Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 31

مِثۡلَ دَأۡبِ قَوۡمِ نُوحٖ وَعَادٖ وَثَمُودَ وَٱلَّذِينَ مِنۢ بَعۡدِهِمۡۚ وَمَا ٱللَّهُ يُرِيدُ ظُلۡمٗا لِّلۡعِبَادِ

“Kamar misalin al’adar mutanen Nuhu da Adawa da Samudawa da kuma waxanda suka zo bayansu. Allah kuwa ba Ya nufin zalunci ga bayi



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 32

وَيَٰقَوۡمِ إِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ يَوۡمَ ٱلتَّنَادِ

“Kuma ya ku mutanena, lalle ni ina jiye muku tsoron ranar kiraye-kirayen juna (ranar alqiyama)[1]


1- Watau mutane za su riqa kiran junansu saboda dangantaka ta jini suna neman alfarma.


Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 33

يَوۡمَ تُوَلُّونَ مُدۡبِرِينَ مَا لَكُم مِّنَ ٱللَّهِ مِنۡ عَاصِمٖۗ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِنۡ هَادٖ

“Ranar da za ku juya kuna masu ba da baya, ba ku da wani mai kare ku daga Allah. Duk kuma wanda Allah Ya vatar to ba shi da wani mai shiryarwa.”



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 34

وَلَقَدۡ جَآءَكُمۡ يُوسُفُ مِن قَبۡلُ بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَمَا زِلۡتُمۡ فِي شَكّٖ مِّمَّا جَآءَكُم بِهِۦۖ حَتَّىٰٓ إِذَا هَلَكَ قُلۡتُمۡ لَن يَبۡعَثَ ٱللَّهُ مِنۢ بَعۡدِهِۦ رَسُولٗاۚ كَذَٰلِكَ يُضِلُّ ٱللَّهُ مَنۡ هُوَ مُسۡرِفٞ مُّرۡتَابٌ

Haqiqa kuma Yusufu ya zo muku da (hujjoji) bayyanannu tun kafin (zuwan Musa), to ba ku gushe kuna kokwanton abin da ya zo muku da shi ba, har yayin da ya mutu sai kuka ce: “Allah ba zai sake aiko da wani manzo bayansa ba.” Kamar haka ne Allah Yake vatar da duk wanda shi mai varna ne, mai shakka



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 35

ٱلَّذِينَ يُجَٰدِلُونَ فِيٓ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ بِغَيۡرِ سُلۡطَٰنٍ أَتَىٰهُمۡۖ كَبُرَ مَقۡتًا عِندَ ٱللَّهِ وَعِندَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْۚ كَذَٰلِكَ يَطۡبَعُ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ قَلۡبِ مُتَكَبِّرٖ جَبَّارٖ

Waxanda suke yin jayayya game da ayoyin Allah ba tare da wata hujja da ta zo musu ba; qyamar (wannan) a wurin Allah da wurin waxanda suka yi imani ta girmama. Kamar haka ne Allah Yake toshe zuciyar duk wani mai girman kai, mai tsaurin rai



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 36

وَقَالَ فِرۡعَوۡنُ يَٰهَٰمَٰنُ ٱبۡنِ لِي صَرۡحٗا لَّعَلِّيٓ أَبۡلُغُ ٱلۡأَسۡبَٰبَ

Fir’auna kuma ya ce: “Ya Hamana, ka gina min dogon gini ko na kai ga hanyoyi



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 37

أَسۡبَٰبَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ فَأَطَّلِعَ إِلَىٰٓ إِلَٰهِ مُوسَىٰ وَإِنِّي لَأَظُنُّهُۥ كَٰذِبٗاۚ وَكَذَٰلِكَ زُيِّنَ لِفِرۡعَوۡنَ سُوٓءُ عَمَلِهِۦ وَصُدَّ عَنِ ٱلسَّبِيلِۚ وَمَا كَيۡدُ فِرۡعَوۡنَ إِلَّا فِي تَبَابٖ

“(Watau) hanyoyin (da ke kaiwa zuwa) sammai sai in gano Ubangijin Musa, lalle kuma ni ina tsammaninsa maqaryaci ne.” Kamar haka kuma aka qawata wa Fir’auna mummunan aikinsa aka kuma kange shi daga hanyar (gaskiya). Makircin Fir’auna kuwa ba a komai yake ba sai cikin halaka



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 38

وَقَالَ ٱلَّذِيٓ ءَامَنَ يَٰقَوۡمِ ٱتَّبِعُونِ أَهۡدِكُمۡ سَبِيلَ ٱلرَّشَادِ

Sai (mutumin nan) wanda ya yi imani ya ce: “Ya ku mutanena, ku bi ni in nuna muku hanyar shiriya



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 39

يَٰقَوۡمِ إِنَّمَا هَٰذِهِ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا مَتَٰعٞ وَإِنَّ ٱلۡأٓخِرَةَ هِيَ دَارُ ٱلۡقَرَارِ

