Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 31

فَبَعَثَ ٱللَّهُ غُرَابٗا يَبۡحَثُ فِي ٱلۡأَرۡضِ لِيُرِيَهُۥ كَيۡفَ يُوَٰرِي سَوۡءَةَ أَخِيهِۚ قَالَ يَٰوَيۡلَتَىٰٓ أَعَجَزۡتُ أَنۡ أَكُونَ مِثۡلَ هَٰذَا ٱلۡغُرَابِ فَأُوَٰرِيَ سَوۡءَةَ أَخِيۖ فَأَصۡبَحَ مِنَ ٱلنَّـٰدِمِينَ

Sai Allah Ya aiko da wani hankaka ya riqa tona qasa don ya nuna masa yadda zai binne gawar xan’uwansa. Sai ya ce: “Kaicona! Yanzu na kasa zama kamar wannan hankakan, in je in binne gawar xan’uwana?” Sai ya wayi gari cikin masu nadama



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 32

مِنۡ أَجۡلِ ذَٰلِكَ كَتَبۡنَا عَلَىٰ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ أَنَّهُۥ مَن قَتَلَ نَفۡسَۢا بِغَيۡرِ نَفۡسٍ أَوۡ فَسَادٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَكَأَنَّمَا قَتَلَ ٱلنَّاسَ جَمِيعٗا وَمَنۡ أَحۡيَاهَا فَكَأَنَّمَآ أَحۡيَا ٱلنَّاسَ جَمِيعٗاۚ وَلَقَدۡ جَآءَتۡهُمۡ رُسُلُنَا بِٱلۡبَيِّنَٰتِ ثُمَّ إِنَّ كَثِيرٗا مِّنۡهُم بَعۡدَ ذَٰلِكَ فِي ٱلۡأَرۡضِ لَمُسۡرِفُونَ

Saboda wannan ne muka wajabta wa Banu-Isra’ila cewa, duk wanda ya kashe wani rai ba tare da (laifin kisan) kai ba, ko kuma wata varna a bayan qasa, to kamar ya kashe mutane ne gaba xaya, wanda kuwa ya raya shi, to kamar ya raya mutane ne gaba xaya. Kuma lalle haqiqa manzanninmu sun zo musu da (hujjoji) mabayyana, amma sai ga shi da yawa daga cikinsu bayan hakan, lalle masu varna ne a bayan qasa



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 33

إِنَّمَا جَزَـٰٓؤُاْ ٱلَّذِينَ يُحَارِبُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَيَسۡعَوۡنَ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَسَادًا أَن يُقَتَّلُوٓاْ أَوۡ يُصَلَّبُوٓاْ أَوۡ تُقَطَّعَ أَيۡدِيهِمۡ وَأَرۡجُلُهُم مِّنۡ خِلَٰفٍ أَوۡ يُنفَوۡاْ مِنَ ٱلۡأَرۡضِۚ ذَٰلِكَ لَهُمۡ خِزۡيٞ فِي ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٌ

Lalle sakamakon waxanda suke yaqar Allah da Manzonsa, kuma suke varna a bayan qasa[1], shi ne kawai a karkashe su ko kuma a giggicciye su ko kuma a yayyanke hannayensu da qafafuwansu a tarnaqe ko kuma a kore su daga qasa. Wannan qasqanci ne a gare su a nan duniya, a lahira kuma suna da azaba mai girma


1- Ana nufin duk wasu masu ta’addanci da aikata fashi da makami, wannan shi ne hukuncinsu.


Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 34

إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ مِن قَبۡلِ أَن تَقۡدِرُواْ عَلَيۡهِمۡۖ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Sai dai waxanda suka tuba tun kafin ku sami damar kama su; to ku sani cewa, lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 35

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱبۡتَغُوٓاْ إِلَيۡهِ ٱلۡوَسِيلَةَ وَجَٰهِدُواْ فِي سَبِيلِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku nemi abin da zai sada ku da shi, kuma ku yi jihadi wajen yaxa kalmarsa, don ku rabauta



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 36

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡ أَنَّ لَهُم مَّا فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا وَمِثۡلَهُۥ مَعَهُۥ لِيَفۡتَدُواْ بِهِۦ مِنۡ عَذَابِ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ مَا تُقُبِّلَ مِنۡهُمۡۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Lalle waxanda suka kafirta, in da a ce duk abin da yake ban qasa gaba xaya nasu ne, haxe kuma da wani kamarsa, domin su fanshi kansu da shi daga azabar ranar tashin alqiyama, da ba za a karva daga gare su ba; kuma suna da azaba mai raxaxi



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 37

يُرِيدُونَ أَن يَخۡرُجُواْ مِنَ ٱلنَّارِ وَمَا هُم بِخَٰرِجِينَ مِنۡهَاۖ وَلَهُمۡ عَذَابٞ مُّقِيمٞ

Suna nufin su fita daga cikin wuta, alhalin su ba masu fita ne daga cikinta ba; kuma suna da wata azaba madawwamiya



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 38

وَٱلسَّارِقُ وَٱلسَّارِقَةُ فَٱقۡطَعُوٓاْ أَيۡدِيَهُمَا جَزَآءَۢ بِمَا كَسَبَا نَكَٰلٗا مِّنَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٞ

Kuma varawo da varauniya, sai ku yanke hannayensu[1], wannan sakamako ne na abin da suka aikata, uquba ce daga Allah. Kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima


1- Za a yanke hannayensu ne na dama daga tsintsiyar hannu. Sunna ta bayyana cewa ana yanke hannun varawon da ya yi satar da ta kai rubu’in dinare ko dirhami uku na azurfa ko abin da ya yi daidai da su.


Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 39

فَمَن تَابَ مِنۢ بَعۡدِ ظُلۡمِهِۦ وَأَصۡلَحَ فَإِنَّ ٱللَّهَ يَتُوبُ عَلَيۡهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ

To (amma) wanda ya tuba bayan zaluncinsa, kuma ya gyara aikinsa, to lalle Allah zai karvi tubansa. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 40

أَلَمۡ تَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ يُعَذِّبُ مَن يَشَآءُ وَيَغۡفِرُ لِمَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Shin ba ka da masaniyar cewa, lalle Allah Shi ne Yake mallakar abin da yake cikin sammai da kuma qasa, Yana yin azaba ga wanda Ya ga dama, kuma Yana gafarta wa wanda Ya ga dama. Kuma Allah Mai iko ne a kan komai?



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 41

۞يَـٰٓأَيُّهَا ٱلرَّسُولُ لَا يَحۡزُنكَ ٱلَّذِينَ يُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡكُفۡرِ مِنَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِأَفۡوَٰهِهِمۡ وَلَمۡ تُؤۡمِن قُلُوبُهُمۡۛ وَمِنَ ٱلَّذِينَ هَادُواْۛ سَمَّـٰعُونَ لِلۡكَذِبِ سَمَّـٰعُونَ لِقَوۡمٍ ءَاخَرِينَ لَمۡ يَأۡتُوكَۖ يُحَرِّفُونَ ٱلۡكَلِمَ مِنۢ بَعۡدِ مَوَاضِعِهِۦۖ يَقُولُونَ إِنۡ أُوتِيتُمۡ هَٰذَا فَخُذُوهُ وَإِن لَّمۡ تُؤۡتَوۡهُ فَٱحۡذَرُواْۚ وَمَن يُرِدِ ٱللَّهُ فِتۡنَتَهُۥ فَلَن تَمۡلِكَ لَهُۥ مِنَ ٱللَّهِ شَيۡـًٔاۚ أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ لَمۡ يُرِدِ ٱللَّهُ أَن يُطَهِّرَ قُلُوبَهُمۡۚ لَهُمۡ فِي ٱلدُّنۡيَا خِزۡيٞۖ وَلَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٞ

