Surah: Suratul Baqara

Ayah : 61

وَإِذۡ قُلۡتُمۡ يَٰمُوسَىٰ لَن نَّصۡبِرَ عَلَىٰ طَعَامٖ وَٰحِدٖ فَٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ يُخۡرِجۡ لَنَا مِمَّا تُنۢبِتُ ٱلۡأَرۡضُ مِنۢ بَقۡلِهَا وَقِثَّآئِهَا وَفُومِهَا وَعَدَسِهَا وَبَصَلِهَاۖ قَالَ أَتَسۡتَبۡدِلُونَ ٱلَّذِي هُوَ أَدۡنَىٰ بِٱلَّذِي هُوَ خَيۡرٌۚ ٱهۡبِطُواْ مِصۡرٗا فَإِنَّ لَكُم مَّا سَأَلۡتُمۡۗ وَضُرِبَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلذِّلَّةُ وَٱلۡمَسۡكَنَةُ وَبَآءُو بِغَضَبٖ مِّنَ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَانُواْ يَكۡفُرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَيَقۡتُلُونَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّۚ ذَٰلِكَ بِمَا عَصَواْ وَّكَانُواْ يَعۡتَدُونَ

Kuma ku tuna lokacin da kuka ce: “Ya Musa, ba za mu iya haquri a kan abinci iri xaya ba, don haka ka roqa mana Ubangijinka Ya fitar mana (wani abincin) daga abin da qasa take tsirarwa, daga mabunqusanta da gurjinta da alkamarta da wakenta da albasarta.” Sai ya ce, “Yanzu kwa nemi musanya qasqantaccen abu da wanda yake shi ne mafifici? To ku sauka kowane gari, domin za ku samu abin da kuka roqa (a cikinsa).” Don haka sai aka sanya musu qasqanci da talauci, kuma suka koma da fushin Allah. Hakan ya faru gare su ne saboda sun kasance suna kafirce wa ayoyin Allah, kuma suna kashe annabawa ba tare da wani haqqi ba. Hakan ya faru saboda savon da suka yi da kuma ta’addancin da suka riqa yi



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 62

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَٱلَّذِينَ هَادُواْ وَٱلنَّصَٰرَىٰ وَٱلصَّـٰبِـِٔينَ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَلَهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ وَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

Lalle waxanda suka yi imani da Yahudawa da Nasara da Sabi’awa[1], duk wanda ya yi imani da Allah da ranar Lahira kuma ya yi aiki na qwarai, to suna da ladansu a wurin Ubangijinsu, kuma babu tsoro a tare da su, kuma ba za su yi baqin ciki ba


1- Waxanda suka yi imani, su ne al’ummar Annabi Muhammadu (). Yahudawa, ana nufin mabiya Annabi Musa () kafin a shafe addininsa, ko kafin su gurvata shi. Nasara, ana nufin mabiya Annabi Isa () kafin a shafe addininsa ko kafin su gurvata shi. Sabi’awa, wasu qungiyoyi ne, daga cikinsu akwai masu aqidar kaxaita Allah da haramta duk wata alfasha da zalunci, duk da kasancewarsu ba bisa wani addini suke ba, to amma ba sa aikata shirka.


Surah: Suratul Baqara

Ayah : 63

وَإِذۡ أَخَذۡنَا مِيثَٰقَكُمۡ وَرَفَعۡنَا فَوۡقَكُمُ ٱلطُّورَ خُذُواْ مَآ ءَاتَيۡنَٰكُم بِقُوَّةٖ وَٱذۡكُرُواْ مَا فِيهِ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ

Kuma ku tuna lokacin da Muka xauki alqawari mai qarfi daga gare ku, kuma Muka xaga dusten Xuri a kanku (Muka ce): “Ku karvi abin da Muka ba ku da qarfi (Attaura), kuma ku tuna abin da yake cikinsa, don ku yi taqawa.”



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 64

ثُمَّ تَوَلَّيۡتُم مِّنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَۖ فَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ لَكُنتُم مِّنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

Sannan bayan haka sai kuka juya da baya, to ba domin falalar Allah da rahamarsa a gare ku ba, lalle da kun kasance daga cikin asararru



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 65

وَلَقَدۡ عَلِمۡتُمُ ٱلَّذِينَ ٱعۡتَدَوۡاْ مِنكُمۡ فِي ٱلسَّبۡتِ فَقُلۡنَا لَهُمۡ كُونُواْ قِرَدَةً خَٰسِـِٔينَ

Kuma haqiqa kun san waxanda suka yi shisshigi daga cikinku game da ranar Assabar, sai Muka ce da su: “Ku zama birrai kuna qasqantattu.”



