Surah: Suratu Hud

Ayah : 91

قَالُواْ يَٰشُعَيۡبُ مَا نَفۡقَهُ كَثِيرٗا مِّمَّا تَقُولُ وَإِنَّا لَنَرَىٰكَ فِينَا ضَعِيفٗاۖ وَلَوۡلَا رَهۡطُكَ لَرَجَمۡنَٰكَۖ وَمَآ أَنتَ عَلَيۡنَا بِعَزِيزٖ

Suka ce: “Ya kai Shu’aibu, ba ma fahimtar da yawa daga abin da kake faxa; lalle kuma tabbas muna ganin ka rarrauna a cikinmu, kuma ba don danginka ba da mun jefe ka; ba kuwa za ka gagare mu ba.”



Surah: Suratu Hud

Ayah : 92

قَالَ يَٰقَوۡمِ أَرَهۡطِيٓ أَعَزُّ عَلَيۡكُم مِّنَ ٱللَّهِ وَٱتَّخَذۡتُمُوهُ وَرَآءَكُمۡ ظِهۡرِيًّاۖ إِنَّ رَبِّي بِمَا تَعۡمَلُونَ مُحِيطٞ

Ya ce: “Ya ku mutanena, yanzu dangin nawa ne suka fi Allah girma a wurinku, kuka kuma xauke shi abin jefarwa a can bayanku? Lalle Ubangijina a kewaye Yake da (sanin) abin da kuke aikatawa



Surah: Suratu Hud

Ayah : 93

وَيَٰقَوۡمِ ٱعۡمَلُواْ عَلَىٰ مَكَانَتِكُمۡ إِنِّي عَٰمِلٞۖ سَوۡفَ تَعۡلَمُونَ مَن يَأۡتِيهِ عَذَابٞ يُخۡزِيهِ وَمَنۡ هُوَ كَٰذِبٞۖ وَٱرۡتَقِبُوٓاْ إِنِّي مَعَكُمۡ رَقِيبٞ

“Kuma ya ku mutanena, ku yi aiki a kan irin hanyarku; ni ma lalle mai yin aiki ne (a kan tawa). Ba da daxewa ba za ku san wanda azaba mai wulakantawa za ta zo masa, da kuma wanda yake maqaryaci. Ku saurara, ni ma lalle mai sauraro ne tare da ku.”



Surah: Suratu Hud

Ayah : 94

وَلَمَّا جَآءَ أَمۡرُنَا نَجَّيۡنَا شُعَيۡبٗا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ بِرَحۡمَةٖ مِّنَّا وَأَخَذَتِ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ ٱلصَّيۡحَةُ فَأَصۡبَحُواْ فِي دِيَٰرِهِمۡ جَٰثِمِينَ

Lokacin kuwa da umarninmu ya zo Muka tserar da Shu’aibu tare da waxanda suka yi imani da shi da wata rahama daga gare mu; tsawa kuma ta kama waxanda suka kafirta, sai suka wayi gari cikin gidajensu a duddurqushe, (ba rai)



Surah: Suratu Hud

Ayah : 95

كَأَن لَّمۡ يَغۡنَوۡاْ فِيهَآۗ أَلَا بُعۡدٗا لِّمَدۡيَنَ كَمَا بَعِدَتۡ ثَمُودُ

Kamar daxai ba su tava zama ba a cikinsu (gidajen) ba. Ku saurara; halaka ta tabbata ga (mutanen) Madyana kamar yadda Samudawa suka halaka



Surah: Suratu Hud

Ayah : 96

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مُوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَا وَسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٍ

Haqiqa kuma Mun aiko Musa da ayoyinmu da hijjoji bayyanannu



Surah: Suratu Hud

Ayah : 97

إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ فَٱتَّبَعُوٓاْ أَمۡرَ فِرۡعَوۡنَۖ وَمَآ أَمۡرُ فِرۡعَوۡنَ بِرَشِيدٖ

Zuwa ga Fir’auna da manyan fadawansa, sai suka bi umarnin Fir’auna; amma kuma umarnin Fir’auna ba a kan hanya yake ba



