۞قَالَ فَمَا خَطۡبُكُمۡ أَيُّهَا ٱلۡمُرۡسَلُونَ
(Ibrahimu) ya ce: “To me yake tafe da ku, ya ku waxannan manzanni?”
قَالُوٓاْ إِنَّآ أُرۡسِلۡنَآ إِلَىٰ قَوۡمٖ مُّجۡرِمِينَ
Suka ce: “Lalle mu an aiko mu ne zuwa ga wasu mutane masu manyan laifuka[1]
1- Su ne mutanen Annabi Lux () masu neman maza da sha’awa.
لِنُرۡسِلَ عَلَيۡهِمۡ حِجَارَةٗ مِّن طِينٖ
“Don mu zuba musu qonannun duwatsu na tavon (wuta)
مُّسَوَّمَةً عِندَ رَبِّكَ لِلۡمُسۡرِفِينَ
“Waxanda aka yi wa alama daga wurin Ubangijinka saboda mavarnata.”
فَأَخۡرَجۡنَا مَن كَانَ فِيهَا مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Sai Muka tserar da duk wanda ya kasance a cikinta (alqaryar) daga muminai
فَمَا وَجَدۡنَا فِيهَا غَيۡرَ بَيۡتٖ مِّنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ
Sai ba mu sami wani (gida) a cikinta ba in ban da gida xaya na Musulmi[1]
1- Shi ne gidan Annabi Lux (), in ban da matarsa, ita ba ta yi imani ba.
وَتَرَكۡنَا فِيهَآ ءَايَةٗ لِّلَّذِينَ يَخَافُونَ ٱلۡعَذَابَ ٱلۡأَلِيمَ
Muka kuma bar aya ta wa’azi a cikinta ga waxanda suke tsoron azaba mai raxaxi
وَفِي مُوسَىٰٓ إِذۡ أَرۡسَلۡنَٰهُ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ بِسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٖ
Game da Musa kuma (akwai aya), lokacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir’auna da hujjoji bayyanannu
فَتَوَلَّىٰ بِرُكۡنِهِۦ وَقَالَ سَٰحِرٌ أَوۡ مَجۡنُونٞ
Sai ya ba da baya shi da qarfin rundunarsa, ya kuma ce: “(Musa) mai sihiri ne ko mahaukaci.”
فَأَخَذۡنَٰهُ وَجُنُودَهُۥ فَنَبَذۡنَٰهُمۡ فِي ٱلۡيَمِّ وَهُوَ مُلِيمٞ
Saboda haka Muka kama shi tare da rundunarsa, sai Muka watsa su a cikin kogi, alhali yana mai aikata abin Allah-wadai
وَفِي عَادٍ إِذۡ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمُ ٱلرِّيحَ ٱلۡعَقِيمَ
Kuma game da Adawa (akwai aya), lokacin da Muka aiko musu da iska marar alhairi
مَا تَذَرُ مِن شَيۡءٍ أَتَتۡ عَلَيۡهِ إِلَّا جَعَلَتۡهُ كَٱلرَّمِيمِ
Ba ta barin wani abu idan ta biyo ta kansa sai ta mayar da shi kamar daddagagge qashi
وَفِي ثَمُودَ إِذۡ قِيلَ لَهُمۡ تَمَتَّعُواْ حَتَّىٰ حِينٖ
Kuma game da Samudawa (akwai aya), lokacin da aka ce da su: “Ku ji daxi zuwa wani xan lokaci[1].”
1- Watau wa’adin kwana uku kacal.