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 66

فَجَعَلۡنَٰهَا نَكَٰلٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهَا وَمَا خَلۡفَهَا وَمَوۡعِظَةٗ لِّلۡمُتَّقِينَ

Sai Muka sanya ta (wannan uqubar) ta zama izina ga (al’ummomin) da suke zamanin faruwarta da kuma (garuruwan) da suke daura da su, kuma don ta zama wa’azi ga masu taqawa



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 67

وَإِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِۦٓ إِنَّ ٱللَّهَ يَأۡمُرُكُمۡ أَن تَذۡبَحُواْ بَقَرَةٗۖ قَالُوٓاْ أَتَتَّخِذُنَا هُزُوٗاۖ قَالَ أَعُوذُ بِٱللَّهِ أَنۡ أَكُونَ مِنَ ٱلۡجَٰهِلِينَ

Kuma ku tuna lokacin da Musa ya ce wa mutanensa: “Allah Yana umartar ku da ku yanka saniya”, sai suka ce: “Yanzu ka riqa yi mana izgili?” Sai ya ce: “Ina neman Allah Ya kiyaye ni da in zama cikin jahilai!”



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 68

قَالُواْ ٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ يُبَيِّن لَّنَا مَا هِيَۚ قَالَ إِنَّهُۥ يَقُولُ إِنَّهَا بَقَرَةٞ لَّا فَارِضٞ وَلَا بِكۡرٌ عَوَانُۢ بَيۡنَ ذَٰلِكَۖ فَٱفۡعَلُواْ مَا تُؤۡمَرُونَ

Sai suka ce: “Ka roqa mana Ubangijinka Ya yi mana bayanin yaya take?” Sai ya ce: “Lalle Shi Yana cewa, lalle ita saniya ce, ba tsohuwa ba kuma ba budurwa ba, tana tsakatsakin haka.” Don haka ku aikata abin da ake umartar ku



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 69

قَالُواْ ٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ يُبَيِّن لَّنَا مَا لَوۡنُهَاۚ قَالَ إِنَّهُۥ يَقُولُ إِنَّهَا بَقَرَةٞ صَفۡرَآءُ فَاقِعٞ لَّوۡنُهَا تَسُرُّ ٱلنَّـٰظِرِينَ

Sai suka ce: “Ka roqa mana Ubangijinka Ya bayyana mana mene ne launinta?” Sai ya ce, “Lalle Shi Yana cewa, lalle ita saniya ce mai launin fatsi-fatsi mai tsananin cizawa, tana faranta wa masu kallon ta rai.”



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 70

قَالُواْ ٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ يُبَيِّن لَّنَا مَا هِيَ إِنَّ ٱلۡبَقَرَ تَشَٰبَهَ عَلَيۡنَا وَإِنَّآ إِن شَآءَ ٱللَّهُ لَمُهۡتَدُونَ

Sai suka ce: “Ka roqa mana Ubangijinka Ya bayyana mana yaya take, lalle shanu sun rikitar da mu, kuma lalle mu, insha Allahu masu shiryuwa ne.”



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 71

قَالَ إِنَّهُۥ يَقُولُ إِنَّهَا بَقَرَةٞ لَّا ذَلُولٞ تُثِيرُ ٱلۡأَرۡضَ وَلَا تَسۡقِي ٱلۡحَرۡثَ مُسَلَّمَةٞ لَّا شِيَةَ فِيهَاۚ قَالُواْ ٱلۡـَٰٔنَ جِئۡتَ بِٱلۡحَقِّۚ فَذَبَحُوهَا وَمَا كَادُواْ يَفۡعَلُونَ

Ya ce: “Lalle Shi Yana cewa, ita saniya ce wadda ba horarriya ba ce da take noma kasa, kuma ba ta shayar da shuka; lafiyayya ce, babu dabbare-dabbare a jikinta”. Sai suka ce: “Yanzu ne ka zo da gaskiya”. Sai suka yanka ta, kamar dai ba za su aikata ba



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 72

وَإِذۡ قَتَلۡتُمۡ نَفۡسٗا فَٱدَّـٰرَٰٔتُمۡ فِيهَاۖ وَٱللَّهُ مُخۡرِجٞ مَّا كُنتُمۡ تَكۡتُمُونَ

Kuma ku tuna lokacin da kuka kashe wani mutum, kuma kuka riqa tura wa juna (laifin kisan), Allah kuma Mai bayyanar da abin da kuka kasance kuna voyewa ne



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 73

فَقُلۡنَا ٱضۡرِبُوهُ بِبَعۡضِهَاۚ كَذَٰلِكَ يُحۡيِ ٱللَّهُ ٱلۡمَوۡتَىٰ وَيُرِيكُمۡ ءَايَٰتِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ

Sai Muka ce: “Ku doke shi (mataccen) da wani sashinta (saniyar).”[1] Kamar haka ne Allah Yake raya matattu, Yake kuma nuna muku ayoyinsa don ku hankalta


1- Sai Allah ya sake raya shi, ya tashi ya faxa musu sunan wanda ya kashe shi.


