Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 91

وَٱلَّتِيٓ أَحۡصَنَتۡ فَرۡجَهَا فَنَفَخۡنَا فِيهَا مِن رُّوحِنَا وَجَعَلۡنَٰهَا وَٱبۡنَهَآ ءَايَةٗ لِّلۡعَٰلَمِينَ

(Ka tuna) kuma wadda ta tsare matancinta, sai Muka yi busa a cikinta daga Ruhinmu, Muka kuma sanya ta ita da xanta aya ga talikai



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 92

إِنَّ هَٰذِهِۦٓ أُمَّتُكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَأَنَا۠ رَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُونِ

Lallai wannan addini naku guda xaya ne (wato Musulunci), kuma Ni ne Ubangijinku, to ku bauta min



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 93

وَتَقَطَّعُوٓاْ أَمۡرَهُم بَيۡنَهُمۡۖ كُلٌّ إِلَيۡنَا رَٰجِعُونَ

Sannan sai suka rarraba al’amarinsu (na addini) a tsakaninsu; dukkaninsu dai masu komowa ne zuwa gare Mu



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 94

فَمَن يَعۡمَلۡ مِنَ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَا كُفۡرَانَ لِسَعۡيِهِۦ وَإِنَّا لَهُۥ كَٰتِبُونَ

To duk wanda ya aikata kyawawan ayyuka alhali kuwa shi mumini ne, to babu musantawa ga aikinsa[1], lallai kuma Mu Masu rubuta masa shi ne


1- Watau ba za a yi masa runton aikinsa mai kyau ba, za a yi masa kyakkyawar sakayya ne a kai.


Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 95

وَحَرَٰمٌ عَلَىٰ قَرۡيَةٍ أَهۡلَكۡنَٰهَآ أَنَّهُمۡ لَا يَرۡجِعُونَ

Kuma haramun ne ga (duk) wata al’umma da Muka hallaka cewa za su komo (duniya)



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 96

حَتَّىٰٓ إِذَا فُتِحَتۡ يَأۡجُوجُ وَمَأۡجُوجُ وَهُم مِّن كُلِّ حَدَبٖ يَنسِلُونَ

Har sai lokacin da aka buxe Yajuju da Majuju, su kuwa za su gangaro ne ta kowanne tudu



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 97

وَٱقۡتَرَبَ ٱلۡوَعۡدُ ٱلۡحَقُّ فَإِذَا هِيَ شَٰخِصَةٌ أَبۡصَٰرُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يَٰوَيۡلَنَا قَدۡ كُنَّا فِي غَفۡلَةٖ مِّنۡ هَٰذَا بَلۡ كُنَّا ظَٰلِمِينَ

Kuma alqawarin gaskiya ya gabato, sai ga shi idanuwan waxanda suka kafirta sun yi zuru-zuru (suna cewa): “Kaiconmu! Haqiqa mun kasance cikin gafala game da wannan (ranar); a’a, kai mu dai mun kasance azzalumai ne!”



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 98

إِنَّكُمۡ وَمَا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ حَصَبُ جَهَنَّمَ أَنتُمۡ لَهَا وَٰرِدُونَ

(Sai a ce da su): “Lallai ku da abin da kuke bauta wa ba Allah ba, (duka) makamashin Jahannama ne, kuma ku masu shigar ta ne.”



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 99

لَوۡ كَانَ هَـٰٓؤُلَآءِ ءَالِهَةٗ مَّا وَرَدُوهَاۖ وَكُلّٞ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Da waxancan (gumakan) sun kasance alloli (na gaske) da ba su shiga cikinta ba, dukkaninsu kuwa madawwama ne a cikinta



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 100

لَهُمۡ فِيهَا زَفِيرٞ وَهُمۡ فِيهَا لَا يَسۡمَعُونَ

Suna ta qaraji a cikinta, alhali kuwa su a cikinta ba sa jin (sautin komai)



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 101

إِنَّ ٱلَّذِينَ سَبَقَتۡ لَهُم مِّنَّا ٱلۡحُسۡنَىٰٓ أُوْلَـٰٓئِكَ عَنۡهَا مُبۡعَدُونَ

Lalle waxanda kalmarmu mafi kyau (ta cewa su ‘yan Aljanna ne) ta riga ta tabbata gare su, waxannan waxanda ake nesantawa ne daga gare ta (wutar)



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 102

لَا يَسۡمَعُونَ حَسِيسَهَاۖ وَهُمۡ فِي مَا ٱشۡتَهَتۡ أَنفُسُهُمۡ خَٰلِدُونَ

Ba za su ji hargowarta ba, kuma su masu dawwama ne cikin abin da ransu yake so



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 103

لَا يَحۡزُنُهُمُ ٱلۡفَزَعُ ٱلۡأَكۡبَرُ وَتَتَلَقَّىٰهُمُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ هَٰذَا يَوۡمُكُمُ ٱلَّذِي كُنتُمۡ تُوعَدُونَ

Babbar firgitar (wannan ranar) ba ta samun su, kuma mala’iku za su tare su, (suna cewa): “Wannan ita ce ranar taku wadda kuka zamanto ana yi muku alqawarinta (a duniya).”



