيلٗا وَإِن يَرَوۡاْ سَبِيلَ ٱلۡغَيِّ يَتَّخِذُوهُ سَبِيلٗاۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَكَانُواْ عَنۡهَا غَٰفِلِينَ

Zan kautar da waxanda suke yin girman kai a bayan qasa ba tare da haqqi ba daga (fahimtar) ayoyina; idan kuma za su ga kowace irin aya ba za su yi imani da ita ba, idan kuma da za su ga hanyar shiriya ba za su riqe ta hanyar bi ba, (amma) idan kuwa za su ga hanyar vata, to za su riqe ta hanyar bi. Wannan kuwa saboda sun qaryata ayoyinmu, kuma sun kasance gafalallu ga barin su



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 147

وَٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَلِقَآءِ ٱلۡأٓخِرَةِ حَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡۚ هَلۡ يُجۡزَوۡنَ إِلَّا مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Waxanda kuma suka qaryata ayoyinmu da haxuwa a ranar alqiyama, ayyukansu sun rushe. Shin kuwa za a yi musu wani sakamako ne in ba abin da suka kasance suna aikatawa ba?



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 148

وَٱتَّخَذَ قَوۡمُ مُوسَىٰ مِنۢ بَعۡدِهِۦ مِنۡ حُلِيِّهِمۡ عِجۡلٗا جَسَدٗا لَّهُۥ خُوَارٌۚ أَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّهُۥ لَا يُكَلِّمُهُمۡ وَلَا يَهۡدِيهِمۡ سَبِيلًاۘ ٱتَّخَذُوهُ وَكَانُواْ ظَٰلِمِينَ

Mutanen Musa kuma a bayansa sun qera wani xan maraqi daga kayan adonsu mai surar jiki yana wata qara (don su bauta masa). Shin ba su ga cewa ba ya yi musu Magana, kuma ba ya iya shiryar da su wani tafarki? Sun riqe shi (a matsayin abin bauta), kuma sun tabbata azzalumai



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 149

وَلَمَّا سُقِطَ فِيٓ أَيۡدِيهِمۡ وَرَأَوۡاْ أَنَّهُمۡ قَدۡ ضَلُّواْ قَالُواْ لَئِن لَّمۡ يَرۡحَمۡنَا رَبُّنَا وَيَغۡفِرۡ لَنَا لَنَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

Kuma lokacin da suka yi nadama, suka gane cewa sun vata, sai suka ce: “Matuqar Ubangijinmu bai ji qan mu ba, kuma bai gafarta mana ba, lalle za mu kasance cikin hasararru.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 150

وَلَمَّا رَجَعَ مُوسَىٰٓ إِلَىٰ قَوۡمِهِۦ غَضۡبَٰنَ أَسِفٗا قَالَ بِئۡسَمَا خَلَفۡتُمُونِي مِنۢ بَعۡدِيٓۖ أَعَجِلۡتُمۡ أَمۡرَ رَبِّكُمۡۖ وَأَلۡقَى ٱلۡأَلۡوَاحَ وَأَخَذَ بِرَأۡسِ أَخِيهِ يَجُرُّهُۥٓ إِلَيۡهِۚ قَالَ ٱبۡنَ أُمَّ إِنَّ ٱلۡقَوۡمَ ٱسۡتَضۡعَفُونِي وَكَادُواْ يَقۡتُلُونَنِي فَلَا تُشۡمِتۡ بِيَ ٱلۡأَعۡدَآءَ وَلَا تَجۡعَلۡنِي مَعَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Lokacin kuma da Musa ya dawo wajen mutanensa a fusace yana mai damuwa, sai ya ce: “Tir da abin da kuka aikata bayana. Yanzu kwa gaggauto al’amarin Ubangijinku?” Sai ya jefar da allunan, ya kama kan xan’uwansa yana jan sa zuwa gare shi. Sai (Haruna) ya ce: “Ya kai xan’ummata, mutanen nan haqiqa sun raina ni, har ma sun kusa kashe ni, don haka kar ka sa maqiya su yi min dariya, kuma kada ka sa ni cikin mutane azzalumai.”