Surah: Suratul Baqara

Ayah : 74

ثُمَّ قَسَتۡ قُلُوبُكُم مِّنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ فَهِيَ كَٱلۡحِجَارَةِ أَوۡ أَشَدُّ قَسۡوَةٗۚ وَإِنَّ مِنَ ٱلۡحِجَارَةِ لَمَا يَتَفَجَّرُ مِنۡهُ ٱلۡأَنۡهَٰرُۚ وَإِنَّ مِنۡهَا لَمَا يَشَّقَّقُ فَيَخۡرُجُ مِنۡهُ ٱلۡمَآءُۚ وَإِنَّ مِنۡهَا لَمَا يَهۡبِطُ مِنۡ خَشۡيَةِ ٱللَّهِۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ

Sannan sai zukatanku suka qeqashe bayan haka, suka zama kamar dutse ko ma fiye da dutse qeqashewa. Kuma lalle daga cikin duwatsu akwai waxanda qoramu suke vuvvugowa daga cikinsu; akwai kuma waxanda suke tsattsagewa ruwa ya fito daga cikinsu; akwai kuma waxanda suke faxowa saboda tsoron Allah. Allah ba marafkani ne ba game da abin da kuke aikatawa



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 75

۞أَفَتَطۡمَعُونَ أَن يُؤۡمِنُواْ لَكُمۡ وَقَدۡ كَانَ فَرِيقٞ مِّنۡهُمۡ يَسۡمَعُونَ كَلَٰمَ ٱللَّهِ ثُمَّ يُحَرِّفُونَهُۥ مِنۢ بَعۡدِ مَا عَقَلُوهُ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ

Yanzu (ku muminai) kwa sa ran su yi imani saboda ku, alhalin wata qungiya daga cikinsu suna sauraron maganar Allah sannan su jirkita ta bayan sun fahimce ta alhalin kuwa suna sane?



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 76

وَإِذَا لَقُواْ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ قَالُوٓاْ ءَامَنَّا وَإِذَا خَلَا بَعۡضُهُمۡ إِلَىٰ بَعۡضٖ قَالُوٓاْ أَتُحَدِّثُونَهُم بِمَا فَتَحَ ٱللَّهُ عَلَيۡكُمۡ لِيُحَآجُّوكُم بِهِۦ عِندَ رَبِّكُمۡۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ

Kuma idan suka haxu da waxanda suka yi imani sai su ce: “Mun yi imani”, amma kuma idan sashinsu ya kevance da sashi sai su ce: “Yanzu kwa riqa faxa musu abin da Allah Ya yi muku buxi da shi don su kafa muku hujja da shi a wurin Ubangijinku? Shin ba za ku hankalta ba?”



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 77

أَوَلَا يَعۡلَمُونَ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعۡلِنُونَ

Shin ko ba su san Allah Yana sane da abin da suke voyewa da abin da suke bayyanawa ba?



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 78

وَمِنۡهُمۡ أُمِّيُّونَ لَا يَعۡلَمُونَ ٱلۡكِتَٰبَ إِلَّآ أَمَانِيَّ وَإِنۡ هُمۡ إِلَّا يَظُنُّونَ

Kuma daga cikinsu akwai jahilai waxanda ba su san Littafi ba sai burace-burace, kuma zato kawai suke yi



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 79

فَوَيۡلٞ لِّلَّذِينَ يَكۡتُبُونَ ٱلۡكِتَٰبَ بِأَيۡدِيهِمۡ ثُمَّ يَقُولُونَ هَٰذَا مِنۡ عِندِ ٱللَّهِ لِيَشۡتَرُواْ بِهِۦ ثَمَنٗا قَلِيلٗاۖ فَوَيۡلٞ لَّهُم مِّمَّا كَتَبَتۡ أَيۡدِيهِمۡ وَوَيۡلٞ لَّهُم مِّمَّا يَكۡسِبُونَ