Ya kai wannan Manzo, kar waxannan da suke gaggawa cikin kafirci su baqanta maka rai, daga cikin waxanda suka ce: “Mun yi imani” da bakunansu, amma zukatansu ba su yi imani ba; da kuma waxanda suke Yahudawa, masu yawan sauraron qarya, masu yawan sauraron waxansu mutanen da ba su zo wajenka ba[1]; suna caccanja kalmomi daga wurarensu, suna cewa: “Idan an ba ku wannan, to ku karve shi, idan kuwa ba shi aka ba ku ba, to ku yi hattara[2].” Duk kuwa wanda Allah Ya nufi fitinar sa, to ba abin da za ka iya mallaka masa daga wurin Allah. Waxannan su ne waxanda Allah bai yi nufin Ya tsarkake zukatansu ba. a nan duniya suna da qasqanci, a lahira kuma suna da azaba mai girma


1- Su ne malamansu da shugabanninsu waxanda ba sa halartar majalisin Manzon Allah ().


2- Watau suna faxa wa mabiyansu cewa, su kai qara wurin Manzon Allah (), idan ya yi musu hukuncin da ya dace da son zuciyarsu su karva, idan kuwa ya yi musu hukuncin da ya sava wa son zuciyarsu, to kada su yarda.


Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 42

سَمَّـٰعُونَ لِلۡكَذِبِ أَكَّـٰلُونَ لِلسُّحۡتِۚ فَإِن جَآءُوكَ فَٱحۡكُم بَيۡنَهُمۡ أَوۡ أَعۡرِضۡ عَنۡهُمۡۖ وَإِن تُعۡرِضۡ عَنۡهُمۡ فَلَن يَضُرُّوكَ شَيۡـٔٗاۖ وَإِنۡ حَكَمۡتَ فَٱحۡكُم بَيۡنَهُم بِٱلۡقِسۡطِۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُقۡسِطِينَ

(Su ne) masu yawan sauraron qarya, masu yawan cin haram. Don haka idan sun zo maka, to ka yi musu hukunci, ko ka kau da kai daga gare su; idan kuwa ka kawar da kai daga gare su, to ba za su cutar da kai da komai ba; idan kuwa za ka yi hukuncin, to ka yi hukunci tsakaninsu da adalci. Lalle Allah Yana son masu adalci



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 43

وَكَيۡفَ يُحَكِّمُونَكَ وَعِندَهُمُ ٱلتَّوۡرَىٰةُ فِيهَا حُكۡمُ ٱللَّهِ ثُمَّ يَتَوَلَّوۡنَ مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَۚ وَمَآ أُوْلَـٰٓئِكَ بِٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Kuma ta yaya za su kawo maka hukunci, alhalin Attaura tana wurinsu, a cikinta akwai hukuncin Allah, sannan su juya baya bayan haka? Waxannan kam ba muminai ba ne



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 44

إِنَّآ أَنزَلۡنَا ٱلتَّوۡرَىٰةَ فِيهَا هُدٗى وَنُورٞۚ يَحۡكُمُ بِهَا ٱلنَّبِيُّونَ ٱلَّذِينَ أَسۡلَمُواْ لِلَّذِينَ هَادُواْ وَٱلرَّبَّـٰنِيُّونَ وَٱلۡأَحۡبَارُ بِمَا ٱسۡتُحۡفِظُواْ مِن كِتَٰبِ ٱللَّهِ وَكَانُواْ عَلَيۡهِ شُهَدَآءَۚ فَلَا تَخۡشَوُاْ ٱلنَّاسَ وَٱخۡشَوۡنِ وَلَا تَشۡتَرُواْ بِـَٔايَٰتِي ثَمَنٗا قَلِيلٗاۚ وَمَن لَّمۡ يَحۡكُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَٰفِرُونَ

Lalle Mu Muka saukar da Attaura, (wadda) a cikinta akwai shiriya da haske. Annabawa waxanda suka miqa wuya suna hukunci da ita, ga waxanda suke Yahudawa, da malamai na-Allah da malamai masana, saboda abin da aka xora musu na kiyaye Littafin Allah, kuma sun kasance masu ba da shaida a kansa. Don haka kada ku ji tsoron mutane, ku ji tsoro Na Ni kaxai, kuma kada ku musanya ayoyina da wani xan farashi qanqani. Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba kuwa, to waxannan su ne kafirai