Surah: Suratu Hud

Ayah : 98

يَقۡدُمُ قَوۡمَهُۥ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فَأَوۡرَدَهُمُ ٱلنَّارَۖ وَبِئۡسَ ٱلۡوِرۡدُ ٱلۡمَوۡرُودُ

Zai jagoranci mutanensa ranar alqiyama sai ya shigar da su wuta. Kuma tir da shiga wannan mashiga



Surah: Suratu Hud

Ayah : 99

وَأُتۡبِعُواْ فِي هَٰذِهِۦ لَعۡنَةٗ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ بِئۡسَ ٱلرِّفۡدُ ٱلۡمَرۡفُودُ

Aka kuma bi su da la’ana a wannan (duniyar) da kuma ranar alqiyama. Irin wannan kyauta kuwa da aka yi musu ta munana



Surah: Suratu Hud

Ayah : 100

ذَٰلِكَ مِنۡ أَنۢبَآءِ ٱلۡقُرَىٰ نَقُصُّهُۥ عَلَيۡكَۖ مِنۡهَا قَآئِمٞ وَحَصِيدٞ

Waxannan suna daga labarun alqaryu da Muke labarta maka su; daga cikinsu akwai waxanda suke tsaye da waxanda suke a rushe



Surah: Suratu Hud

Ayah : 101

وَمَا ظَلَمۡنَٰهُمۡ وَلَٰكِن ظَلَمُوٓاْ أَنفُسَهُمۡۖ فَمَآ أَغۡنَتۡ عَنۡهُمۡ ءَالِهَتُهُمُ ٱلَّتِي يَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مِن شَيۡءٖ لَّمَّا جَآءَ أَمۡرُ رَبِّكَۖ وَمَا زَادُوهُمۡ غَيۡرَ تَتۡبِيبٖ

Ba Mu kuwa zalunce su ba, sai dai su ne suka zalunci kansu; allolinsu da suke bauta wa ba Allah ba, ba su maganta musu komai ba, lokacin da umarnin Ubangijinka ya zo; ba su kuwa qara musu komai ba in ban da halaka



Surah: Suratu Hud

Ayah : 102

وَكَذَٰلِكَ أَخۡذُ رَبِّكَ إِذَآ أَخَذَ ٱلۡقُرَىٰ وَهِيَ ظَٰلِمَةٌۚ إِنَّ أَخۡذَهُۥٓ أَلِيمٞ شَدِيدٌ

Haka kuwa damqar Ubangijinka take idan ya damqi alqaryu yayin da suka yi zalunci. Haqiqa damqarsa mai raxaxi ce mai tsanani



Surah: Suratu Hud

Ayah : 103

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّمَنۡ خَافَ عَذَابَ ٱلۡأٓخِرَةِۚ ذَٰلِكَ يَوۡمٞ مَّجۡمُوعٞ لَّهُ ٱلنَّاسُ وَذَٰلِكَ يَوۡمٞ مَّشۡهُودٞ

Lalle game da wannan akwai aya ga wanda ya ji tsoron azabar lahira. Wannan kuwa rana ce da za a tattara mutane a cikinta, kuma wannan rana ce wadda kowa zai halarta



Surah: Suratu Hud

Ayah : 104

وَمَا نُؤَخِّرُهُۥٓ إِلَّا لِأَجَلٖ مَّعۡدُودٖ

Kuma ba ma jinkirta ta sai zuwa lokaci qayyadadde



Surah: Suratu Hud

Ayah : 105

يَوۡمَ يَأۡتِ لَا تَكَلَّمُ نَفۡسٌ إِلَّا بِإِذۡنِهِۦۚ فَمِنۡهُمۡ شَقِيّٞ وَسَعِيدٞ

Ranar da za ta zo ba wani mai rai da zai yi magana sai da izininsa. To daga cikinsu akwai tavavve da kuma mai rabauta