To tsananin azaba ya tabbata ga waxanda suke rubuta littafi da hannayensu sannan su ce: “Wannan daga Allah yake”, don su musanya shi da wani xan kuxi kaxan. To tsananin azaba ya tabbata a gare su saboda abin da hannayensu suka rubuta, kuma tsananin azaba ya tabbata a gare su saboda abin da suka kasance suna tsuwurwuta



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 80

وَقَالُواْ لَن تَمَسَّنَا ٱلنَّارُ إِلَّآ أَيَّامٗا مَّعۡدُودَةٗۚ قُلۡ أَتَّخَذۡتُمۡ عِندَ ٱللَّهِ عَهۡدٗا فَلَن يُخۡلِفَ ٱللَّهُ عَهۡدَهُۥٓۖ أَمۡ تَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ

Kuma suka ce: “Wuta ba za ta shafe mu ba sai cikin wasu ‘yan kwanaki qididdigaggu.” Ka ce: “Shin kun yi wani alqawari ne da Allah, don haka Allah ba zai sava alqawarinsa ba? Ko kuma kuna faxar abin da ba ku da ilimi ne kuna jingina wa Allah?”



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 81

بَلَىٰۚ مَن كَسَبَ سَيِّئَةٗ وَأَحَٰطَتۡ بِهِۦ خَطِيٓـَٔتُهُۥ فَأُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

E! Wanda duk ya aikata mummunan aiki kuma laifuffukansa suka kewaye shi, to waxannan su ne ‘yan wuta, su masu dawwama ne a cikinta



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 82

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Waxanda kuma suka yi imani kuma suka yi ayyuka na qwarai, to waxannan ‘yan Aljanna ne, kuma su masu dawwama ne a cikinta



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 83

وَإِذۡ أَخَذۡنَا مِيثَٰقَ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ لَا تَعۡبُدُونَ إِلَّا ٱللَّهَ وَبِٱلۡوَٰلِدَيۡنِ إِحۡسَانٗا وَذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَقُولُواْ لِلنَّاسِ حُسۡنٗا وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ ثُمَّ تَوَلَّيۡتُمۡ إِلَّا قَلِيلٗا مِّنكُمۡ وَأَنتُم مُّعۡرِضُونَ

Kuma ka tuna lokacin da Muka xauki alqwari daga Banu Isra’ila cewa, ba za ku bauta wa kowa ba sai Allah, kuma za ku kyautata wa iyaye da makusanta da marayu da miskinai, kuma ku riqa yi wa mutane kyakkyawar magana, kuma ku tsai da salla, kuma ku ba da zakka, sannan sai kuka ba da baya sai ‘yan kaxan daga cikinku, alhalin kuna masu bijirewa



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 84

وَإِذۡ أَخَذۡنَا مِيثَٰقَكُمۡ لَا تَسۡفِكُونَ دِمَآءَكُمۡ وَلَا تُخۡرِجُونَ أَنفُسَكُم مِّن دِيَٰرِكُمۡ ثُمَّ أَقۡرَرۡتُمۡ وَأَنتُمۡ تَشۡهَدُونَ

Kuma ku tuna lokacin da Muka xauki alqawari da ku cewa, ba za ku zubar da jinanenku ba, kuma ba za ku fitar da junanku daga gidajenku ba, sannan kuka tabbatar da hakan, alhalin kuna masu shaida



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 85

ثُمَّ أَنتُمۡ هَـٰٓؤُلَآءِ تَقۡتُلُونَ أَنفُسَكُمۡ وَتُخۡرِجُونَ فَرِيقٗا مِّنكُم مِّن دِيَٰرِهِمۡ تَظَٰهَرُونَ عَلَيۡهِم بِٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَٰنِ وَإِن يَأۡتُوكُمۡ أُسَٰرَىٰ تُفَٰدُوهُمۡ وَهُوَ مُحَرَّمٌ عَلَيۡكُمۡ إِخۡرَاجُهُمۡۚ أَفَتُؤۡمِنُونَ بِبَعۡضِ ٱلۡكِتَٰبِ وَتَكۡفُرُونَ بِبَعۡضٖۚ فَمَا جَزَآءُ مَن يَفۡعَلُ ذَٰلِكَ مِنكُمۡ إِلَّا خِزۡيٞ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ يُرَدُّونَ إِلَىٰٓ أَشَدِّ ٱلۡعَذَابِۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ

Sannan sai ga ku, ku xin nan kuna kashe junanku, kuma kuna fitar da wata qungiya daga cikinku daga gidajensu, kuma kuna taimaka wa juna wajen cutar da su ta hanyar laifi da zalunci. Idan kuma sun zo muku suna kamammun yaqi sai ku fanshe su, alhali fitar da su haramun ne a gare ku. Yanzu kwa riqa yin imani da sashen Littafi kuma ku riqa kafircewa da wani sashen? To ba komai ne sakamakon wanda yake aikata haka daga cikinku ba face wani wulaqanci a rayuwar duniya, kuma ranar alqiyama a mayar da su zuwa ga mafi tsananin azaba, kuma Allah ba rafkananne ba ne game da abin da kuke aikatawa



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 86

أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ ٱشۡتَرَوُاْ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا بِٱلۡأٓخِرَةِۖ فَلَا يُخَفَّفُ عَنۡهُمُ ٱلۡعَذَابُ وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ

Waxannan su ne waxanda suka musanya rayuwar duniya da ta lahira, kuma ba za a sassauta musu azaba ba, kuma ba za a taimaka musu ba



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 87

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ وَقَفَّيۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِۦ بِٱلرُّسُلِۖ وَءَاتَيۡنَا عِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ ٱلۡبَيِّنَٰتِ وَأَيَّدۡنَٰهُ بِرُوحِ ٱلۡقُدُسِۗ أَفَكُلَّمَا جَآءَكُمۡ رَسُولُۢ بِمَا لَا تَهۡوَىٰٓ أَنفُسُكُمُ ٱسۡتَكۡبَرۡتُمۡ فَفَرِيقٗا كَذَّبۡتُمۡ وَفَرِيقٗا تَقۡتُلُونَ

Kuma haqiqa Mun ba wa Musa Littafi, kuma Muka biyo bayansa da manzanni, kuma Mun bai wa Isa xan Maryam hujjoji bayyananu, kuma Mun qarfafe shi da Ruhi mai tsarki. Ashe yanzu duk sa’adda wani manzo ya zo muku da abin da zukatanku ba sa so, sai ku yi girman kai, don haka sai ku qaryata wasu, kuma ku kashe wasu?



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 88

وَقَالُواْ قُلُوبُنَا غُلۡفُۢۚ بَل لَّعَنَهُمُ ٱللَّهُ بِكُفۡرِهِمۡ فَقَلِيلٗا مَّا يُؤۡمِنُونَ

Suka ce kuma: “Zukatanmu rufaffu ne.” A’a ba haka ba ne, Allah dai Ya la’ane su ne saboda kafircinsu, don haka kaxan ne waxanda suke yin imani



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 89

وَلَمَّا جَآءَهُمۡ كِتَٰبٞ مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِ مُصَدِّقٞ لِّمَا مَعَهُمۡ وَكَانُواْ مِن قَبۡلُ يَسۡتَفۡتِحُونَ عَلَى ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَلَمَّا جَآءَهُم مَّا عَرَفُواْ كَفَرُواْ بِهِۦۚ فَلَعۡنَةُ ٱللَّهِ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ

Yayin da kuma wani littafi ya zo musu daga Allah, yana mai gaskata abin da yake tare da su, alhali kuma a da sun kasance suna addu’ar neman nasara a kan waxanda suka kafirta (mushrikai). To yayin da abin da suka sani ya zo musu sai suka kafirce masa[1]. Don haka la’anar Allah ta tabbata a kan kafirai


1- Kafin aiko Annabi Muhammadu (), idan faxa ya varke tsaknin Yahudu da Larabawa, Yahudu sukan ce, za a aiko wani annabi, idan ya bayyana za mu bi shi, mu haxa qarfi da shi mu yaqe ku. Yayin da Annabi () ya bayyana ba a cikinsu ba sai suka kafirce masa.


Surah: Suratul Baqara

Ayah : 90

بِئۡسَمَا ٱشۡتَرَوۡاْ بِهِۦٓ أَنفُسَهُمۡ أَن يَكۡفُرُواْ بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بَغۡيًا أَن يُنَزِّلَ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۖ فَبَآءُو بِغَضَبٍ عَلَىٰ غَضَبٖۚ وَلِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٞ مُّهِينٞ

Tir da wannan abu da suka sayar da kawunansu da shi, wato suka kafirce wa abin da Allah Ya saukar, don hassadar cewa, (don me) Allah zai saukar da falalarsa ga wanda Ya ga dama daga bayinsa, sai suka wayi gari da fushin Allah a kan wani fushin. Kuma azaba ta wulaqanci ta tabbata ga kafirai