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 45

وَكَتَبۡنَا عَلَيۡهِمۡ فِيهَآ أَنَّ ٱلنَّفۡسَ بِٱلنَّفۡسِ وَٱلۡعَيۡنَ بِٱلۡعَيۡنِ وَٱلۡأَنفَ بِٱلۡأَنفِ وَٱلۡأُذُنَ بِٱلۡأُذُنِ وَٱلسِّنَّ بِٱلسِّنِّ وَٱلۡجُرُوحَ قِصَاصٞۚ فَمَن تَصَدَّقَ بِهِۦ فَهُوَ كَفَّارَةٞ لَّهُۥۚ وَمَن لَّمۡ يَحۡكُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ

Kuma Mun wajabta a kansu a cikinta (Attaura), lalle rai da rai, kuma ido da ido, kuma hanci da hanci, kuma kunne da kunne, kuma haqori da haqori, raunuka kuma a yi ramuwa. To duk wanda ya yi sadaka da shi, to wannan kaffara ce gare shi. Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba kuwa, to waxannan su ne azzalumai



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 46

وَقَفَّيۡنَا عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِم بِعِيسَى ٱبۡنِ مَرۡيَمَ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ مِنَ ٱلتَّوۡرَىٰةِۖ وَءَاتَيۡنَٰهُ ٱلۡإِنجِيلَ فِيهِ هُدٗى وَنُورٞ وَمُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ مِنَ ٱلتَّوۡرَىٰةِ وَهُدٗى وَمَوۡعِظَةٗ لِّلۡمُتَّقِينَ

Sai Muka biyar da Isa xan Maryamu a bayansu wanda yake gaskata abin da ya gabace shi na Attaura, kuma Muka ba shi Linjila, a cikinta akwai shiriya da haske, kuma tana gaskata abin da ya gabace ta na Attaura, kuma shiriya ce, da wa’azi ga masu taqawa



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 47

وَلۡيَحۡكُمۡ أَهۡلُ ٱلۡإِنجِيلِ بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فِيهِۚ وَمَن لَّمۡ يَحۡكُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ

Lalle kuma ma’abota Linjila su yi hukunci da abin da Allah Ya saukar a cikinsa. Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba kuwa, to waxannan su ne fasiqai



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 48

وَأَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَمُهَيۡمِنًا عَلَيۡهِۖ فَٱحۡكُم بَيۡنَهُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُۖ وَلَا تَتَّبِعۡ أَهۡوَآءَهُمۡ عَمَّا جَآءَكَ مِنَ ٱلۡحَقِّۚ لِكُلّٖ جَعَلۡنَا مِنكُمۡ شِرۡعَةٗ وَمِنۡهَاجٗاۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَجَعَلَكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَلَٰكِن لِّيَبۡلُوَكُمۡ فِي مَآ ءَاتَىٰكُمۡۖ فَٱسۡتَبِقُواْ ٱلۡخَيۡرَٰتِۚ إِلَى ٱللَّهِ مَرۡجِعُكُمۡ جَمِيعٗا فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ فِيهِ تَخۡتَلِفُونَ

Kuma Mun saukar maka da Littafin (Alqur’ani) da gaskiya, yana mai gaskata abin da ya gabace shi na sauran littattafai, kuma mai xaukaka a kansu; don haka ka yi hukunci a tsakaninsu da abin da Allah Ya saukar; kuma kada ka bi soye-soyen zukatansu ka bar abin da ya zo maka na gaskiya don bin son zuciyarsu. Kowanne daga cikinku Mun sanya musu tsari na shari’a da tsari na rayuwa. Kuma in da Allah Ya ga dama, da sai Ya sanya ku ku zamo al’umma xaya, sai dai kuma don Ya jarrabe ku cikin abin da Ya ba ku; don haka sai ku yi gaggawar aikata ayyuka na alheri. Gaba xaya makomarku zuwa ga Allah take, kuma zai ba ku labarin abin da kuka kasance kuna savani a kansa