فَعَتَوۡاْ عَنۡ أَمۡرِ رَبِّهِمۡ فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلصَّـٰعِقَةُ وَهُمۡ يَنظُرُونَ
Sai suka yi tsaurin kai game da umarnin Ubangijinsu, saboda haka tsawa ta faxa musu alhali kuwa suna kallo
فَمَا ٱسۡتَطَٰعُواْ مِن قِيَامٖ وَمَا كَانُواْ مُنتَصِرِينَ
To ba su sami damar tsayuwa ba, kuma ba su zamanto masu taimaka wa (junansu) ba
وَقَوۡمَ نُوحٖ مِّن قَبۡلُۖ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَوۡمٗا فَٰسِقِينَ
Kuma (Mun hallakar da) mutanen Nuhu a gabaninsu; don kuwa lalle sun kasance mutane ne fasiqai
وَٱلسَّمَآءَ بَنَيۡنَٰهَا بِأَيۡيْدٖ وَإِنَّا لَمُوسِعُونَ
Sama kuma Mun gina ta da qarfi, lalle kuma Mu tabbas Masu yalwatawa ne
وَٱلۡأَرۡضَ فَرَشۡنَٰهَا فَنِعۡمَ ٱلۡمَٰهِدُونَ
Qasa kuma Muka shimfixa ta, to madalla da Masu shimfixar
وَمِن كُلِّ شَيۡءٍ خَلَقۡنَا زَوۡجَيۡنِ لَعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ
Daga kowane abu kuma Mun halicci nau’i biyu, don ku wa’azantu
فَفِرُّوٓاْ إِلَى ٱللَّهِۖ إِنِّي لَكُم مِّنۡهُ نَذِيرٞ مُّبِينٞ
To ku gudo zuwa ga Allah[1], lalle ni mai gargaxi ne game da Shi, mai bayyana (gargaxi)
1- Watau su guje wa azabarsa zuwa kyakkyawan sakamakonsa ta hanyar yi masa biyayya.
وَلَا تَجۡعَلُواْ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَۖ إِنِّي لَكُم مِّنۡهُ نَذِيرٞ مُّبِينٞ
Kada kuma ku sanya wani abin bauta tare da Allah; lalle ni mai gargaxi ne game da Shi, mai bayyana (gargaxi)
كَذَٰلِكَ مَآ أَتَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا قَالُواْ سَاحِرٌ أَوۡ مَجۡنُونٌ
Kamar haka abin yake, ba waxanda wani manzo ya zo musu a gabaninsu (mutan Makka) sai sun ce mai sihiri ne ko mahaukaci
أَتَوَاصَوۡاْ بِهِۦۚ بَلۡ هُمۡ قَوۡمٞ طَاغُونَ
Shin wasiyya suke yi wa junansu ne game da shi? A’a, su dai mutane ne masu qetare iyaka
فَتَوَلَّ عَنۡهُمۡ فَمَآ أَنتَ بِمَلُومٖ
Sai ka rabu da su, don kuwa kai ba abin zargi ba ne
وَذَكِّرۡ فَإِنَّ ٱلذِّكۡرَىٰ تَنفَعُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Kuma ka yi wa’azi, don ko lalle wa’azi yana amfanar muminai
وَمَا خَلَقۡتُ ٱلۡجِنَّ وَٱلۡإِنسَ إِلَّا لِيَعۡبُدُونِ
Ban halicci aljanu da mutane ba sai don su bauta min
مَآ أُرِيدُ مِنۡهُم مِّن رِّزۡقٖ وَمَآ أُرِيدُ أَن يُطۡعِمُونِ
Ba Na neman wani arziki a wurinsu, kuma ba Na neman su ciyar da Ni
إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلرَّزَّاقُ ذُو ٱلۡقُوَّةِ ٱلۡمَتِينُ
Lalle Allah Shi ne Mai arzutawa, Mai tsananin qarfi
فَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُواْ ذَنُوبٗا مِّثۡلَ ذَنُوبِ أَصۡحَٰبِهِمۡ فَلَا يَسۡتَعۡجِلُونِ
To lalle waxanda suka zalunci (kansu) suna da wani kaso na azaba kamar kason abokansu[1], saboda haka kada su nemi gaggauto shi
1- Watau kafiran farko.
فَوَيۡلٞ لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن يَوۡمِهِمُ ٱلَّذِي يُوعَدُونَ
To tsananin azaba ya tabbata ga waxanda suka kafirta a ranar da ake alqawarta musu