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 104

يَوۡمَ نَطۡوِي ٱلسَّمَآءَ كَطَيِّ ٱلسِّجِلِّ لِلۡكُتُبِۚ كَمَا بَدَأۡنَآ أَوَّلَ خَلۡقٖ نُّعِيدُهُۥۚ وَعۡدًا عَلَيۡنَآۚ إِنَّا كُنَّا فَٰعِلِينَ

(Ita ce) ranar da za Mu naxe sama kamar naxin marubuci ga takardu. Kamar yadda Muka qagi halitta da farko (haka) za Mu mai da ita. Wannan alqawari ne da Muka xauka. Lallai Mun kasance Masu aikata (haka)



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 105

وَلَقَدۡ كَتَبۡنَا فِي ٱلزَّبُورِ مِنۢ بَعۡدِ ٱلذِّكۡرِ أَنَّ ٱلۡأَرۡضَ يَرِثُهَا عِبَادِيَ ٱلصَّـٰلِحُونَ

Kuma haqiqa Mun rubuta cikin saukakkun littattafai bayan (an rubuta a Lauhul-Mahfuzu) cewa, ita qasa bayina na gari ne za su gaje ta



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 106

إِنَّ فِي هَٰذَا لَبَلَٰغٗا لِّقَوۡمٍ عَٰبِدِينَ

Lallai a cikin wannan (Alqur’ani) akwai isar da saqo ga mutane masu bauta



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 107

وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ إِلَّا رَحۡمَةٗ لِّلۡعَٰلَمِينَ

Ba Mu aiko ka ba sai don rahama ga talikai



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 108

قُلۡ إِنَّمَا يُوحَىٰٓ إِلَيَّ أَنَّمَآ إِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ فَهَلۡ أَنتُم مُّسۡلِمُونَ

Ka ce (da su): “Abin da kawai ake yiwo min wahayinsa (shi ne) lallai abin bautar ku Allah ne Guda Xaya; to shin ko za ku miqa wuya?”



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 109

فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَقُلۡ ءَاذَنتُكُمۡ عَلَىٰ سَوَآءٖۖ وَإِنۡ أَدۡرِيٓ أَقَرِيبٌ أَم بَعِيدٞ مَّا تُوعَدُونَ

To idan sun ba da baya sai ka ce (da su): “Na sanar da ku cewa ni da ku muna kan abu xaya ne (wato ta-ware). Kuma ni ban sani ba, shin abin da ake yi muku alqawari da shi[1] kusa yake ko kuwa nesa?


1- Watau alqawarin zuwan azabar Allah a gare su.


Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 110

إِنَّهُۥ يَعۡلَمُ ٱلۡجَهۡرَ مِنَ ٱلۡقَوۡلِ وَيَعۡلَمُ مَا تَكۡتُمُونَ

“Lalle Shi (Allah) Yana sane da (abin da kuke) bayyanawa na magana Yana kuma sane da abin da kuke voyewa



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 111

وَإِنۡ أَدۡرِي لَعَلَّهُۥ فِتۡنَةٞ لَّكُمۡ وَمَتَٰعٌ إِلَىٰ حِينٖ

“Kuma ban sani ba ko wataqila shi (jinkirta azabtar da ku) fitina ne a gare ku da kuma jin daxi zuwa wani xan lokaci



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 112

قَٰلَ رَبِّ ٱحۡكُم بِٱلۡحَقِّۗ وَرَبُّنَا ٱلرَّحۡمَٰنُ ٱلۡمُسۡتَعَانُ عَلَىٰ مَا تَصِفُونَ

(Annabi Muhammadu) ya ce: “Ya Ubangijina, Ka yi hukunci (tsakanina da kafirai) da gaskiya. Ubangijinmu kuwa (Shi ne) Ar-Rahamanu Wanda ake neman taimakonsa a kan abin da kuke siffantawa.”