ءَآلۡـَٰٔنَ وَقَدۡ عَصَيۡتَ قَبۡلُ وَكُنتَ مِنَ ٱلۡمُفۡسِدِينَ
Sai yanzu kuma, bayan da can ka yi ta savo, ka kuma kasance cikin masu varna?
فَٱلۡيَوۡمَ نُنَجِّيكَ بِبَدَنِكَ لِتَكُونَ لِمَنۡ خَلۡفَكَ ءَايَةٗۚ وَإِنَّ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلنَّاسِ عَنۡ ءَايَٰتِنَا لَغَٰفِلُونَ
To a yau kam za Mu tserar da gangar jikinka don ka zamanto aya ga na bayanka. Lalle kuwa yawancin mutane masu gafala ne ga lura da ayoyinmu
وَلَقَدۡ بَوَّأۡنَا بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ مُبَوَّأَ صِدۡقٖ وَرَزَقۡنَٰهُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِ فَمَا ٱخۡتَلَفُواْ حَتَّىٰ جَآءَهُمُ ٱلۡعِلۡمُۚ إِنَّ رَبَّكَ يَقۡضِي بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فِيمَا كَانُواْ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ
Haqiqa Mun sanya Banu Isra’ila a kyakkyawan matsayi na gaskiya, Muka kuma arzuta su da abubuwa daxaxa na halal, to kawunansu ba su tashi rabuwa ba har sai lokacin da ilimi ya zo musu. Lalle Ubangijinka zai yi hukunci tsakaninsu ranar alqiyama game da abin da suka kasance suna savani a kansa
فَإِن كُنتَ فِي شَكّٖ مِّمَّآ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ فَسۡـَٔلِ ٱلَّذِينَ يَقۡرَءُونَ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلِكَۚ لَقَدۡ جَآءَكَ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُمۡتَرِينَ
To idan kana tababa[1] game da abin da Muka saukar maka to sai ka tambayi waxanda suke karanta littafi gabaninka. Haqiqa gaskiya ta zo maka daga Ubangijinka; to kada ka zama daga cikin masu kokwanto
1- Annabi () ba tava yin tababa ba game da wahayin da Allah () ya yi masa, amma abin nufi a nan shi ne kafa hujja ga Ahlulkitab a kan gaskiyar Annabi ().
وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ فَتَكُونَ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ
Lalle kuma kada ka kasance daga cikin waxanda suka qaryata ayoyin Allah, sai ka zamo daga asararru
إِنَّ ٱلَّذِينَ حَقَّتۡ عَلَيۡهِمۡ كَلِمَتُ رَبِّكَ لَا يُؤۡمِنُونَ
Lalle waxanda kalmar Ubangijinka ta tabbata a kansu (ta zamansu ‘yan wuta) ba za su yi imani ba
وَلَوۡ جَآءَتۡهُمۡ كُلُّ ءَايَةٍ حَتَّىٰ يَرَوُاْ ٱلۡعَذَابَ ٱلۡأَلِيمَ
Ko da kuwa dukkanin ayoyi sun zo musu har sai sun ga azaba mai raxaxi
فَلَوۡلَا كَانَتۡ قَرۡيَةٌ ءَامَنَتۡ فَنَفَعَهَآ إِيمَٰنُهَآ إِلَّا قَوۡمَ يُونُسَ لَمَّآ ءَامَنُواْ كَشَفۡنَا عَنۡهُمۡ عَذَابَ ٱلۡخِزۡيِ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَمَتَّعۡنَٰهُمۡ إِلَىٰ حِينٖ
Babu wasu mutane na wata alqarya da suka yi imani, sannan imaninsu ya amfane su, sai fa mutanen Yunusa, lokacin da suka yi imani sai Muka yaye musu azabar wulaqanci a rayuwar duniya, Muka kuma jiyar da su daxi har zuwa wani lokaci (iyakantacce)
وَلَوۡ شَآءَ رَبُّكَ لَأٓمَنَ مَن فِي ٱلۡأَرۡضِ كُلُّهُمۡ جَمِيعًاۚ أَفَأَنتَ تُكۡرِهُ ٱلنَّاسَ حَتَّىٰ يَكُونُواْ مُؤۡمِنِينَ
Da Ubangijinka Ya ga dama lalle da duk waxanda suke bayan qasa sun yi imani gaba xayansu. Shin kai ne za ka tilasa wa mutane har su zama muminai?
