إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Lalle Mu kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa
Share :
إِنَّهُمَا مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Lalle suna daga cikin bayinmu muminai
وَإِنَّ إِلۡيَاسَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Kuma lalle Ilyasu tabbas yana daga cikin manzanni
إِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهِۦٓ أَلَا تَتَّقُونَ
Lokacin da ya ce da mutanensa: “Yanzu ba za ku kiyaye dokokin (Allah) ba?
أَتَدۡعُونَ بَعۡلٗا وَتَذَرُونَ أَحۡسَنَ ٱلۡخَٰلِقِينَ
“Yanzu kwa riqa bauta wa (gunkin) Ba’alu ku riqa barin Mafi iya kyautata halitta?
ٱللَّهَ رَبَّكُمۡ وَرَبَّ ءَابَآئِكُمُ ٱلۡأَوَّلِينَ
“(Wato) Allah Ubangijinku kuma Ubangijin iyayenku na farko?”
فَكَذَّبُوهُ فَإِنَّهُمۡ لَمُحۡضَرُونَ
Sai suka qaryata shi, to don haka, lalle za a halarto da su (wuta)
إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ
Sai dai bayin Allah waxanda aka tsarkake
وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ
Muka kuma bar (kyakkyawan yabo) a gare shi ga ‘yan baya
سَلَٰمٌ عَلَىٰٓ إِلۡ يَاسِينَ
Aminci ya tabbata ga Ilyasu
إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Lalle shi yana daga bayinmu muminai
وَإِنَّ لُوطٗا لَّمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Lalle kuma Luxu tabbas yana daga cikin manzanni
إِذۡ نَجَّيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥٓ أَجۡمَعِينَ
(Ka tuna) sanda Muka tserar da shi tare da iyalinsa baki xaya
إِلَّا عَجُوزٗا فِي ٱلۡغَٰبِرِينَ
Sai dai wata tsohuwa (wato matarsa) da take cikin halakakku
ثُمَّ دَمَّرۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ
Sannan Muka hallakar da sauran
وَإِنَّكُمۡ لَتَمُرُّونَ عَلَيۡهِم مُّصۡبِحِينَ
Kuma lalle ku[1] tabbas kuna wucewa ta wajan (gidajensu) da asussuba
1- Watau ku mutanen Makka.
وَبِٱلَّيۡلِۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ
Da kuma cikin dare. Yanzu ba kwa hankalta ba?
وَإِنَّ يُونُسَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Kuma lalle Yunusa tabbas yana daga cikin manzanni
إِذۡ أَبَقَ إِلَى ٱلۡفُلۡكِ ٱلۡمَشۡحُونِ
(Ka tuna) lokacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwan da yake maqare
فَسَاهَمَ فَكَانَ مِنَ ٱلۡمُدۡحَضِينَ
Sannan ya shiga quri’a, sai ya zama cikin waxanda aka yi galaba a kansu
فَٱلۡتَقَمَهُ ٱلۡحُوتُ وَهُوَ مُلِيمٞ
Sai kifi ya haxiye shi, alhali yana abin zargi[1]
1- Watau a kan guduwa ya bar mutanensa ba tare da izinin Allah ba.
فَلَوۡلَآ أَنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلۡمُسَبِّحِينَ
Ba don dai shi ya zama daga masu tsarkake Allah (da yawan tasbihi) ba
لَلَبِثَ فِي بَطۡنِهِۦٓ إِلَىٰ يَوۡمِ يُبۡعَثُونَ
Tabbas da ya zauna a cikin cikinsa har zuwa ranar da za a tashe su[1]
1- Watau ranar alqiyama, domin zai zama shi ne qabarinsa.
۞فَنَبَذۡنَٰهُ بِٱلۡعَرَآءِ وَهُوَ سَقِيمٞ
Sai Muka jefa shi a tudu, a halin yana cikin rashin lafiya
وَأَنۢبَتۡنَا عَلَيۡهِ شَجَرَةٗ مِّن يَقۡطِينٖ
Muka kuma tsirar masa wata bishiya ta kabewa[1]
1- Domin ya rufe tsiraicinsa da ganyenta, ya kuma ci ‘ya’yanta, ya kuma sha inuwarta.
وَأَرۡسَلۡنَٰهُ إِلَىٰ مِاْئَةِ أَلۡفٍ أَوۡ يَزِيدُونَ
Muka kuma aika shi zuwa ga mutum dubu xari, ko kuma sama da haka
فَـَٔامَنُواْ فَمَتَّعۡنَٰهُمۡ إِلَىٰ حِينٖ
Sai suka yi imani, sai Muka jiyar da su daxi har zuwa wani lokaci
فَٱسۡتَفۡتِهِمۡ أَلِرَبِّكَ ٱلۡبَنَاتُ وَلَهُمُ ٱلۡبَنُونَ
Ka tambaye su: Yanzu Ubangijinka ne Yake da ‘ya’ya mata, su kuma suna da ‘ya’ya maza[1]?
1- Mushirikan Larabawa suna cewa mala’iku mata ne kuma ‘ya’yan Allah ne, yayin da sus uke fifita ‘ya’ya maza ga kawunansu.
أَمۡ خَلَقۡنَا ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ إِنَٰثٗا وَهُمۡ شَٰهِدُونَ
Ko kuma Mun halicci mala’iku ne ‘ya’ya mata a gaban idonsu suna gani?