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 49

وَأَنِ ٱحۡكُم بَيۡنَهُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ وَلَا تَتَّبِعۡ أَهۡوَآءَهُمۡ وَٱحۡذَرۡهُمۡ أَن يَفۡتِنُوكَ عَنۢ بَعۡضِ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ إِلَيۡكَۖ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَٱعۡلَمۡ أَنَّمَا يُرِيدُ ٱللَّهُ أَن يُصِيبَهُم بِبَعۡضِ ذُنُوبِهِمۡۗ وَإِنَّ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلنَّاسِ لَفَٰسِقُونَ

Kuma ka yi hukunci a tsakaninsu da abin da Allah Ya saukar, kuma kada ka bi soye-soyen zukatansu, kuma ka yi hattara da su, don kada su fitine ka ka bar wani sashi na abin da Allah Ya saukar maka; idan kuwa sun juya baya, to ka sani lalle Allah Yana nufin Ya kama su ne da wani sashi na zunubansu. Kuma lalle yawancin mutane fasiqai ne



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 50

أَفَحُكۡمَ ٱلۡجَٰهِلِيَّةِ يَبۡغُونَۚ وَمَنۡ أَحۡسَنُ مِنَ ٱللَّهِ حُكۡمٗا لِّقَوۡمٖ يُوقِنُونَ

Shin hukuncin jahiliyya suke nema ne? To wane ne ya fi Allah kyakkyawan hukunci ga mutanen da suke da sakankancewa?



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 51

۞يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّخِذُواْ ٱلۡيَهُودَ وَٱلنَّصَٰرَىٰٓ أَوۡلِيَآءَۘ بَعۡضُهُمۡ أَوۡلِيَآءُ بَعۡضٖۚ وَمَن يَتَوَلَّهُم مِّنكُمۡ فَإِنَّهُۥ مِنۡهُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku riqi Yahudawa da Nasara masoya. Sashinsu masoya sashi ne. Duk kuwa cikinku wanda ya jivinci lamarinsu, to lalle shi yana cikinsu. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 52

فَتَرَى ٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ يُسَٰرِعُونَ فِيهِمۡ يَقُولُونَ نَخۡشَىٰٓ أَن تُصِيبَنَا دَآئِرَةٞۚ فَعَسَى ٱللَّهُ أَن يَأۡتِيَ بِٱلۡفَتۡحِ أَوۡ أَمۡرٖ مِّنۡ عِندِهِۦ فَيُصۡبِحُواْ عَلَىٰ مَآ أَسَرُّواْ فِيٓ أَنفُسِهِمۡ نَٰدِمِينَ

Sai ka ga waxanda suke da cuta a cikin zukatansu suna gaggawa a ciki (jivintar su), suna cewa: “Muna jin tsoron kar wata musiba ta same mu.” To mai yiwuwa ne Allah Ya zo da buxi ko wani lamari daga gare Shi, sai su wayi gari suna nadama kan abin da suka riqa voyewa a zukatansu



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 53

وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَهَـٰٓؤُلَآءِ ٱلَّذِينَ أَقۡسَمُواْ بِٱللَّهِ جَهۡدَ أَيۡمَٰنِهِمۡ إِنَّهُمۡ لَمَعَكُمۡۚ حَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡ فَأَصۡبَحُواْ خَٰسِرِينَ

Kuma waxanda suka yi imani suna cewa[1]: “Yanzu waxannan su ne waxanda suka rantse da Allah iya qurewar rantsuwarsu; cewa, lalle suna tare da ku?” Ayyukansu sun rushe, don haka sai suka wayi gari suna masu hasara


1- Watau lokacin da asirin munafukai ya tonu.


Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 54

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَن يَرۡتَدَّ مِنكُمۡ عَن دِينِهِۦ فَسَوۡفَ يَأۡتِي ٱللَّهُ بِقَوۡمٖ يُحِبُّهُمۡ وَيُحِبُّونَهُۥٓ أَذِلَّةٍ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ أَعِزَّةٍ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ يُجَٰهِدُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلَا يَخَافُونَ لَوۡمَةَ لَآئِمٖۚ ذَٰلِكَ فَضۡلُ ٱللَّهِ يُؤۡتِيهِ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٌ

Ya ku waxanda suka yi imani, duk wanda ya yi ridda daga cikinku, ya bar addininsa, to (ya sani) Allah zai kawo waxansu mutane da Yake son su suna son Sa, suna masu qasqantar da kai ga muminai, suna masu nuna wa kafirai isa, suna yin jihadi don xaukaka kalmar Allah, kuma ba sa jin tsoron zargin wani mai zargi. Wannan falalar Allah ce da Yake bayar da ita ga wanda Ya ga dama. Kuma Allah Mayalwaci ne, Masani



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 55

إِنَّمَا وَلِيُّكُمُ ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱلَّذِينَ يُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَهُمۡ رَٰكِعُونَ

Allah ne kaxai Majivincin al’amarinku da Manzonsa da kuma waxanda suka yi imani, waxanda suke tsayar da salla, kuma suke bayar da zakka, suna kuma masu yin ruku’i



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 56

وَمَن يَتَوَلَّ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ فَإِنَّ حِزۡبَ ٱللَّهِ هُمُ ٱلۡغَٰلِبُونَ

Kuma duk wanda ya jivinci Allah da Manzonsa da waxanda suka yi imani, to lalle rundunar Allah su ne masu rinjaye



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 57

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّخِذُواْ ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ دِينَكُمۡ هُزُوٗا وَلَعِبٗا مِّنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلِكُمۡ وَٱلۡكُفَّارَ أَوۡلِيَآءَۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku riqi waxanda suke yin izgili da wasa da addininku, waxanda aka bai wa Littafi tun kafinku, da kuma kafirai, a matsayin masoya, kuma ku kiyaye dokokin Allah, in har da gaske ku muminai ne



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 58

وَإِذَا نَادَيۡتُمۡ إِلَى ٱلصَّلَوٰةِ ٱتَّخَذُوهَا هُزُوٗا وَلَعِبٗاۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَوۡمٞ لَّا يَعۡقِلُونَ

Kuma idan kuka yi kiran salla, sai su xauke ta abin yi wa izgili da wasa. Suna yin hakan don su mutane ne da ba sa hankalta



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 59

قُلۡ يَـٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ هَلۡ تَنقِمُونَ مِنَّآ إِلَّآ أَنۡ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡنَا وَمَآ أُنزِلَ مِن قَبۡلُ وَأَنَّ أَكۡثَرَكُمۡ فَٰسِقُونَ

Ka ce: “Ya ku Ma’abota Littafi, shin kuna da abin da kuke qi a tare da mu ne? Sai fa cewa, mun yi imani da Allah da abin da aka saukar mana da abin da aka saukar kafinmu da kuma cewa, lalle yawancinku fasiqai ne.”



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 60

قُلۡ هَلۡ أُنَبِّئُكُم بِشَرّٖ مِّن ذَٰلِكَ مَثُوبَةً عِندَ ٱللَّهِۚ مَن لَّعَنَهُ ٱللَّهُ وَغَضِبَ عَلَيۡهِ وَجَعَلَ مِنۡهُمُ ٱلۡقِرَدَةَ وَٱلۡخَنَازِيرَ وَعَبَدَ ٱلطَّـٰغُوتَۚ أُوْلَـٰٓئِكَ شَرّٞ مَّكَانٗا وَأَضَلُّ عَن سَوَآءِ ٱلسَّبِيلِ

Ka ce: “Shin ba na ba ku labarin sakamakon da ya fi wannan sharri a wurin Allah ba? Shi ne wanda Allah Ya la’anta, kuma Ya yi fushi da shi, kuma Ya mayar da wasu daga cikinsu birrai da aladu; kuma ya bauta wa gunki. Su waxannan su ne matsayinsu ya fi sharri, kuma (su ne) suka fi vacewa daga tafarkin shiriya.”