Surah: Suratu Yasin

Ayah : 61

وَأَنِ ٱعۡبُدُونِيۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ

Kuma ku bauta min. Wannan shi ne tafarki madaidaici



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 62

وَلَقَدۡ أَضَلَّ مِنكُمۡ جِبِلّٗا كَثِيرًاۖ أَفَلَمۡ تَكُونُواْ تَعۡقِلُونَ

Haqiqa kuma (Shaixan) ya vatar da halittu masu yawa; shin ba za ku hankalta ba?



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 63

هَٰذِهِۦ جَهَنَّمُ ٱلَّتِي كُنتُمۡ تُوعَدُونَ

Wannan ita ce Jahannamar da ta kasance ana yi muku alqawarinta



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 64

ٱصۡلَوۡهَا ٱلۡيَوۡمَ بِمَا كُنتُمۡ تَكۡفُرُونَ

Ku shige ta a yau saboda kafircin da kuke yi



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 65

ٱلۡيَوۡمَ نَخۡتِمُ عَلَىٰٓ أَفۡوَٰهِهِمۡ وَتُكَلِّمُنَآ أَيۡدِيهِمۡ وَتَشۡهَدُ أَرۡجُلُهُم بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ

A yau za Mu toshe bakunansu, hannayensu su yi mana magana, qafafuwansu kuma su ba da shaidar irin abin da suka kasance suna aikatawa



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 66

وَلَوۡ نَشَآءُ لَطَمَسۡنَا عَلَىٰٓ أَعۡيُنِهِمۡ فَٱسۡتَبَقُواْ ٱلصِّرَٰطَ فَأَنَّىٰ يُبۡصِرُونَ

Da kuma Mun ga dama da sai Mu shafe idanuwansu su riqa rige-rigen hawan siraxi, to ta yaya za su iya gani (a wannan lokaci)[1]?


1- Watau a shafe idanunsu su daina ganin komai, sannan a umarce su da su yi rige-rigen hawan siraxi zuwa Aljanna, amma ina!


Surah: Suratu Yasin

Ayah : 67

وَلَوۡ نَشَآءُ لَمَسَخۡنَٰهُمۡ عَلَىٰ مَكَانَتِهِمۡ فَمَا ٱسۡتَطَٰعُواْ مُضِيّٗا وَلَا يَرۡجِعُونَ

Da kuma Mun ga dama da sai Mu jirkita halittarsu a inda suke, saboda haka ba za su iya ci gaba da tafiya ba, ba kuma za su iya dawowa ba[1]


1- Watau ya jirkita halittarsu ya mayar da su sandararru; ba za su iya yin gaba ba ko baya.


Surah: Suratu Yasin

Ayah : 68

وَمَن نُّعَمِّرۡهُ نُنَكِّسۡهُ فِي ٱلۡخَلۡقِۚ أَفَلَا يَعۡقِلُونَ

Wanda kuma Muka tsawaita rayuwarsa, za Mu mayar da halittarsa baya[1]; me ya sa ne ba sa hankalta?


1- Watau ya koma ya yi rauni na jiki da na qwaqwalwa.


Surah: Suratu Yasin

Ayah : 69

وَمَا عَلَّمۡنَٰهُ ٱلشِّعۡرَ وَمَا يَنۢبَغِي لَهُۥٓۚ إِنۡ هُوَ إِلَّا ذِكۡرٞ وَقُرۡءَانٞ مُّبِينٞ

Ba Mu kuma koyar da shi (Muhammadu) waqa ba, kuma ba za ta yiwu ba gare shi. (Abin da ya zo da shi) ba wani abu ba ne sai wa’azi da kuma Alqur’ani mabayyani



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 70

لِّيُنذِرَ مَن كَانَ حَيّٗا وَيَحِقَّ ٱلۡقَوۡلُ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ

Don ya gargaxi wanda ya kasance rayayye (wato mumini), azaba kuma ta tabbata a kan kafirai



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 71

أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّا خَلَقۡنَا لَهُم مِّمَّا عَمِلَتۡ أَيۡدِينَآ أَنۡعَٰمٗا فَهُمۡ لَهَا مَٰلِكُونَ

Yanzu ba sa gani ne cewa Mu Muka halitta musu dabbobin ni’ima daga abin da hannanyenmu suka aikata, sai ga su suna mallakar su?



