وَلِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ لِيَجۡزِيَ ٱلَّذِينَ أَسَـٰٓـُٔواْ بِمَا عَمِلُواْ وَيَجۡزِيَ ٱلَّذِينَ أَحۡسَنُواْ بِٱلۡحُسۡنَى
Kuma abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa na Allah ne, don Ya saka wa waxanda suka munana da irin abin da suka aikata, Ya kuma saka wa waxanda suka kyautata da mafi kyan sakamako
ٱلَّذِينَ يَجۡتَنِبُونَ كَبَـٰٓئِرَ ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡفَوَٰحِشَ إِلَّا ٱللَّمَمَۚ إِنَّ رَبَّكَ وَٰسِعُ ٱلۡمَغۡفِرَةِۚ هُوَ أَعۡلَمُ بِكُمۡ إِذۡ أَنشَأَكُم مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ وَإِذۡ أَنتُمۡ أَجِنَّةٞ فِي بُطُونِ أُمَّهَٰتِكُمۡۖ فَلَا تُزَكُّوٓاْ أَنفُسَكُمۡۖ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَنِ ٱتَّقَىٰٓ
(Su ne) waxanda suke nisantar manya-manyan zunubai da munanan ayyukan savo, sai dai ‘yan qananan zunubai. Lalle Ubangijinka Mayalwacin gafara ne. Shi ne Ya fi sanin ku, tun sanda Ya halicce ku daga qasa, sai ga ku kun zama ‘yan tayi a cikin cikin iyayenku mata; to kada ku tsarkake kanku; Shi ne Ya fi sanin wanda ya fi taqawa
أَفَرَءَيۡتَ ٱلَّذِي تَوَلَّىٰ
Ka ba ni labarin wanda ya ba da baya
وَأَعۡطَىٰ قَلِيلٗا وَأَكۡدَىٰٓ
Ya kuma bayar da dukiya kaxan kuma ya yi rowa
أَعِندَهُۥ عِلۡمُ ٱلۡغَيۡبِ فَهُوَ يَرَىٰٓ
Shin yana da ilimin gaibu ne don haka yana ganin (komai)?
أَمۡ لَمۡ يُنَبَّأۡ بِمَا فِي صُحُفِ مُوسَىٰ
Ko ba a ba shi labarin abin da yake cikin takardun Musa ba ne?
وَإِبۡرَٰهِيمَ ٱلَّذِي وَفَّىٰٓ
Da kuma Ibrahimu wanda ya cika alqawari?
أَلَّا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰ
Cewa: “Wani rai ba ya xaukar nauyin laifin wani
وَأَن لَّيۡسَ لِلۡإِنسَٰنِ إِلَّا مَا سَعَىٰ
“Kuma mutum bai mallaki wani sakamako ba sai na abin da ya aikata
وَأَنَّ سَعۡيَهُۥ سَوۡفَ يُرَىٰ
“Kuma lalle aikin nasa ba da daxewa ba za a gan shi
ثُمَّ يُجۡزَىٰهُ ٱلۡجَزَآءَ ٱلۡأَوۡفَىٰ
“Sannan a saka masa da cikakken sakamako
وَأَنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلۡمُنتَهَىٰ
“Lalle kuma zuwa ga Ubangijinka ne makoma
وَأَنَّهُۥ هُوَ أَضۡحَكَ وَأَبۡكَىٰ
“Kuma lalle Shi ne Ya sa a yi dariya, kuma Ya sa a yi kuka
وَأَنَّهُۥ هُوَ أَمَاتَ وَأَحۡيَا
“Kuma lalle Shi ne Ya kashe kuma Ya raya
وَأَنَّهُۥ خَلَقَ ٱلزَّوۡجَيۡنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰ
“Kuma lalle Shi ne Ya halicci dangi biyu namiji da mace
مِن نُّطۡفَةٍ إِذَا تُمۡنَىٰ
“Daga maniyyi yayin da ake zuba shi
وَأَنَّ عَلَيۡهِ ٱلنَّشۡأَةَ ٱلۡأُخۡرَىٰ
“Kuma lalle Ya xora wa kansa sake tashin matattu
وَأَنَّهُۥ هُوَ أَغۡنَىٰ وَأَقۡنَىٰ
“Lalle kuma Shi ne Ya wadata, Ya kuma yalwata
وَأَنَّهُۥ هُوَ رَبُّ ٱلشِّعۡرَىٰ
“Kuma lalle Shi ne Ubangijin tauraron nan Shi’ira
وَأَنَّهُۥٓ أَهۡلَكَ عَادًا ٱلۡأُولَىٰ
“Lalle kuma Ya hallakar da Adawa na farko
وَثَمُودَاْ فَمَآ أَبۡقَىٰ
“Da kuma Samudawa, don haka bai bar saura ba
وَقَوۡمَ نُوحٖ مِّن قَبۡلُۖ إِنَّهُمۡ كَانُواْ هُمۡ أَظۡلَمَ وَأَطۡغَىٰ
“Da mutanen Nuhu tun kafin su; lalle su sun kasance su ne mafiya zalunci kuma mafiya xagawa
وَٱلۡمُؤۡتَفِكَةَ أَهۡوَىٰ
“Da waxanda aka kife (mutanen Luxu, Allah) ya qasqanta su
فَغَشَّىٰهَا مَا غَشَّىٰ
“Sannan abin da ya lulluve su (na azaba) ya lulluve su.”
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكَ تَتَمَارَىٰ
To (kai xan’adam) da waxanne ni’imomin Ubangijinka kake jayayya?
هَٰذَا نَذِيرٞ مِّنَ ٱلنُّذُرِ ٱلۡأُولَىٰٓ
Wannan mai gargaxi ne daga irin masu gargaxin farko
أَزِفَتِ ٱلۡأٓزِفَةُ
Mai kusantowa ta kusanto (watau alqiyama)
لَيۡسَ لَهَا مِن دُونِ ٱللَّهِ كَاشِفَةٌ
Ba wani mai bayyana lokacinta in ban da Allah
أَفَمِنۡ هَٰذَا ٱلۡحَدِيثِ تَعۡجَبُونَ
Yanzu game da wannan zancen ne[1] kuke mamaki?
1- Watau Alqur’ani mai girma.
وَتَضۡحَكُونَ وَلَا تَبۡكُونَ
Kuke kuma dariya ba kwa yin kuka?