Surah: Suratu Hud

Ayah : 106

فَأَمَّا ٱلَّذِينَ شَقُواْ فَفِي ٱلنَّارِ لَهُمۡ فِيهَا زَفِيرٞ وَشَهِيقٌ

To waxanda suka tave suna cikin wuta suna ta kururuwa da ihu a cikinta



Surah: Suratu Hud

Ayah : 107

خَٰلِدِينَ فِيهَا مَا دَامَتِ ٱلسَّمَٰوَٰتُ وَٱلۡأَرۡضُ إِلَّا مَا شَآءَ رَبُّكَۚ إِنَّ رَبَّكَ فَعَّالٞ لِّمَا يُرِيدُ

Suna madawwama a cikinta matuqar sammai da qasa suna nan a dawwame, sai dai abin da Ubangijinka Ya ga dama. Lalle Ubangijinka Mai yawan aikata abin da Yake nufi ne



Surah: Suratu Hud

Ayah : 108

۞وَأَمَّا ٱلَّذِينَ سُعِدُواْ فَفِي ٱلۡجَنَّةِ خَٰلِدِينَ فِيهَا مَا دَامَتِ ٱلسَّمَٰوَٰتُ وَٱلۡأَرۡضُ إِلَّا مَا شَآءَ رَبُّكَۖ عَطَآءً غَيۡرَ مَجۡذُوذٖ

Amma waxanda aka yi musu dace da rabauta, to suna cikin Aljanna suna masu dawwama a cikinta matuqar sammai da qasa suna nan a dawwame, sai dai abin da Ubangijinka Ya ga dama, (wannan) kyauta ce marar yankewa



Surah: Suratu Hud

Ayah : 109

فَلَا تَكُ فِي مِرۡيَةٖ مِّمَّا يَعۡبُدُ هَـٰٓؤُلَآءِۚ مَا يَعۡبُدُونَ إِلَّا كَمَا يَعۡبُدُ ءَابَآؤُهُم مِّن قَبۡلُۚ وَإِنَّا لَمُوَفُّوهُمۡ نَصِيبَهُمۡ غَيۡرَ مَنقُوصٖ

To kada ka zamo cikin kokwanto dangane da abin da waxannan suke bauta wa. Ba sa bauta sai kamar yadda iyayensu a da can suke bautar. Lalle kuma tabbas za Mu cika musu sakamakonsu ba da tauyewa ba



Surah: Suratu Hud

Ayah : 110

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ فَٱخۡتُلِفَ فِيهِۚ وَلَوۡلَا كَلِمَةٞ سَبَقَتۡ مِن رَّبِّكَ لَقُضِيَ بَيۡنَهُمۡۚ وَإِنَّهُمۡ لَفِي شَكّٖ مِّنۡهُ مُرِيبٖ

Haqiqa kuma Mun bai wa Musa Littafi, sai aka sassava a game da shi. Ba don kuwa wata kalma da ta rigaya daga Ubangijinka ba, to lalle da an yi hukunci a tsakaninsu. Kuma lalle suna cikin matuqar kokwanto game da shi (Alqur’ani)



Surah: Suratu Hud

Ayah : 111

وَإِنَّ كُلّٗا لَّمَّا لَيُوَفِّيَنَّهُمۡ رَبُّكَ أَعۡمَٰلَهُمۡۚ إِنَّهُۥ بِمَا يَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ

Kuma lalle kowannensu tabbas sai Ubangijinka Ya cika musu sakamakon ayyukansu. Lalle Shi Masanin abin da suke aikatawa ne



Surah: Suratu Hud

Ayah : 112

فَٱسۡتَقِمۡ كَمَآ أُمِرۡتَ وَمَن تَابَ مَعَكَ وَلَا تَطۡغَوۡاْۚ إِنَّهُۥ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ

Don haka sai ka tsaya totar kamar yadda aka umarce ka kai da waxanda suka tuba tare da kai, kada kuwa ku wuce iyaka. Lalle Shi (Allah) Mai ganin abin da kuke aikatawa ne



Surah: Suratu Hud

Ayah : 113

وَلَا تَرۡكَنُوٓاْ إِلَى ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ فَتَمَسَّكُمُ ٱلنَّارُ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ مِنۡ أَوۡلِيَآءَ ثُمَّ لَا تُنصَرُونَ