“Ya ku mutanena, lalle wannan rayuwar ta duniya xan jin daxi ne, kuma lalle lahira ita ce gidan tabbata



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 40

مَنۡ عَمِلَ سَيِّئَةٗ فَلَا يُجۡزَىٰٓ إِلَّا مِثۡلَهَاۖ وَمَنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَأُوْلَـٰٓئِكَ يَدۡخُلُونَ ٱلۡجَنَّةَ يُرۡزَقُونَ فِيهَا بِغَيۡرِ حِسَابٖ

“Wanda ya aikata wani mummunan aiki, to ba za a saka masa ba sai da kwatankwacinsa, wanda kuwa ya aikata wani kyakkyawan aiki, namiji ne ko mace alhali shi yana mumini, to waxannan za su shiga Aljanna, a riqa arzuta su a cikinta ba tare da lissafi ba



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 41

۞وَيَٰقَوۡمِ مَا لِيٓ أَدۡعُوكُمۡ إِلَى ٱلنَّجَوٰةِ وَتَدۡعُونَنِيٓ إِلَى ٱلنَّارِ

“Kuma ya ku mutanena, me ya sa ne nake kiranku zuwa ga tsira, ku kuma kuke kira na zuwa wuta?



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 42

تَدۡعُونَنِي لِأَكۡفُرَ بِٱللَّهِ وَأُشۡرِكَ بِهِۦ مَا لَيۡسَ لِي بِهِۦ عِلۡمٞ وَأَنَا۠ أَدۡعُوكُمۡ إِلَى ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡغَفَّـٰرِ

“Kuna kira na da in kafirce wa Allah, in kuma tara Shi da abin da ba ni da wani sani a kansa, ni kuma ina kiran ku zuwa Mabuwayi, Mai yawan gafara?



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 43

لَا جَرَمَ أَنَّمَا تَدۡعُونَنِيٓ إِلَيۡهِ لَيۡسَ لَهُۥ دَعۡوَةٞ فِي ٱلدُّنۡيَا وَلَا فِي ٱلۡأٓخِرَةِ وَأَنَّ مَرَدَّنَآ إِلَى ٱللَّهِ وَأَنَّ ٱلۡمُسۡرِفِينَ هُمۡ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِ

“Ba shakka abin da kuke kira na zuwa gare shi ba shi da wani kira karvavve a duniya ko a lahira, kuma lalle makomarmu zuwa ga Allah ne, mavarnata kuma tabbas su ne ‘yan wuta



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 44

فَسَتَذۡكُرُونَ مَآ أَقُولُ لَكُمۡۚ وَأُفَوِّضُ أَمۡرِيٓ إِلَى ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ بَصِيرُۢ بِٱلۡعِبَادِ

“To ba da daxewa ba za ku tuna abin da nake gaya muku. Ina kuma miqa al’amarina zuwa ga Allah. Lalle Allah Mai ganin bayi ne.”



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 45

فَوَقَىٰهُ ٱللَّهُ سَيِّـَٔاتِ مَا مَكَرُواْۖ وَحَاقَ بِـَٔالِ فِرۡعَوۡنَ سُوٓءُ ٱلۡعَذَابِ

Sai Allah Ya kiyaye shi (sakamakon) mummunan abin da suka shirya; kuma mummunar azaba ta saukar wa mutanen Fir’auna



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 46

ٱلنَّارُ يُعۡرَضُونَ عَلَيۡهَا غُدُوّٗا وَعَشِيّٗاۚ وَيَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ أَدۡخِلُوٓاْ ءَالَ فِرۡعَوۡنَ أَشَدَّ ٱلۡعَذَابِ

(Ita ce) wuta da za a riqa bijirar da su a gare ta safe da yamma; Ranar tashin alqiyama kuma za a ce: “Ku shigar da mutanen Fir’auna mafi tsananin azaba



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 47

وَإِذۡ يَتَحَآجُّونَ فِي ٱلنَّارِ فَيَقُولُ ٱلضُّعَفَـٰٓؤُاْ لِلَّذِينَ ٱسۡتَكۡبَرُوٓاْ إِنَّا كُنَّا لَكُمۡ تَبَعٗا فَهَلۡ أَنتُم مُّغۡنُونَ عَنَّا نَصِيبٗا مِّنَ ٱلنَّارِ

(Ka tuna) kuma lokacin da suke ta yin jayayya a cikin wuta, sai raunanan su riqa ce wa waxanda suka yi girman kai: “Lalle mun kasance mabiyanku (a duniya), to shin za ku iya xauke mana wani kaso na (azabar) wuta?”



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 48

قَالَ ٱلَّذِينَ ٱسۡتَكۡبَرُوٓاْ إِنَّا كُلّٞ فِيهَآ إِنَّ ٱللَّهَ قَدۡ حَكَمَ بَيۡنَ ٱلۡعِبَادِ

Waxanda suka yi girman kai sai su ce: “Lalle mu duka a cikinta muke, lalle Allah Ya riga Ya yi hukunci tsakanin bayi.”