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 72

وَذَلَّلۡنَٰهَا لَهُمۡ فَمِنۡهَا رَكُوبُهُمۡ وَمِنۡهَا يَأۡكُلُونَ

Muka kuma hore musu su, don haka ababen hawansu daga cikinsu ne, kuma daga gare su suke ci



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 73

وَلَهُمۡ فِيهَا مَنَٰفِعُ وَمَشَارِبُۚ أَفَلَا يَشۡكُرُونَ

Suna kuma da wata moriya da abin sha daga gare su. Yanzu ba za su riqa godiya ba?



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 74

وَٱتَّخَذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ ءَالِهَةٗ لَّعَلَّهُمۡ يُنصَرُونَ

Suka kuma riqi wasu ababen bauta ba Allah ba, don a taimaka musu



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 75

لَا يَسۡتَطِيعُونَ نَصۡرَهُمۡ وَهُمۡ لَهُمۡ جُندٞ مُّحۡضَرُونَ

Ba za su iya taimakon su ba, su da gumakan nasu duka ababen tattarawa ne (cikin wuta)



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 76

فَلَا يَحۡزُنكَ قَوۡلُهُمۡۘ إِنَّا نَعۡلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعۡلِنُونَ

To kada maganarsu ta baqanta maka. Lalle Mu Muna sane da abin da suke voyewa da kuma abin da suke bayyanawa



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 77

أَوَلَمۡ يَرَ ٱلۡإِنسَٰنُ أَنَّا خَلَقۡنَٰهُ مِن نُّطۡفَةٖ فَإِذَا هُوَ خَصِيمٞ مُّبِينٞ

Yanzu mutum ba ya gani cewa Mu Muka halicce shi daga maniyyi, sai ga shi ya zama mai jayayya a fili?



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 78

وَضَرَبَ لَنَا مَثَلٗا وَنَسِيَ خَلۡقَهُۥۖ قَالَ مَن يُحۡيِ ٱلۡعِظَٰمَ وَهِيَ رَمِيمٞ

Ya kuma buga mana misali, kuma ya manta da halittarsa (yayin da) ya ce: “Wane ne zai raya qasusuwa, alhali kuma sun rududduge?



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 79

قُلۡ يُحۡيِيهَا ٱلَّذِيٓ أَنشَأَهَآ أَوَّلَ مَرَّةٖۖ وَهُوَ بِكُلِّ خَلۡقٍ عَلِيمٌ

Ka ce: “Wannan da Ya fare su tun farko Shi ne zai raya su; Shi kuwa Masanin kowacce irin halitta ne



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 80

ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُم مِّنَ ٱلشَّجَرِ ٱلۡأَخۡضَرِ نَارٗا فَإِذَآ أَنتُم مِّنۡهُ تُوقِدُونَ

“Wanda kuma Ya samar muku wuta daga koriyar bishiya, sai ga shi kuna hura wuta daga gare ta.”



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 81

أَوَلَيۡسَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِقَٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يَخۡلُقَ مِثۡلَهُمۚ بَلَىٰ وَهُوَ ٱلۡخَلَّـٰقُ ٱلۡعَلِيمُ

Yanzu wanda Ya halacci sammai da qasa ba zai zama Mai ikon halitta irinsu ba? Ai tabbas zai iya, kuma Shi ne Mai yawan yin halitta, Masani



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 82

إِنَّمَآ أَمۡرُهُۥٓ إِذَآ أَرَادَ شَيۡـًٔا أَن يَقُولَ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ

Umarninsa kawai idan Ya yi nufin wani abu sai Ya ce da shi: “Kasance”, sai ya kasance



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 83

فَسُبۡحَٰنَ ٱلَّذِي بِيَدِهِۦ مَلَكُوتُ كُلِّ شَيۡءٖ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

To tsarki ya tabbata ga wanda mulkin kowane abu yake a hannunsa, kuma wurinsa ne kawai za a komar da ku