وَمَا كَانَ لِنَفۡسٍ أَن تُؤۡمِنَ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَيَجۡعَلُ ٱلرِّجۡسَ عَلَى ٱلَّذِينَ لَا يَعۡقِلُونَ
Ba zai yiwu wani rai ya yi imani ba sai da izinin Allah. Yana kuma sanya azaba ne a kan waxanda ba sa hankalta
قُلِ ٱنظُرُواْ مَاذَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَمَا تُغۡنِي ٱلۡأٓيَٰتُ وَٱلنُّذُرُ عَن قَوۡمٖ لَّا يُؤۡمِنُونَ
Ka ce: “Ku yi tunanin abubuwan da suke cikin sammai da qasa.” Ayoyi kuwa da masu gargaxi ba sa wadatar da mutanen da ba sa yin imani
فَهَلۡ يَنتَظِرُونَ إِلَّا مِثۡلَ أَيَّامِ ٱلَّذِينَ خَلَوۡاْ مِن قَبۡلِهِمۡۚ قُلۡ فَٱنتَظِرُوٓاْ إِنِّي مَعَكُم مِّنَ ٱلۡمُنتَظِرِينَ
Ai ba abin da suke saurare sai irin azabar da ta sami waxanda suka wuce gabaninsu. Ka ce: “Sai ku saurara, lalle ni ma ina tare da ku cikin masu sauraro.”
ثُمَّ نُنَجِّي رُسُلَنَا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْۚ كَذَٰلِكَ حَقًّا عَلَيۡنَا نُنجِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Sannan Muka riqa tserar da manzanninmu da waxanda suka yi imani da su. Kamar haka ne ya zama lalle a kanmu Mu tserar da muminai
قُلۡ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِن كُنتُمۡ فِي شَكّٖ مِّن دِينِي فَلَآ أَعۡبُدُ ٱلَّذِينَ تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَٰكِنۡ أَعۡبُدُ ٱللَّهَ ٱلَّذِي يَتَوَفَّىٰكُمۡۖ وَأُمِرۡتُ أَنۡ أَكُونَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Ka ce: “Ya ku mutane, idan kun kasance cikin kokwanto game da addinina, to ba zan bauta wa waxanda kuke bauta wa ba Allah ba, sai dai ni zan bauta wa Allah ne wanda Yake karvar rayukanku, an kuma umarce ni da in zama cikin muminai
وَأَنۡ أَقِمۡ وَجۡهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفٗا وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ
“Kuma (an umarce ni) da cewa: ‘Ka tsai da fuskarka ga addinin Allah wanda ya karkace wa varna, kada kuma ka kasance cikin mushirikai
وَلَا تَدۡعُ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُكَ وَلَا يَضُرُّكَۖ فَإِن فَعَلۡتَ فَإِنَّكَ إِذٗا مِّنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ
“Kada kuma ka bauta wa wani ba Allah ba, abin da ba zai amfane ka ba, ba kuma zai cuce ka ba; to idan kuwa ka aikata haka to lalle daga sannan ka zama cikin azzalumai.’”
وَإِن يَمۡسَسۡكَ ٱللَّهُ بِضُرّٖ فَلَا كَاشِفَ لَهُۥٓ إِلَّا هُوَۖ وَإِن يُرِدۡكَ بِخَيۡرٖ فَلَا رَآدَّ لِفَضۡلِهِۦۚ يُصِيبُ بِهِۦ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۚ وَهُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ
Idan Allah Ya xora maka wata cuta to ba mai yaye maka ita sai shi; idan kuma Ya nufe ka da alheri to ba mai juyar da falalarsa. Yana bayar da shi ga waxanda Ya ga dama daga bayinsa. Shi ne kuma Mai gafara, Mai jin qai
قُلۡ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ قَدۡ جَآءَكُمُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكُمۡۖ فَمَنِ ٱهۡتَدَىٰ فَإِنَّمَا يَهۡتَدِي لِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيۡهَاۖ وَمَآ أَنَا۠ عَلَيۡكُم بِوَكِيلٖ
Ka ce: “Ya ku mutane, haqiqa gaskiya ta zo muku daga Ubangijinku; duk wanda ya shiriya to ya shiriya ne don kansa; wanda kuma ya vace to lalle ya vace don kansa ne; ni kuwa ba wakili ne a kanku ba.”
وَٱتَّبِعۡ مَا يُوحَىٰٓ إِلَيۡكَ وَٱصۡبِرۡ حَتَّىٰ يَحۡكُمَ ٱللَّهُۚ وَهُوَ خَيۡرُ ٱلۡحَٰكِمِينَ
Kuma ka bi abin da aka yi maka wahayinsa, ka kuma yi haquri har sai Allah Ya yi hukunci. Shi ne kuwa Fiyayyen masu hukunci