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 49

وَقَالَ ٱلَّذِينَ فِي ٱلنَّارِ لِخَزَنَةِ جَهَنَّمَ ٱدۡعُواْ رَبَّكُمۡ يُخَفِّفۡ عَنَّا يَوۡمٗا مِّنَ ٱلۡعَذَابِ

Kuma waxanda suke cikin wuta suka ce da masu tsaron Jahannama: “Ku roqa mana Ubangijinku mana Ya sauqaqe mana azaba ta wuni (xaya).”



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 50

قَالُوٓاْ أَوَلَمۡ تَكُ تَأۡتِيكُمۡ رُسُلُكُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِۖ قَالُواْ بَلَىٰۚ قَالُواْ فَٱدۡعُواْۗ وَمَا دُعَـٰٓؤُاْ ٱلۡكَٰفِرِينَ إِلَّا فِي ضَلَٰلٍ

Suka ce: “Yanzu manzanninku ba su kasance suna zo muku da (ayoyi) bayyanannu ba?” Suka ce: “Haka ne (sun zo)”. Sai su ce: “To sai ku yi ta roqon. Roqon kafirai kuwa bai zamo ba sai a tave.”



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 51

إِنَّا لَنَنصُرُ رُسُلَنَا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَيَوۡمَ يَقُومُ ٱلۡأَشۡهَٰدُ

Lalle Mu tabbas Muna taimakon manzanninmu da kuma waxanda suka yi imani a rayuwar duniya da kuma ranar da shedu za su tsaya



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 52

يَوۡمَ لَا يَنفَعُ ٱلظَّـٰلِمِينَ مَعۡذِرَتُهُمۡۖ وَلَهُمُ ٱللَّعۡنَةُ وَلَهُمۡ سُوٓءُ ٱلدَّارِ

Ranar da hanzarin azzulamai ba zai amfane su ba; la’ana kuma ta tabbata a kansu, suna kuma da mummunan gida



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 53

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡهُدَىٰ وَأَوۡرَثۡنَا بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ ٱلۡكِتَٰبَ

Kuma haqiqa Mun bai wa Musa shiriya, Muka kuwa gadar wa Banu-Isra’ila littafin (Attaura)



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 54

هُدٗى وَذِكۡرَىٰ لِأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ

Don shiriya da wa’azantuwa ga masu hankali



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 55

فَٱصۡبِرۡ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لِذَنۢبِكَ وَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ بِٱلۡعَشِيِّ وَٱلۡإِبۡكَٰرِ

Sai ka yi haquri, lalle alqawarin Allah gaskiya ne, ka kuma nemi gafarar zunubinka, kuma ka yi tasbihi da yabon Ubangijinka a maraice da safiya



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 56

إِنَّ ٱلَّذِينَ يُجَٰدِلُونَ فِيٓ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ بِغَيۡرِ سُلۡطَٰنٍ أَتَىٰهُمۡ إِن فِي صُدُورِهِمۡ إِلَّا كِبۡرٞ مَّا هُم بِبَٰلِغِيهِۚ فَٱسۡتَعِذۡ بِٱللَّهِۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ

Lalle waxanda suke yin jayayya game da ayoyin Allah ba tare da wata hujja da ta zo musu ba, ba komai a cikin zukatansu sai neman xaukaka wadda ba za su same ta ba. Sai ka nemi tsari daga Allah; lalle Shi Mai ji ne, Mai gani



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 57

لَخَلۡقُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ أَكۡبَرُ مِنۡ خَلۡقِ ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ

Tabbas halittar sammai da qasa ta fi girma a kan halittar mutane, sai dai kuma yawancin mutane ba sa sanin (haka)



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 58

وَمَا يَسۡتَوِي ٱلۡأَعۡمَىٰ وَٱلۡبَصِيرُ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَلَا ٱلۡمُسِيٓءُۚ قَلِيلٗا مَّا تَتَذَكَّرُونَ

Kuma makaho da mai gani ba za su yi daidai ba, kuma waxanda suka yi imani suka yi aiki nagari ba za su yi (daidai) da mai mummunan aiki ba. Kaxan ne qwarai kuke wa’azantuwa



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 59

إِنَّ ٱلسَّاعَةَ لَأٓتِيَةٞ لَّا رَيۡبَ فِيهَا وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يُؤۡمِنُونَ

Lalle alqiyama tabbas za ta zo babu kokwanto a cikinta, sai dai kuma yawancin mutane ba sa yin imani



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 60

وَقَالَ رَبُّكُمُ ٱدۡعُونِيٓ أَسۡتَجِبۡ لَكُمۡۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَسۡتَكۡبِرُونَ عَنۡ عِبَادَتِي سَيَدۡخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِينَ

Ubangijinku kuma Ya ce: “Ku roqe Ni zan amsa muku. Lalle waxanda suke yin girman kai game da bauta min, ba da daxewa ba za su shiga Jahannama a wulaqance.”