Kuma kada ku karkata zuwa ga waxanda suka yi zalunci, sai wuta ta shafe ku, ba ku kuwa da wasu majivinta lamura ba Allah ba, sannan ba za a taimake ku ba



Surah: Suratu Hud

Ayah : 114

وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ طَرَفَيِ ٱلنَّهَارِ وَزُلَفٗا مِّنَ ٱلَّيۡلِۚ إِنَّ ٱلۡحَسَنَٰتِ يُذۡهِبۡنَ ٱلسَّيِّـَٔاتِۚ ذَٰلِكَ ذِكۡرَىٰ لِلذَّـٰكِرِينَ

Ka kuma tsai da salla farkon rana da qarshenta da kuma farkon dare. Lalle kyawawan (ayyuka) suna shafe munana. Wannan tunasarwa ne ga masu tunawa



Surah: Suratu Hud

Ayah : 115

وَٱصۡبِرۡ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Kuma ka yi haquri, domin lalle Allah ba Ya tozarta ladan masu kyautatawa



Surah: Suratu Hud

Ayah : 116

فَلَوۡلَا كَانَ مِنَ ٱلۡقُرُونِ مِن قَبۡلِكُمۡ أُوْلُواْ بَقِيَّةٖ يَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡفَسَادِ فِي ٱلۡأَرۡضِ إِلَّا قَلِيلٗا مِّمَّنۡ أَنجَيۡنَا مِنۡهُمۡۗ وَٱتَّبَعَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مَآ أُتۡرِفُواْ فِيهِ وَكَانُواْ مُجۡرِمِينَ

Ina ma da a ce an samu mutanen kirki daga tsarekun da suka gabace ku da za su riqa hana yaxuwar varna a bayan qasa? Sai ‘yan kaxan kawai (aka samu) daga waxanda Muka tserar cikinsu. Waxanda kuma suka yi zalunci sai suka bi abin da aka wadata su da shi, suka kuwa zamanto masu laifi



Surah: Suratu Hud

Ayah : 117

وَمَا كَانَ رَبُّكَ لِيُهۡلِكَ ٱلۡقُرَىٰ بِظُلۡمٖ وَأَهۡلُهَا مُصۡلِحُونَ

Kuma Ubangijinka bai kasance mai hallaka alqarya ba da zalunci alhali kuwa mutanenta suna masu gyara



Surah: Suratu Hud

Ayah : 118

وَلَوۡ شَآءَ رَبُّكَ لَجَعَلَ ٱلنَّاسَ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗۖ وَلَا يَزَالُونَ مُخۡتَلِفِينَ

Kuma da Ubangijinka Ya ga dama da lalle Ya yi mutane al’umma xaya (a kan addini xaya). Ba kuwa za su gushe suna masu savawa juna ba



Surah: Suratu Hud

Ayah : 119

إِلَّا مَن رَّحِمَ رَبُّكَۚ وَلِذَٰلِكَ خَلَقَهُمۡۗ وَتَمَّتۡ كَلِمَةُ رَبِّكَ لَأَمۡلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنَ ٱلۡجِنَّةِ وَٱلنَّاسِ أَجۡمَعِينَ

Sai wanda Ubangijinka Ya yi wa rahama. A kan haka kuwa Ya halicce su; kuma Kalmar Ubangijinka ta tabbata (cewa): Lalle zan cika Jahannama da aljannu da mutane baki xaya



Surah: Suratu Hud

Ayah : 120

وَكُلّٗا نَّقُصُّ عَلَيۡكَ مِنۡ أَنۢبَآءِ ٱلرُّسُلِ مَا نُثَبِّتُ بِهِۦ فُؤَادَكَۚ وَجَآءَكَ فِي هَٰذِهِ ٱلۡحَقُّ وَمَوۡعِظَةٞ وَذِكۡرَىٰ لِلۡمُؤۡمِنِينَ

Muna labarta maka kowanne daga labarun manzanni, abin da za Mu kwantar da zuciyarka da shi. Gaskiya kuwa ta zo maka cikin wannan (Surar) da izina da gargaxi ga muminai